Jigawa: PDP Ta Gama Tantance wa, Ta Sake Mika Takarar Gwamna ga Ɗan Sule Ladimo

Jigawa: PDP Ta Gama Tantance wa, Ta Sake Mika Takarar Gwamna ga Ɗan Sule Ladimo

  • Mustapha Sule Lamido, wanda shi ne ɗan takarar gwamnan Jigawa na jam'iyyar PDP a 2023, ya sake shiga takarar gwamnan jihar a zaɓen 2027
  • Santurakin Dutse ya miƙa fom din takararsa ga kwamitin amintattu na PDP na jihar Jigawa a ranar Talata, kuma ya ce tuni sun amince masa
  • Mustapha Lamido ya yi ikirarin cewa jam'iyyun da suka karbi mulki daga PDP sun lalata Jigawa da kuma Najeriya, don haka akwai bukatar canji

Sani Hamza ƙwararren edita ne a fannin nishaɗi, al'amuran yau da kullum, da kuma siyasa, wanda ke da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Jigawa - Mustapha Sule Lamido, tsohon d'an takarar gwamnan Jigawa a zaben 2023 karkashin PDP, ya sake shiga zaben gwamnan jihar na 2027.

Tsohon dan takarar ya karbi fom din tsayawa takara kuma ya mika shi ga kwmaitin gudanarwa na jam'iyyar PDP da sauran masu ruwa da tsaki a ranar Talata don sanya masa albarka.

Kara karanta wannan

"Haka Allah ya tsara," 'Dan takarar APC, Jamilu Gwamna ya nemi hadin kan Pantami a Gombe

Mustapha Sule Lamido ya karbi fom din takarar gwamnan Jigawa karkashin jam'iyyar PDP.
Mustapha Sule Lamido ya karbi fom din takarar gwamnan Jigawa karkashin jam'iyyar PDP a Dutse. Hoto: Mustapha Sule Lamido
Source: Facebook

"Mun yarda da PDP" - Mustapha Sule Lamido

Mustapha Sule Lamido, wanda ɗa ne ga tsohon gwamnan jihar Jigawa Sule Lamido, ya bayyana cewa burinsa shi ne ya dawo da ingantaccen shugabanci da kuma gina amincewar jama'a ga jagoranci, in ji rahoton Punch.

Bayan ganawa da masu ruwa da tsaki a garin Dutse, ya bayyana cewa sun yi amanna da falsafar jam'iyyar PDP da kuma ƙarfinta na tunkarar ƙalubalen cikin gida.

Mustapha Sule Lamido ya bayyana cewa:

"Mu cikakkun 'yan jam'iyyar PDP ne, kuma mun gamsu da manufofin jam'iyyarmu, karfinta da kuma jajurcewarta na magance rikice-rikicen cikin gida.
“Muna da kyakkyawan yaƙini ga jam'iyyarmu, kuma mun yi amanna cewa mutanen Jigawa da ma ƴan Najeriya sun yarda da ita kamar yadda muka yi”.

Mustapha ya soki sukar sauran jam'iyyun siyasa

A lokacin da yake jawabi, Mustapha Lamido ya soki sauran jam'iyyun siyasa da suka karɓi mulki bayan PDP, inda ya bayyana cewa sun gaza cika burin al'umma baki ɗaya.

Kara karanta wannan

Bayan rasa mukaminsa, ministan Tinubu ya koma PDP domin takarar gwamna

Ya kafa hujja da cewa babu wata jam'iyya da ta kai PDP yin ayyukan da suka taɓa rayuwar jama'a kai-tsaye ta hanyar ayyukan raya ƙasa da shirye-shirye masu amfani.

Haka kuma, ya bayyana cewa maimakon gwamnati mai ci ta magance matsalolin tattalin arziki, zamantakewa, da na tsaro, sai ma ƙara dagula su da ta yi.

Ya zargi jam'iyyun da ke adawa da PDP da raunana yanayin ƙasar ta hanyar amfani da manufofi marasa tasiri tun bayan karɓar mulki daga hannun jam'iyyarsu.

Mustapha Sule Lamido ya ce zai yi aiki tukuru don gyara barnar da jam'iyyun adawa suka yi a Jigawa bayan karbar mulki daga hannun PDP
Shugabannin PDP a Jigawa suna sanya hannu kan fom din takarar Mustapha Sule Lamido. Hoto: Mustapha Sule Lamido
Source: Facebook

PDP ta ba Mustapha Lamido takara

A wani sako da ya wallafa a shafinsa na Facebook, Mustapha Lamido ya gode wa PDP bisa sake ba shi takarar gwamna, inda ya ce:

"Ina godiya ga dukkan shugabanni, masu ruwa da tsaki da sauran ƴan jam'iyyar PDP ta Jihar Jigawa bisa fitar da ni da suka yi a matsayin wanda zai yi wa jam'iyyar takarar gwamna a zaɓen 2027 a yau.
"Ina addu'ar Allah Ya bamu nasara, Ya bamu ikon ceto jiharmu da ƙasarmu daga halin da take ciki."

Karanta sakonsa a kasa:

Mustapha ya fadi kuskuren 'yan Najeriya a 2023

Kara karanta wannan

APC ko ADC: Gwamna Makindee ya fadi jam'iyyar da za ta samar da shugaban kasa a 2027

A wani labari, mun ruwaito cewa, tsohon dan takarar gwamnan PDP a Jigawa, Mustapha Sule Lamido, ya soki APC da masu kada kuri’a, inda ya ce da gangan aka shiga wahala.

'Dan tsohon gwamna Jigawa, Sule Lamido ya ce tun a zaben 2023 suka gargadi yan Najeriya kan zaben APC amma sun ki ji, yanzu kuma kowa na ji a jikinsa.

Yayin wani shirin tallafawa al’umma a Birninkudu/Buji da Yakubu Danmaliki ya shirya, Lamido ya yabawa d'an majalisar wakilan PDP bisa jajircewarsa a samar da ayyukan raya jama’a.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com