NDC: An Samu Bayanin Abin da Aka Tattauna a Sabuwar Haduwar Kwankwaso da Dickson

NDC: An Samu Bayanin Abin da Aka Tattauna a Sabuwar Haduwar Kwankwaso da Dickson

  • Rabiu Musa Kwankwaso ya karbi bakuncin Sanata Henry Seriake Dickson a gidansa da ke unguwar Maitaima a birnin Abuja
  • An yi wannan haduwa ne kwanaki kalilan bayan an ga tsohon gwamnan na Kano a gidan Dickson wanda shi ne jagoran NDC na kasa
  • Sanatan ya fadi yadda suka yi da Kwankwaso da kuma yadda aka tabbatar masa cewa an daura sunan shi a shafin hukumar INEC

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

M. Malumfashi ya shafe shekaru 10 yana kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada

Abuja - Rabiu Musa Kwankwaso yana cigaba da kai ruwa rana domin ganin an yaye soke rajistar da wata kotun tarayya ta yi wa jam’iyyar NDC.

Sanata Rabiu Musa Kwankwaso mai yi wa NDC takarar mataimakin shugaban kasa a zabe mai zuwa ya sake yin zama da Henry Seriake Dickson.

Kwankwaso
Sanata Henry Seriake Dickson a gidan Rabiu Musa Kwankwaso tare da wasu manyan NDC a Abuja Hoto: @SaifullahiHon
Source: Twitter

Rabiu Kwankwaso ya zauna da Seriake Dickson

Bayanan da aka samu a shafin wani hadimin Rabiu Musa Kwankwaso a X ya nuna ya gana da Sanata Henry Seriake Dickson a gidansa a Abuja.

Kara karanta wannan

Soke rajista: Daga jin hukuncin kotu, na hannun daman jagoran NDC ya ruga APC

Sanarwar da aka fitar a yammacin Talata, 30 ga watan Yuni 2026 ta ce an yi wannan ganawa ne a gidan Madugun Kwankwasiyya da ke Maitama.

Alhaji Saifullahi Hassan ya wallafa hotunan ganawar mai gidansa da jagoran na NDC na kasa, ya yi hakan ne da kimanin karfe 6:00 na yamma.

Daga cikin wadanda aka yi zaman da su akwai na hannun daman tsohon gwamnan Kano kuma dattijo a siyasar Najeriya, Injiniya Buba Galadima.

Bayan nan, Saifullahi Hassan ya ce Sanata Muhammad Hassan yana wajen wannan zama da aka yi.

Kafin shigowarsa jam’iyyar NDC inda yake takarar gwamnan jihar Yobe a 2027, Sanata Muhammad Hassan ya taba wakiltar kudancin Yobe.

Sanata Henry Seriake Dickson a gidan Rabiu Musa Kwankwaso
Rabiu Musa Kwankwaso lokacin zamansa da Sanata Henry Seriake Dickson a Abuja Hoto: @SaifullahiHon
Source: Twitter

Wainar da aka toya tattaunawar Dickson da Kwankwaso

Daga cikin abubuwan da aka tattauna a kai wajen zaman akwai zancen daura sunan Rabiu Kwankwaso a shafin INEC a matsayin ‘dan takara.

Tsohon gwamnan na Kano zai yi wa Peter Obi abokin gami a zaben shugaban kasa na 2027 a NDC.

Idan za a tuna, matsala ta bijiro wa jam’iyyar hamayyar sakamakon soke rajistarta da alkalin wani kotun tarayya a Lokoja ya yi a karshen makon jiya.

Kara karanta wannan

Bayanai sun fito da ake rade radin matsalar NDC ta jawo Kwankwaso zai koma PRP

Shi ma Sanata Henry Seriake Dickson ya tabbatar da wannan lamari domin jim kadan bayan nan ya wallafa makamantan hotuna a dandalin X.

Seriake Dickson ya ce ya zoyarci Mai girma Rabiu Musa Kwankwaso, CON kuma an yi masa bayanin halin da NDC take ciki a Arewa maso yamma.

Tsohon gwamnan ya ce Madugun na Kwankwasiyya ya shaida masa nasarorin da aka samu daga zagayen da ya rika yi a yankin na shi.

A nan kuma aka tabbatar wa tsohon ministan tsaron cewa an yi nasarar wallafa sunansa a shain hukumar INEC a shirin tunkarar 2027.

Abin da sanarwarsa ta kunsa a karshe shi ne tabbatar wa magoya bayan NDC cewa jam’iyyar ta tsaya tsayin-daka wajen samun nasara.

Tsohon hadimin Dickson ya bar NDC

Tun ba a je ko ina ba sai ga rahoto cewa wani mutumin Seriake Dickson ya rabu da NDC zuwa APC da aka soke masu rajista a dalilin wani hukuncin kotu.

Hukuncin kotu ke da wuya, sai aka ji na hannun daman Seriake Dickson ya shiga APC daga jam’iyyar NDC kuma ya samu tarba mai kyau a Bayelsa.

Hon. Fyneman Wilson ya yi sallama da wanda ake gani na kusa da shi ne sosai a siyasa a jihar Bayelsa tun ba yau ba, kuma sun fito daga mahaifa daya.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng