2023: Bola Tinubu Ya Lashe Zaben Kananan Hukumomi 10 a Jihar Ekiti

2023: Bola Tinubu Ya Lashe Zaben Kananan Hukumomi 10 a Jihar Ekiti

  • Baturen zabe na jihar Ekiti, Farfesa Akeem Lasisi, ya fara karban sakamakon zaben shugaban kasa daga kananan hukumomi
  • Zuwa yanzu ya tattara sakamako guda 10 kuma ɗan takarar jam'iyyar APC, Asiwaju Bola Tinubu, ne ya samu nasara
  • A jiya Asabar 10 ga watan Fabrairu, 2023, yan Najeriya suka futa suka zabi wanda zai gaji shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari

Ekiti - Hukumar zabe ta ayyana Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, ɗan takarar shugaban kasa a inuwar jam'iyyar APC, a matsayin wanda ya lashe zabe a kananan hukumo 10 a jihar Ekiti.

Baturen zaben INEC na jihar kuma shugaban jami'ar lafiya ta tarayya da ke Ila Orogun, jihar Osun, Farfesa Akeem Lasisi, shi ne ya bayyana sakamakon yankunan.

Bola Ahmed Tinubu.
Bola Ahmed Tinubu ya ɗaga tsintsiya a wurin kamfe. Hoto: dailytrust
Asali: UGC

Ya ce Tinubu ya samu nasara da kuri'u mafiya rinjaye a waɗan nan kananan hukumomin yayin da Atiku Abubakar, na jam'iyyar PDP ke yake masa baya a matsayin na biyu.

Kara karanta wannan

Atiku Ya Kunyata a Gida, Peter Obi Ya Dankara PDP da Kasa a Kauyen Jihar Adamawa

Rahoton Daily Trust ya nuna cewa tsohon gwamnan Anambra kuma ɗan takarar shugaban ƙasa a inuwar Labour Party, Peter Obi ne ya zo na uku, sai kuma Kwankwaso na NNPP.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Legit.ng ta haɗa maku sakamakon zaben daga kananan hukumomin guda 10, gasu kamar haka;

Karamar hukumar Efon Alaaye

APC 5873

LP 125

NNPP 03

PDP 2521

Ƙaramar hukumar Gboyin

APC 11,969

LP 245

NNPP 11

PDP 4178

Karamar hukumar Ijero

APC 12628

LP 373

NNPP 06

PDP 5731

Karamar hukumar Ikere

APC 11659

LP 910

NNPP 24

PDP 7198

Karamar hukumar Ise-Orun

APC 11415

LP 497

NNPP 10

PDP 2734

Karamar hukumar Ido/Osi

APC 11917

LP 782

NNPP 14

PDP 7476

Karamar hukumar Irepodun/Ifeodun

APC 14265

LP 544

NNPP 24

PDP 5516

Karamar hukumar Ekiti ta yamma

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Dino Melaye Ya Kawo Wa Atiku Akwatinsa A Kogi, Duba Sakamakon

APC 14516

LP 391

NNPP 10

PDP 4318

Karamar hukumar Moba

APC 12,046

LP 246

NNPP 11

PDP 5847

Karamar hukumar Ikole

APC 15465

LP 779

NNPP 11

PDP 10198

A wani labarin kuma Atiku Ya Lallasa Tinubu a Daya Daga Cikin Akwatin Gidan Gwamnatin Kaduna

Duk da gwamna El-Rufai na jihar Kaduna mamba ne a APC amma hakan bai hana mutanen cikin gwamnatin jihar su juya wa Bola Ahmed Tinubu baya ba.

A ɗaya daga cikin akwatun gidan gwamnatin, Atiku Abubakar na PDP ya samu nasara kan Tinubu, Obi da Kwankwaso.

Asali: Legit.ng

Online view pixel