Ba Atiku ba ne, ADC Tsagin Nafiu Bala ta Tsaida Dan Takarar Shugaban Kasa
- Tsagin jam'iyyar ADC karkashin jagorancin Nafiu Bala Gombe ya tsayar da dan takarar shugaban kasa a zaben 2027
- Nafiu Bala Gombe ya bayyana cewa an zabi dan takarar shugaban kasar ne ta hanyar yin amfani da tsarin maslaha
- Hakazalika, tsagin na ADC mai adawa ya mika tutar jam'iyyar ga 'yan takarar gwamna a jihohi 29 na tarayyar Najeriya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza ƙwararren edita ne a fannin nishaɗi, al'amuran yau da kullum, da kuma siyasa, wanda ke da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
FCT, Abuja - Wani ɓangare na jam'iyyar ADC ya bayyana ɗan kasuwa, Farfesa Chris Uba, a matsayin ɗan takararsa na shugaban ƙasa a babban zaɓen 2027.
Hakan na zuwa ne biyo bayan kammala zaɓubbukan fitar da gwani na jam'iyyar a faɗin ƙasa baki ɗaya.

Source: Twitter
Jaridar The Punch ta ce ɓangaren jam'iyyar ADC ƙarƙashin jagorancin Nafiu Bala Gombe ya kuma miƙa tutoci ga 'yan takarar gwamna guda 29 a faɗin shiyyoyin siyasa guda shida na ƙasar a ranar Lahadi, 31 ga watan Mayun 2026.
Nafiu Bala ya yi jawabi
Yayin da yake magana a lokacin miƙa wa 'yan takarar tutocin a hukumance a Abuja, Nafiu Bala Gombe, ya ce an ware tikitin shugabancin ƙasar ne ga Kudancin Najeriya domin dacewa da madaidaitan ginshiƙai na daidaito, adalci, haɗa kai, da kuma tsarin raba daidai na tarayya.
A cewarsa, masu neman takara guda uku ne da farko suka sayi fam ɗin na gani ina so da na tsayawa takara na jam'iyyar domin fafatawa a tikitin shugabancin ƙasar.
“Su ne Dakta Bashir Sani, Prince Williams Charles, da kuma Farfesa Chris Uba."
- Nafiu Bala Gombe
Wanene wanda aka ba takara?
Nafiu Bala Gombe ya bayyana cewa jam'iyyar ta ɗauki tsarin maslaha da aka tanada a ƙarƙashin dokar zaɓe, wanda hakan ya kai ga samar da Chris Uba a matsayin ɗan takararta ɗaya tilo na shugaban ƙasa bayan janyewar sauran masu neman takarar.
“Bisa bin tsarin raba daidai na tarayya da kuma dacewa da sashe na 84(2) na dokar zaɓe ta shekarar 2026, wanda aka yi wa gyaran fuska, wanda ya amince da tsarin maslaha a matsayin halatacciyar hanya ta zaɓen 'yan takara na 'yan jam'iyyun siyasa, jam'iyyar ADC ta ɗauki tsarin maslaha a matsayin hanyar zaɓen fitar da gwaninta na shugaban ƙasa, gwamna, Majalisar tarayya, da na Majalisun dokoki na jihohi."

Kara karanta wannan
Gwamna Makinde ya samu tikitin takara, zai gwabza da Atiku da Tinubu a zaben 2027
“Bisa ga wannan tanadi kuma domin muradin haɗin kan jam'iyya, mutane biyu daga cikin masu neman takarar shugabancin ƙasa na jam'iyyar sun janye jikinsu da son ransu kuma suka amince da Farfesa Chief Chris Uba a matsayin ɗan takarar shugaban ƙasa ɗaya tilo na jam'iyyar."
“Sakamakon haka, an bayyana Farfesa Uba a matsayin ɗan takarar haɗin gwiwa kuma aka zaɓe shi bisa ƙa'ida domin ya wakilci ADC a matsayin mai ɗauke da tutarta na shugaban ƙasa a babban zaɓen shekarar 2027.”
- Nafiu Bala Gombe

Source: Facebook
Dan El-Rufai ya samu tikitin ADC
A wani labarin kuma, kun ji cewa dan tsohon gwamnan Kaduna, Bello El-Rufai, ya samu nasara a zaben fitar da gwani na jam'iyyar ADC.
Bello El-Rufai ya lashe zaɓen fitar da gwani na jam’iyyar ADC ba tare da samun wani abokin hamayya ba domin tsayawa takarar kujerar Kaduna ta Arewa.
Hon. Bello ya gode wa shugabannin jam’iyyar, wakilai, masu ruwa da tsaki, magoya baya da al’ummar Kaduna North saboda amincewa da goyon bayan da suka nuna masa.
Asali: Legit.ng
