2027: Maza da Mata Sun Fito Gangamin Nuna Goyon baya ga Tazarcen Tinubu a Kwara
- Jam'iyyar APC a jihar Kwara ta fara gangamin neman goyon bayan tazarcen Shugaba Bola Tinubu da kuma shirye-shiryen babban zaɓen 2027
- Jagororin APC sun ce zaɓen fitar da gwani ya gudana cikin lumana, kuma an kafa kwamitin sulhu domin sasanta rashin jituwa a jam'iyyar
- Ɗan takarar gwamna daga Kwara ta Arewa, Ahmad Muhammad, ya yabawa jam'iyyar kan bai wa yankin damar tsayar da gwamna a 2027
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza ƙwararren edita ne a fannin nishaɗi, al'amuran yau da kullum, da kuma siyasa, wanda ke da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
Kwara – Jam'iyyar APC a jihar Kwara ta fara gangamin wayar da kan magoya bayanta domin tunkarar babban zaɓen shekarar 2027, tare da nuna goyon baya ga tazarcen Shugaba Bola Ahmed Tinubu.
Gangamin, wanda ƙungiyar Kwara Progressives ta shirya ƙarƙashin taken "Kwara Ndupe (Kwara na godiya)", ya haɗa shugabannin jam'iyyar, 'yan takara da dubban magoya baya da suka yi jerin gwano a manyan titunan Ilorin.

Source: Facebook
An gudanar gangamin APC kan tazarcen Tinubu
Masu shirya taron sun bayyana cewa manufar gangamin ita ce murnar nasarar zaɓen fidda gwani da kuma fara shirye-shiryen yaƙin neman zaɓen 2027, in ji rahoton Punch.
Da yake zantawa da manema labarai, mai kula da ƙungiyar Renewed Hope Ambassadors a jihar, Abdulateef Alakawa, ya ce an shirya taron ne domin gode wa Allah bisa yadda zaɓen fidda gwani ya gudana cikin kwanciyar hankali.
Ya ce tsarin zaɓen kai tsaye da jam'iyyar ta yi amfani da shi ya bai wa mambobi damar bayyana ra'ayinsu, kuma hakan ya samar da 'yan takarar da za su wakilci APC a matakai daban-daban.
Alakawa ya kuma jaddada cewa APC ta Kwara na ci gaba da mara wa Shugaba Tinubu da Gwamna AbdulRahman AbdulRazaq baya.
APCta fara sasanta masu ruwa da tsaki
Alakawa ya yi watsi da ra'ayin cewa sakamakon zaɓen fidda gwani zai iya janyo rabuwar kai a jam'iyyar.

Kara karanta wannan
2027: Malami ya gana da ɗan takarar mataimakin shugaban ƙasa na jam'iyyar ADC a Abuja
A cewarsa, APC ta riga ta kafa kwamitin sulhu domin sasanta duk wani rashin jituwa tsakanin masu ruwa da tsaki kafin babban zaɓen 2027.
Ya ce duk da cewa a kowace gasa akwai masu nasara da waɗanda ba su yi nasara ba, jam'iyyar ba ta ɗauki kowa a matsayin wanda ya yi rashin nasara.
'Dan takarar gwamna ya yabawa shugabannin APC
Ɗan takarar gwamnan APC daga yankin Kwara ta Arewa, Ahmad Muhammad, ya yabawa jam'iyyar bisa ware kujerar gwamna ga yankin.
Ya gode wa Shugaba Tinubu, Gwamna AbdulRahman AbdulRazaq da mambobin APC bisa amincewar da suka nuna masa.
Muhammad ya ce gangamin ya nuna irin goyon bayan da jam'iyyar ke da shi a faɗin jihar, yana mai bayyana kwarin gwiwar cewa APC za ta ci gaba da riƙe mulki bayan zaɓen 2027.
Haka kuma, ɗan takarar APC na kujerar Sanatan Kwara ta Kudu, Olalekan Adewoye, ya gode wa shugabannin jam'iyyar bisa damar da aka ba shi, yana mai cewa APC ta ci gaba da kasancewa jam'iyya mai haɗin kai da manufar cimma nasara tare.
Asali: Legit.ng
