Tinubu Ya Waiwayi Manyan Kamfanonin Kafafen Sadarwa, Za a Binciki Meta, X da Sauransu

Tinubu Ya Waiwayi Manyan Kamfanonin Kafafen Sadarwa, Za a Binciki Meta, X da Sauransu

  • Kungiyar masu yada labarai ta Najeriya (NPO) ta shigar da korafi kan wasu abubuwa da ta zargi kamfanonin Meta, X da sauransu na aikatawa
  • An shigar da korafin ne ga fadar shugaban kasa bayan an zarge kamfanonin da yin wasu abubuwa da suka sabawa doka
  • Mai girma shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya umarci hukumar FCCPC da ta gudanar da bincike kan lamarin

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

FCT, Abuja - Shugaba Bola Tinubu ya ba hukumar FCCPC umarnin gudanar da bincike kan manyan kamfanonin fasaha da na AI na duniya.

Shugaba Tinubu ya bada umarnin ne bisa zargin nuna rashin adalci a gasar kasuwanci da kuma amfani da kayayyakin kungiyoyin yada labarai na Najeriya ba bisa ka'ida ba.

Tinubu ya ce a binciki Meta da X
Shugaba Bola Tinubu na jawabi a wajen taro Hoto: @aonanuga1956
Source: Twitter

Umarnin ya biyo bayan wata hadakar takardar koke ce da kungiyar masu yada labarai ta Najeriya (NPO) ta mika wa fadar shugaban kasa, rahoton jaridar Daily Trust ya nuna hakan.

Kara karanta wannan

"Ko dai ka yi murabus"; Peter Obi ya ba Tinubu zabi 2 kan rashin tsaro

Za a binciki Meta, X da sauransu

An mika umarnin gwamnatin tarayyar ga hukumar FCCPC ne a cikin wata wasika da Ministan yada labarai da wayar da kan jama'a, Mohammed Idris, ya sanya wa hannu.

Kamar yadda sanarwar ta bayyana, ana sa ran binciken zai duba damuwar da masana'antar yada labarai ta Najeriya ta nuna game da yadda dandalolin dijital ke dada yin tasiri a kan dorewar yanayin yada labarai na kasar.

Takardar kukan ta ambaci sunayen manyan kamfanonin fasaha na musamman, ciki har da Meta, Alphabet, X, da kuma wasu dandalolin AI da ke aiki a Najeriya.

An zarge su da wasu halaye da za su iya gurgunta gasar adalci, bunkasar kasuwanci ta kungiyoyin yada labarai na Najeriya, da kuma hakkokin masu kirkirar abubuwa da mawallafa, cewar rahoton jaridar The Punch.

Meyasa za a yi binciken?

Yayin da yake mayar da martani kan umarnin, mataimakin shugaban hukumar kuma babban jami'i na FCCPC, Tunji Bello, ya ce hukumar za ta gudanar da bincike mai zaman kansa, mai gaskiya, bisa dogaro da hujjoji.

Kara karanta wannan

Peter Obi ya sake bukatar Tinubu ya yi murabus kan badakalar da IMF ta tono

A cewar FCCPC, binciken zai tantance ko halayen da ake zargi sun keta dokar kare gasar kasuwanci da ma'aikata ta tarayya (FCCPA) ta shekarar 2018 ko wata doka daban da ta shafi lamarin.

Wadanne zarge-zarge ake yi masu?

Daga cikin batutuwan da za a bincika har da zargin mamaye kasuwa da nuna halayen adawa da gasar adalci, kwasar kayan mutane ba tare da izini ba, satar bayanai, shigar da su ko amfani da su ta hanyar kasuwanci na labaran da ke da hakkin mallaka..

Hukumar za ta kuma binciki damuwar da ake da ita game da rashin tsarin kasuwanci na adalci tsakanin kamfanonin fasaha na duniya da mawallafa labarai na Najeriya.

Tinubu ya umarci a binciki su Meta da X
Shugaban kasar Najeriya, mai girma Bola Tinubu Hoto: @aonanuga1956
Source: Facebook

Hakazalika, akwai zargin cewa an hana kungiyoyin yada labarai na cikin gida damammaki masu ma'ana na yin shawarwari kan samun diyya ta adalci saboda amfani da kayansu.

Obi ya bukaci Tinubu ya yi murabus

A wani labarin kuma, kun ji cewa dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar NDC, Peter Obi, ya bukaci Shugaba Bola Tinubu, ya yi murabus.

Peter Obi ya kafa hujja da​ bayanin da asusun IMF ya fitar game da kashe kudade a boye wadanda ba su cikin kasafin kudin Najeriya.

A cewarsa, kudaden da aka ruwaito an kashe din, wadanda ya kiyasta sun kai kusan Naira tiriliyan 8.83.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng