Tinubu, Atiku ko Obi? Gwamnoni 5 Sun Yi Matsaya 1, Sun Faɗi Ɗan Takararsu a 2027

Tinubu, Atiku ko Obi? Gwamnoni 5 Sun Yi Matsaya 1, Sun Faɗi Ɗan Takararsu a 2027

  • Gwamna Hope Uzodimma ya ce gwamnonin Kudu maso Gabas biyar sun cimma matsaya ta goyon bayan sake zaben Bola Tinubu a 2027
  • Ya ce matakin ya samo asali ne daga ayyukan ci gaba da gwamnatin Tinubu ta aiwatar a yankin, ciki har da kafa Hukumar Raya Kudu maso Gabas
  • Uzodimma ya bayyana cewa gwamnonin za su kai ziyarar hadin gwiwa ga Shugaba Tinubu domin kara karfafa hadin kai da gwamnatin tarayya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza ƙwararren edita ne a fannin nishaɗi, al'amuran yau da kullum, da kuma siyasa, wanda ke da shekaru sama da takwas a aikin jarida.

Imo - Gwamnan jihar Imo kuma shugaban kungiyar gwamnonin Kudu maso Gabas, Hope Uzodimma, ya bayyana cewa gwamnonin yankin guda biyar sun cimma matsaya ta mara wa Shugaba Bola Ahmed Tinubu baya domin tazarce a zaben 2027.

Uzodimma ya ce matakin ya biyo bayan nazarin ayyukan gwamnatin Tinubu, musamman irin ci gaban da ta kawo wa yankin ta fuskar manyan ayyukan more rayuwa da tattalin arziki.

Kara karanta wannan

Abu ya girma: Za a shiga kasuwa, shago shago domin nema wa Tinubu ƙuri'u

Gwamnonin Kudu maso Gabas sun amince Tinubu ya yi tazarce a 2027
Gwamna Hope Uzodimma yana karanta takardar bayan taron kungiyar gwamnonin Kudu maso Gabas. Hoto: @Hope_Uzodimma1
Source: Twitter

Gwamnoni 5 sun goyi bayan Tinubu

Da yake jawabi yayin ganawa da Majalisar Dattawan Jihar Imo da kuma sarakunan gargajiya a Owerri, Uzodimma ya ce yankin ba zai sake bari maganganun siyasa su rinjayi gaskiyar ci gaban da ake gani ba, in ji rahoton Channels TV.

Ya ce:

"Mu gwamnonin Kudu maso Gabas biyar mun duba dukkan zabuka, sannan muka yanke shawarar yin aiki tare da Shugaba Bola Tinubu saboda muna son zama wani bangare na Project Nigeria."

Ya kara da cewa nan ba da jimawa ba gwamnonin yankin za su kai ziyarar hadin gwiwa ga Shugaba Tinubu domin kara karfafa alakar su da gwamnatin tarayya.

Uzodimma ya ce daya daga cikin manyan dalilan da suka sa suka yanke wannan matsaya shi ne kafa Hukumar Raya Kudu maso Gabas (SEDC), wadda ya ce yankin ya dade yana neman a kafa tun bayan yakin basasa.

A cewarsa, Shugaba Tinubu ya sanya hannu kan dokar kafa hukumar a ranar 24 ga Yulin 2024, sannan aka rantsar da kwamitin gudanarwarta a watan Fabrairun 2025 tare da fara ba ta kudaden gudanar da aiki.

Kara karanta wannan

Masoyan Tinubu sun mayar wa Kwankwaso martani kan tikitin Musulmi Musulmi

Ayyukan layin dogo da hanyoyi

Gwamnan ya kuma yabawa gwamnatin tarayya kan farfado da layin dogo tsakanin Port Harcourt da Aba, wanda ya ce ya fara aiki a kasuwanci.

Haka kuma ya ambaci amincewar gwamnatin tarayya da aikin sake gina hanyar dogo ta Gabas da darajarta ta kai dala biliyan uku, daga Port Harcourt zuwa Maiduguri, ta bi ta yankin Kudu maso Gabas.

A bangaren hanyoyi, Uzodimma ya ce gwamnatin Tinubu ta aiwatar da hanyoyin shiga gadar Second Niger Bridge da kuma wasu manyan tituna kamar:

  • Hanyar Otuocha–Anam–Abaji mai tsawon kilomita 108
  • Hanyar Oba–Nnewi–Uga–Ihube/Okigwe Junction mai tsawon kilomita 150
Gwamnonin Kudu maso Gabas sun ce Tinubu ya yi masu ayyuka
Shugaba Bola Ahmed Tinubu (hagu), Gwamna Hope Uzodimma (tsakiya) Gwamna Ahmad Aliyu (dama) a bikin kamun kifi a Kebbi. Hoto: @Hope_Uzodimma1
Source: Twitter

Kudu ta amfana da manufofin Tinubu

Uzodimma ya kara da cewa baya ga ayyukan da suka shafi yankin kai tsaye, Kudu maso Gabas ta kuma amfana da wasu manufofin gwamnatin Tinubu.

Manufofin sun hada da karin rabon kudade ga jihohi, shirin bashin karatu, inganta tsaro da sauye-sauyen tattalin arziki domin rage tsadar gudanar da kasuwanci.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com