Kiran da Sheikh Maqary Ya Yi wa Mabiya Darika a Jami'a a Rigimar Wazifa da ATBU

Kiran da Sheikh Maqary Ya Yi wa Mabiya Darika a Jami'a a Rigimar Wazifa da ATBU

  • Ana tunanin Ibrahim Ahmad Maqary ya yi magana a kan abubuwan da yake faruwa da ‘yan darika a jami’o’in Arewacin Najeriya
  • Limamin na Babban masallacin Abuja ya yi Allah-wadai da yadda ake hana mutane yin ibada irinsu wazifa da zikirori a makarantu
  • Duk abin da zai faru, Farfesa Ibrahim Ahmad Maqary ya ce bai dace a hana mutane su yi addini gwargwadon yadda suka fahimce shi ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

M. Malumfashi ya shafe shekaru 10 yana kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada

Abuja - Ibrahim Ahmad Maqary ya tofa albarkacin bakinsa game da matsalar da ake samu da mabiyar darika a wasu jami’o’i a Najeriya.

Farfesa Ibrahim Ahmad Maqary wanda yake limanci a babban masallacin kasa da ke Abuja y ayi kira a hada-kai kuma a gujewa samun rabuwar kai.

Farfesa Ibrahim Ahmad Maqary
Babban malamin Musulunci, Farfesa Ibrahim Ahmad Maqary tare da wasu shehunai Hoto: Farfesa Ibrahim Ahmad Maqary
Source: Facebook

Ibrahim Ahmad Maqary ya yi maganar rikicin jami'o'i

A wani fai-fai da Legit Hausa ta samu a shafin wani matashi a dandalin X, Jibril Khaleel, an ji malamin yana tir da abubuwan da ke faruwa.

Kara karanta wannan

Emefiele: Shekara 1 da rasuwa an nemi a jefa Marigayi Buhari a shari'ar satar $6.2m

Malamin addinin Musuluncin bai jin dadin yadda ake hana mabiyar dariku yin ibada a jami’o’i, musamman bayan abin da aka yi a garin Bauchi.

A jami’ar Abubakar Tafawa Balewa a Bauchi, har ta kai an ba kungiyar daliban Tijjaniya ta TIMSAH wuri domin ta gina masallacinta na dabam.

Daga baya gidan rediyon Albarka ya rahoto cewa hukumar jami'ar ATBU ta soke wannan mataki.

Da alama babban bai goyon bayan mabiya darika su ware su gina wani masallaci na dabam da wanda gama-garin musulmai suke sallah a ciki.

Sheikh Maqary ya fada wa masu bin darika cewa su shiga cikin ainihin kungiyar Musulman dalibai domin su ne suka fi cancanta da wannan rumfar.

Sheikh Ibrahim Maqary ya yi zargin ana danne darika

Tsokacin shehin ta yi kira da 'yan darika su hada-kai da sauran Musulmi, ya soki yadda ake hana bayin Allah yin ibadarsu kamar yadda suka fahimta.

Ya bada labarin abin da ya ce ya faru a wata jami’a, aka hana ‘yan darika yin wazifa cikin masallaci, da suka je fili suka yi kuma sai aka cafke su.

Kara karanta wannan

Bayanai sun fito da ake rade radin matsalar NDC ta jawo Kwankwaso zai koma PRP

Ibrahim Maqary ya ce wata rana wannan zai zama tarihi, ya kuma ce wadanda suka yi wannan abin sai sun ji kunya idan aka tado zancen nan gaba.

'Dole a bar ku, ku yi addininku' - Maqary

A karshe, limamin na Babban masallacin Abuja ya nuna ya zama dole almajiransu su bi duk wata irin hanya da za su iya domin su yi ibadarsu.

An ji shi yana mai cewa har a cikin musulman, wasu ba su goyon bayan abin da ake yi a jami'o'i.

Ko da za ta kai ana auka wa masu bin tafarkin darika da makami, babban malamin ya ba su kwarin guiwar cewa ka da su gajiya, su cigaba da addinsu.

Malamin ya kamanta danniyar da ya ce ake yi wa ‘yan darika a jami’a da ta’addanci a gidan ilmi.

Mansur Yelwa ya ajiye limancin jami'ar ATBU

An rahoto cewa Farfesa Mansur Isa Yelwa, wanda ya shafe sama da shekara 17 yana limanci a masallacin jami'ar ATBU da ke Bauchi, ya sauka daga aikin.

Wannan matakin ya biyo bayan jami'ar ta ba wa 'yan Darikar Tijjaniyya fili domin gina masallaci ba tare da tuntubarsa ba, wanda ya ce zai iya kawo rabuwar kai.

Malamin ya kara da cewa idan aka ba wata kungiya masallaci, hakan zai bude kofa ga sauran kungiyoyi kamar Qadiriyya da Izala su ma nemi nasu masallatan.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng