An ba Tinubu Shawarar Wanda Zai Dauko a Matsayin Mataimakinsa a Zaben 2027
- Wani jagoran Yarabawa ya bai wa Shugaba Bola Ahmed Tinubu shawara ya sauya mataimakinsa a zaben 2027 mai zuwa
- Hakan na zuwa ne yayin da ake ci gaba da rade-radin Tinubu na iya ajiye Kashim Shettima, ya dauki sabon abokin takara a APC
- Oyedele Oyewumi ya bukaci Shugaba Bola Tinubu ya mika kujerar shugaban majalisar dattawa na gaba ga yankin Kudu maso Gabas
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Lagos, Nigeria - Wani jagoran Yarabawa kuma mai sharhi kan harkokin jama'a, Dr Oyedele Oyewumi, ya bukaci Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya rungumi tsarin siyasa mai hada kan kasa gabanin zaben 2027.
Oyewumi ya bayyana hakan ne a Legas ranar Alhamis, inda ya ce ya dace shugaban kasa ya yi la'akari da zabar mataimakin shugaban kasa daga ƙabilar Hausa/Fulani.

Source: Facebook
An bukaci Tinubu ya hada kan ƙasa
Jaridar Guardian ta ruwaito cewa Oyewumi ya kuma bukaci Tinubu ya goyi bayan mika kujerar shugaban majalisar dattawa ga yankin Kudu maso Gabas idan ya samu nasara a 2027.
A cewarsa, irin wannan tsari zai karfafa hadin kan kasa, ya tabbatar da raba madafun iko bisa tsarin tarayya, tare da bai wa kowane yanki damar jin cewa yana da muhimmiyar rawa a cikin tsarin mulkin Najeriya.
Ya yi nuni da kalaman tsohon shugaban kasa, Olusegun Obasanjo, wanda ya taba gargadin cewa Najeriya ta kauce wa duk wani yanayi da zai iya haifar da rabuwar kai kamar yadda aka gani kafin yakin basasa na 1967 zuwa 1970.
Oyewumi ya yabawa sauye-sauyen Tinubu
Oyewumi ya ce Shugaba Tinubu ya nuna jarumtaka wajen aiwatar da sauye-sauyen tattalin arziki da tsarin mulki, kuma yanzu yana da wata dama ta kara gina tarihinsa ta hanyar tabbatar da shugabanci mai kunshe da kowa.
Ya ce:
"Shugaban kasa ya nuna jarumtaka wajen daukar matakai masu wahala domin ci gaban kasa, kuma muna ci gaba da karfafa masa gwiwa ya yi fiye da haka."
Ya kara da cewa yayin da ake tunkarar sabon zagayen zabe, akwai bukatar a kara tabbatar da hadin kan kasa ta hanyar adalci wajen rabon mukaman siyasa.
Ana so Tinubu ya canza Shettima
Oyewumi ya bayyana cewa Mataimakin Shugaban Kasa, Kashim Shettima, dan kabilar Kanuri ne daga Maiduguri a Jihar Borno, kuma ya taba bayyana cewa yana da alaka ta jini da al'ummar Fulani.

Source: Facebook
Sai dai ya yi kira da a yi la'akari da zabar dan takarar mataimakin shugaban kasa daga Hausa/Fulani tare da bai wa yankin Kudu maso Gabas shugabancin majalisar dattawa.
A cewarsa, hakan zai nuna bambancin Najeriya tare da tabbatar wa dukkan yankuna cewa suna da muhimmiyar rawa a tsarin dimokuradiyya.
Oyewumi ya kuma bukaci Shugaba Tinubu ya fifita maslahar kasa fiye da tsofaffin sabanin siyasa, cewar rahoton Daily Post.

Kara karanta wannan
DSS da yan sanda sun yi bincike, an ji gaskiya kan ɓullar sabuwar ƙungiyar ta'addanci a Najeriya
Jagoran NDC ya hango faduwar Tinubu
An ji cewa jagoran NDC na ƙasa, Sanata Seriake Dickson, ya ce shugaba Bola Tinubu da APC za su sha kaye idan aka gudanar da zaɓen 2027 cikin gaskiya.
Sanatan ya yi kira da a bi tsarin dimokuraɗiyya, inda ya buƙaci hukumomi su bai wa dukkan jam'iyyun siyasa da ke son yin takara damar shiga zaɓe ba tare da katsalandan ba.
Maganganun jagoran na zuwa ne a daidai lokacin da NDC ta shiga cikin rudanin siyasa bayan kotu ta yi umarni a soke rajistar jam'iyyar.
Asali: Legit.ng

