Sheikh Gumi Ya Sake Magana kan Sulhu da Ƴan Bindiga, Ya Yaba Jonathan, Osinbajo
- Sheikh Ahmad Abubakar Mahmud Gumi ya kakubalanci gwamnatoci game da yin sulhu da ƴan ta'adda a Najeriya
- Gumi ya sake kira ga gwamnati ta tattauna da 'yan Boko Haram da masu garkuwa, yana kwatanta hakan da yadda aka sasanta rikicin Neja Delta
- Malamin ya ce tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan da Yemi Osinbajo sun tattauna da mayaƙan Neja Delta, abin da ya taimaka wajen samar da shirin afuwa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Kaduna - Sheikh Ahmad Abubakar Mahmud Gumi ya sake yin magana game da zama da ƴan ta'adda.
Malamin ya kuma yin kira da a tattauna da kungiyoyin masu dauke da makamai, yana tambayar dalilin da ya sa ba a yi wa 'yan Boko Haram da masu garkuwa irin tsarin da aka yi wa mayaƙan Neja Delta ba.

Source: Facebook
Hakan na cikin sakonsa na a kafofin sadarwa wanda Punch ta bibiya a ranar Asabar 25 ga watan Yulin 2026.
Gumi ya tuna ziyarar Jonathan a Neja Delta
Gumi ya tuna cewa tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan da tsohon mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo sun gana da mayaƙan Neja Delta domin neman zaman lafiya.
A cewarsa:
"Tsohon shugaban kasa Jonathan ya ziyarci mayaƙan Delta a cikin rafuka, haka kuma Osinbajo. Dukkansu sun samar da wani shiri da ya taimaka wajen dakile ayyukan mayaƙan.
"Wa zai je wajen 'yan Boko Haram da masu garkuwa domin sasanta su ba tare da wawaye sun rika suka ba?"
Sheikh Gumi ya dade yana bayyana cewa tattaunawa na daga cikin hanyoyin da za su taimaka wajen magance matsalar tsaro a Arewa maso Yamma da Arewa maso Gabas.
A shekarun baya, ya kai ziyara sansanonin wasu kungiyoyin masu dauke da makamai a Zamfara, yana mai cewa tattaunawa na iya samar da zaman lafiya mai dorewa fiye da amfani da karfin soja kadai.

Kara karanta wannan
Ganduje ya tsokano NDC da Obidents, sun yi masa raddi mai zafi kan taba Obi, Kwankwaso

Source: UGC
Gumi ya musanta zargin alaka da ta'addanci
Malamin ya sha musanta zargin cewa yana goyon bayan ta'addanci, yana cewa duk wata hulda da yake yi da masu dauke da makamai domin inganta zaman lafiya ce, rage zubar da jini da kuma karfafa shirye-shiryen gyaran hali.
An kuma tuna cewa Jonathan ya taba ganawa da tsohon jagoran mayaƙan Neja Delta, Government Ekpemupolo wanda aka fi sani da Tompolo, tun yana mataimakin shugaban kasa, yana bayyana hakan a matsayin muhimmin mataki kafin samar da shirin afuwar.
Hakazalika, Osinbajo ya ziyarci al'ummomin Neja Delta a shekarar 2017 lokacin da yake mukaddashin shugaban kasa, inda ya gana da shugabanni da masu ruwa da tsaki, yana cewa yankin na da korafe-korafe na gaskiya da suka dace a warware ta hanyar tattaunawa maimakon amfani da karfi kawai.
Gumi ya musanta alaka da sace daliban Oyo
A baya, an ji cewa Sheikh Ahmad Gumi ya yi magana game da neman tsoma shi cikin lamarin sace dalibai da aka yi a wata makaranta a jihar Oyo.
Gumi ya bayyana cewa bai je Ibadan bisa gayyatar Musulman Kudu maso Yamma ba, illa wakiltar malaman Musulunci na Arewa.
Malamin ya danganta sukar da aka yi masa da siyasar tsoron Musulunci, yana goyon bayan MURIC kan batun shari'ar Oyo.
Asali: Legit.ng

