Jami’an ‘Yan Sanda Sun Damke Kakakin PDP bisa Zargin Taba Sanata a Facebook
- Ewa Okpo ya yi wasu maganganu da suka jawo ‘yan sanda suka damke shi kuma ana bincike na musamman a kan shi
- Wani tsohon sanata a Akwa Ibom, Effiong Bob ya zargi kakakin PDP da bata masa suna da kalamai da ya yi a Facebook
- Sanata Bob zai je kotu domin neman hakkinsa, ita kuwa uwar jam’iyyar za ta dage wajen ba Sakataren yada labaranta kariya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
M. Malumfashi ya shafe shekaru 10 yana kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada
Akwa Ibom - Jami’an ‘yan sandan Najeriya sun kama wani daga cikin kakakin PDP a rassan da jam’iyyar hamayyar ta ke da su a kasar nan.
‘Yan sandan Najeriya sun cafke Ewa Okpo ne saboda zargin bata suna da wasu laifuffukan da suke da alaka da amfani da dandalin sada zumunta.

Source: Getty Images
Tsohon sanata ya kai kakakin PDP wajen 'yan sanda
Abin da aka samu daga jaridar Premium Times ta ce wani tsohon sanata, Effiong Bob ne ya kai korafin Mista Ewa Okpo wajen ‘yan sanda.
Karar da Sanata Effiong Bob ya shigar tun ranar 17 ga watan Yuni 2026 suka jawo aka damke shi.
‘Dan siyasar ya zargi Sakataren yada labaran PDP na reshen jihar Akwa Ibom da yin wasu bayanai na wulakanci da za su iya taba kimarsa.
'Yan sanda sun fitar da jawabi a Facebook
Jawabin da ‘yan sanda suka wallafa a shafin Facebook ya ce an bi doka wajen kama kakakin na PDP kuma yana bada hadin-kai wajen bincike.
Kakakin jami’an a Akwa Ibom, Timfon John ya ce dokar kasa ta ba kowa yancin fadan ra’ayinsa, amma hakan bai tsallaka zuwa ga yin laifi ba.
Jawabin DSP Timfon John ya kare da gargadin jama’a cewa dandalin sada zumunta na zamani ba wuri ne da za a rika zuwa na yin aikin assha ba.
Rundunar ta kuma ja kunnen daidaikun mutane duk wanda ya labarin karya, ci zarafin wani, keta alfarma ko ya yi barazana zai ji babu dadi.
Duk wanda aka samu yana yada wani daga cikin wadannan ayyukan laifi da aka aikata, zai fuskanci fushin hukuma idan bincike ya zo kan shi.

Kara karanta wannan
Akwai dalili: Gwamnatin tarayya za ta rushe tsarin karatun sakandare na JSS da SSS
Da zarar an gudanar da bincike kuma aka samu mutum da laifi, John ya ce za a gurfanar da wanda ake zargi.

Source: Getty Images
Meyasa sanata ya kai batun ga 'yan sanda?
Sanata Bob wanda ya kai maganar wajen jami'an ‘yan sanda ya yi watsi da zargin da ake yi masa na yi wa ‘dan jam’iyyar hamayyar barazana da hukuma.
“Ya bata mani suna. Ya bude Facebook, ya yi sama da awa guda yana magana a kai na. Ya ce mani dan damfara, ya ce ban taba taimakon kowa ba.”
Tsohon ‘dan majalisar dattawan kasar ya ce ba sukar gwamnatin Akwa Ibom da aka yi ta jawo ya kai kara ba, illa kokarin bata masa suna da kima a idon duniya.
“Na ce ne kana da damar sukar gwamna, amma kar ka taba mutuntukkarsa. Kana da damar sukar manufofi da sha’anin aiwatar da ayyuka ko batun kokari ko rashin shi a ofis. Maimakon wadannan, sai ya zabi ya ci mani zarafi.”
Jam'iyyar PDP za ta kare kakakinta na Akwa Ibom
Tsohon sanatan ya ce ya san doka da kyau domin shi lauya ne tun a 1984 don haka ba zai zura ido ana bata shi ba, sai dai PDP NEC ta yi tir da lamarin.
PDP ta bakin kakakinta na kasa, Ini Ememobong, ta ce abin bai yi zafin da za a hada da ‘yan sanda ba, ya zargi jami’an da ganin bayan ‘yan adawa.
Ini Ememobong ya ce uwar jam’iyya za ta yi kokarin tattaro lauyoyi su kare Okpo a gaban kuliya.
Sauya sheka ta ci kujerar 'dan majalisar NDC
Kamar wasa sai aka ji cewa ‘dan majalisa mai wakiltar mazabar Udu a jihar Delta zai rabu da kujerar da yake kai a dalilin barin APC zuwa jam'iyyar NDC.
‘Dan majalisar Delta da ya shiga NDC daga APC, Hon. Collins Egbetamah ya rasa kujera kuma har majalisa ta bukaci hukumar INEC ta yi sabon zabe.
An kafa hujja da sashe na 109(1)(g) & (2) na kundin tsarin mulkin Najeriya na shekarar 1999 da aka yi wa kwaskwarima wajen tsige shi daga kan kujerarsa.
Asali: Legit.ng

