Kwankwasiyya Ta Fadi Gaskiya kan Zargin Kwankwaso da NDC Sun Samu Baraka

Kwankwasiyya Ta Fadi Gaskiya kan Zargin Kwankwaso da NDC Sun Samu Baraka

  • Kungiyar Kwankwasiyya ya yi martani ga rahoton da ke cewa an samu sabani tsakanin Sanata Rabiu Musa Kwankwaso da shugabannin NDC
  • Habeeb Saleh Mohammed ya bayyana mamaki a kan yadda ake samun bullar rahoton cewa ana samun mummunar baraka da za ta gurgunta jam'iyyar NDC reshen jihar Kano
  • Game da zargin cewa Kwankwasi ya yi kokarin jan Peter Obi zuwa PRP saboda 'baraka a NDC, Habeeb Saleh Mohammed mai magana da yawun Kwankwasiyya ya yi bayani

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kano – Kungiyar Kwankwasiyya ta yi martani kan rahotannin da ke ikirarin cewa an samu baraka tsakanin jagoranta, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, da shugabannin jam'iyyar NDC na kasa.

A wata hira da ya yi da Legit, kakakin kungiyar, Habeeb Saleh Mohammed, ya bayyana cewa rahoton ana samun baraka a tsakanin mutanen biyu ba shi da tushe balle makama.

Kara karanta wannan

Yadda haduwa da Peter Obi zai jawo wa Kwankwaso asarar kuri'a a 2027

Kwankwasiyya ta karyata cewa akwai matsala a NDC reshen jihar Kano
Sanata Rabiu Musa Kwankwaso tare da Peter Obi Hoto: Rabiu Musa Kwankwaso
Source: Twitter

Rahoton da jaridar Nigerian Tribune ta wallafa ya yi ikirarin cewa Kwankwaso ya nuna rashin amincewa da yadda aka raba mukaman takara a jihar, abin da ake cewa ya janyo rashin jituwa a cikin jam'iyyar.

Martanin Kwankwasiyya kan rikicin NDC

Sai dai Habeeb Saleh Mohammed ya ce yana mamakin yadda ake yada irin wadannan rahotanni marasa tushe kan rikici a NDC.

Ya ce:

"90% na abin da ke cikin rahoton jita-jita ce. Bayan kowanne zaben fitar da gwani, ana samun wasu da ba su gamsu da sakamakon ba."

Ya kara da cewa:

"Wasu daga cikin wadannan mutane sun kai jam'iyyar kotu saboda korafe-korafensu. Bayan wannan, babu wani abu."

Kwankwaso ba zai koma PRP ba - Kwankwasiyya

Habeeb Saleh Mohammed ya kuma yi watsi da rade-radin da ke cewa Sanata Rabiu Musa Kwankwaso na shirin komawa jam'iyyar PRP daga NDC.

Kwankwasiyyata ce Kwanwkaso bai yi yunkurin barin NDC ba
Yan takara shugabancin Najeriya a NCD, Rabiu Musa Kwankwaso da Peter Obi lokacin da suka shiga ADC Hoto: Rabiu Musa Kwankwaso
Source: Facebook

A cewarsa:

"Jam'iyyar ta riga ta dora sunayen shugaban Peter Obi, Kwankwaso da na sanatoci."

Kara karanta wannan

Kwankwaso ya aika da sakon ta'aziyya kan rasuwar 'ya'yan tsohon mataimakin gwamna

Ya kara da cewa abin mamaki ne yadda ake ci gaba da yada rahotannin da ke ikirarin cewa ana fama da babban rikici a cikin jam'iyyar NDC reshen jihar Kano, alhali babu gaskiya a ciki.

Habeeb Saleh Mohammed ya bayyana cewa babu lokacin da aka samu wata baraka a tsakanin Kwankwaso da shugabanacin jam'iyyar NDC a jihar Kano game da takara.

NDC ta yi magana kan Gbajabiamila

A wani labarin, mun wallafa cewa jam'iyyar NDC ta bukaci tofa albarkin bakinta a kan badakalar da ake zargin shugaban ma'aikatan Gwamnatin Tarayya, Femi Gbajabiamila da aikata wa.

Daga cikin abubuwan da jam'iyyar NDC ta bukata akwai sauke Femi Gbajabiamila daga mukaminsa domin ba da damar gudanar da bincike mai zaman kansa a kan zarge-zargen da ake yi masa.

Haka kuma jam'iyyar ta ce zarge-zargen da Prince Mathew Adeniyi Adeyemi ya yi sun tayar da tambayoyi kan kasafin kuɗin kasar nan, asusu a babban bankin kasa na CBN da daukar ma'aikata.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng