Kano Ta Yi Gaba, Jihohi Sun Biyo Ta da Mutum Miliyan 6 Suka Yanki Katin Zabe
- Hukumar INEC ta bayyana cewa ta yi rajistar sababbin masu kada ƙuri'a 6,885,330 a matakai uku na rajistar masu zaɓe gabanin zaɓen 2027
- Jihar Kano ce ta fi kowace jiha yawan sabbin masu rajista, sai Legas da Sokoto, yayin da matasa da mata suka fi yawa a cikin waɗanda suka yi rajista
- INEC ta ce adadin da aka bayyana na wucin gadi ne saboda har yanzu ana tantance bayanai tare da cire waɗanda suka yi rajista fiye da sau ɗaya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja – Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) ta bayyana cewa ta yi rajistar sababbin masu kada ƙuri'a 6,885,330 a duk faɗin Najeriya yayin gudanar da rajistar masu zaɓe ta dindindin (CVR) domin babban zaɓen shekarar 2027.
An samu wannan adadi ne bayan kammala matakai uku na rajistar masu zaɓe, inda aka kuma tsawaita wa'adin rajistar da makonni biyu daga ranar 10 ga Yuli zuwa ranar 26 ga Yuli, 2026.

Source: Facebook
Sai dai INEC ta bayyana wa Daily Trust cewa har yanzu wannan adadi na wucin gadi ne, domin ana ci gaba da tantance bayanan masu rajista kafin fitar da adadi na ƙarshe.
Yadda rajistar ta gudana
A cewar shugaban kwamitin yaɗa bayanai da wayar da kan masu zaɓe na INEC, Mohammed Kudu Haruna, mataki na uku shi ne na ƙarshe a shirin rajistar.
Rahotanni sun nuna cewa mataki na farko da aka gudanar tsakanin watan Agusta zuwa Disamban 2025 ya samar da sababbbin masu rajista 2,685,725.
Mataki na biyu kuma ya ƙara mutum 1,228,648, yayin da mataki na uku ya kawo adadin zuwa 2,970,957, wanda ya sa jimillar rajistar ta haura miliyan 6.8.
Hukumar ta ce za ta baje kundin masu zaɓe a watan Agusta domin bai wa jama'a damar gabatar da ƙorafe-ƙorafe ko gyaran bayanai.
Kano ta fi jihohi masu rajista
Binciken alkaluman da INEC ta fitar ya nuna cewa jihar Kano ce ta fi yawan sababbin masu rajista da mutum 465,964.
Rahoton da Punch ta wallafa ya nuna cewa Legas ta biyo baya da mutum 350,337, yayin da Sokoto ta zo ta uku da mutum 338,730.
Sauran jihohin da suka samu yawan rajista sun haɗa da Imo da mutum 251,309, Osun da mutum 238,240 da kuma Borno da mutum 201,724.

Source: Twitter
A yankuna shida na ƙasar, yankin Arewa maso Yamma ne ya fi yawan sababbin masu rajista da mutum 1,560,531, yayin da Arewa maso Gabas ce ta samu mafi ƙarancin adadi.
Rahoton INEC ya nuna cewa mata sun fi maza yawan rajista a mataki na uku. An bayyana cewa mata sun kai mutum 1,561,765, wanda ya kai kashi 52.57 cikin 100, yayin da maza suka kai mutum 1,409,192, wato kashi 47.43 cikin 100.
Magana kan sahihin zabe
A wani labarin, mun ruwaito cewa shugaban INEC, Farfesa Joash Amupitan, ya tabbatar wa 'yan Najeriya cewa za a yi sahihin zabe a 2027.
Ya bayyana hakan ne yayin wata ziyarar girmamawa da ya kai wa tsohon shugaban ƙasa, Janar Abdulsalami Abubakar mai ritaya, a Minna.
Shi ma Janar Abdulsalami ya buƙaci 'yan Najeriya su bai wa INEC cikakken goyon baya domin tabbatar da gudanar da sahihin zaɓe cikin lumana.
Asali: Legit.ng

