Dole Shugaban kasa Buhari ya bar ofis a 2019 – Inji Atiku Abubakar

Dole Shugaban kasa Buhari ya bar ofis a 2019 – Inji Atiku Abubakar

Mun ji labari cewa ‘Dan takarar Shugaban kasa na Jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar yayi alkawari cewa zai dage wajen ganin Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bar Fadar Shugaban kasa a shekara mai zuwa.

Dole Shugaban kasa Buhari ya bar ofis a 2019 – Inji Atiku Abubakar
Saboda kishin kasa na dawo da ‘Ya ‘ya na da ke Turai Najeriya – Atiku
Asali: UGC

Alhaji Atiku Abubakar ya bayyana wannan ne a lokacin da ya gana da wasu Dattawan Kasar Inyamurai a Garin Enugu jiya. Atiku yake cewa ko da bai yi nasara a 2019 ba, zai yi kokarin ganin Shugaba Buhari ya bar kan karagar mulki.

Kungiyar Inyamuran nan ta Ohaneze Ndigbo ta nemi jin ta-bakin Atiku game da batun yi wa kasa garambawul. Shugaban Kungiyar, Nnia Nwodo shi ne yayi wa Atiku wannan tambaya inda ‘Dan takarar yace masa yana tare da su.

KU KARANTA: Zargin rashawa: An ba Shugaba Buhari kwana 14 ya binciki Gwamnan APC

Atiku ya koka da yadda mulkin Buhari ya raba kan ‘Yan Najeriya inda yace ba a taba samun lokacin da Najeriya ta kece kamar yanzu ba, tun bayan yakin Basasa da aka yin a Biyafara. Atiku yace dole a samu kishin kasa da hadin kai.

Atiku Abubakar ya kara da cewa saboda kishin kasa ya dawo da ‘Ya ‘yan sa da ke Turai zuwa Najeriya domin ganin kasar nan ta gyaru. Shugaban Majalisar Dattawa, Bukola Saraki ya nemi mutanen Ibo su shirya zaben Atiku a 2019.

Shugaban PDP, Uche Secodus da sauran Jiga-jigan Jam’iyyar sun koka da yadda ake kashe jama’a kamar Awaki a Gwamnatin nan ta Shugaban kasa Muhammadu Buhari tun da ta karbi mulki a 2015.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng