Baraka Ta Bulla a Izala a Kano kan Goyon Bayan 'Yan Takarar Gwamna a 2027
- An fara samun sabani a tsakanin kungiyar Izala a jihar Kano kan goyon bayan 'yan takarar gwamna a jihar Kano a zaben 2027 da ke tafe
- Kungiyar 'yan Izala masu bin tafarkin siyasar Kwankwasiyya sun bayyana cewa ba su amince da matakin da aka ce kungiyar ta dauka ba
- Gwamnatin Abba Kabir Yusuf ta ce gwamnan ya samu goyon bayan Izala bayan ganawa da shugaban kungiyar, Sheikh Abdullahi Pakistan
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Kano - Maganar goyon bayan Abba Kabir Yusuf a zaben gwamnan jihar Kano da aka ce Izala ta yi ya fara tayar da kura a jihar Kano.
Wasu 'yan kungiyar Izala sun bayyana cewa suna tare da tafiyar Kwankwasiyya da Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ke jagoranta.

Source: Facebook
Legit ta tattaro bayanai game da matsayar 'yan Kwankwasiyya Izala ne a wani sako da kakakinsu, Salisu Yaro Dangaske ya wallafa a Facebook.
Matsayar 'yan Kwankwasiyya Izala
Kungiyar 'yan Kwankwasiyya Izala ta bayyana cewa an kafa JIBWIS ne domin tafiyar da harkokin addinin Musulunci ba siyasa ba.
Sun ce:
"Muna sanar da al'umma cewa Izalawan Kwankwasiyya ba ƙungiyar addini ba ce, ƙungiya ce ta siyasa da ta ƙunshi mabiya tafarkin Kwankwasiyya.
"Kasancewar mambobinmu suna bin tafarkin Izala a addinance ne ya sa aka sanya wa ƙungiyar suna Izalawan Kwankwasiyya. Wannan suna ba ya nufin cewa muna wakiltar ƙungiyar Izala ko kuma reshe ne na ƙungiyar."
"A bisa haka, muna bayyana cewa muna barranta da duk wani matsayi na siyasa da aka jingina wa ƙungiyar Izala na nuna goyon baya ga jam'iyyar APC ko wani ɗan siyasa. Irin wannan matsayi ba ya wakiltar ra'ayin Izalawan Kwankwasiyya, kuma ba shi da wata alaƙa da ƙungiyarmu."

Source: Facebook
Me 'yan Kwankwasiyya ke so?
Salisu Yaro Dangaske ya bayyana cewa abin da suke bukata shi ne kungiyar ta tsaya ba tare da nuna goyon baya ga wani dan siyasa ba.
"A fahimtarmu, ƙungiyar Izala ƙungiya ce ta addini wadda ya dace ta kasance tsaka-tsaki a harkokin siyasa, domin tana da mabiya masu ra'ayoyi da jam'iyyu mabambanta.
"Shigar ƙungiyar addini cikin siyasar ɓangaranci na iya haifar da cece-kuce tare da rage mutunci da martabar da al'umma ke yi mata.
"Muna kuma sake jaddada cewa Izalawan Kwankwasiyya tana nan daram kan akidarta ta siyasa. Har yau har gobe muna tare da jagoran tafarkin Kwankwasiyya, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, kuma muna ci gaba da biyayya ga manufofi da akidar Kwankwasiyya."
Izala ta goyi bayan Abba Kabir
A wani labarin, mun kawo muku cewa kungiyar Izala ta jihar Kano ta nuna goyon baya ga tazarcen gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf.
Gwamnatin Kano ta bayyana cewa Farfesa Abdullahi Saleh Pakistan da ke jagorantar kungiyar ne ya bayyana haka bayan ganawa da Abba Kabir Yusuf.
Gwamna Abba Kabir ya ziyarci Sheikh Pakistan ne a gidan shi domin yi masa ta'aziyyar matar shi da ta riga mu gidan gaskiya a kwanakin baya.
Asali: Legit.ng


