Zaben 2027: Kotu Ta Raba Gardama, Ta Faɗi Sahihin Ɗan Takarar Gwamnan ADC a Jihar Ogun

Zaben 2027: Kotu Ta Raba Gardama, Ta Faɗi Sahihin Ɗan Takarar Gwamnan ADC a Jihar Ogun

  • Babbar Kotun Tarayya ta Abeokuta ta tabbatar da Jimi Lawal a matsayin halastaccen ɗan takarar gwamnan ADC, tare da umartar INEC ta amince da takararsa
  • Hukuncin kotun ya kawo karshen rikicin tikitin gwamna tsakanin bangarorin ADC, bayan kotu ta tabbatar zaben fidda gwani da ya fitar da Lawal ingantacce
  • Shugaban ADC na Ogun da Jimi Lawal sun yi maraba da hukuncin, suna kira ga hadin kai, sulhu da shirye-shiryen tunkarar zaben gwamna mai zuwa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza ƙwararren edita ne a fannin nishaɗi, al'amuran yau da kullum, da kuma siyasa, wanda ke da shekaru sama da takwas a aikin jarida.

Ogun - Babbar Kotun Tarayya da ke zamanta a Abeokuta, jihar Ogun, ta ayyana Jimi Lawal a matsayin halastaccen ɗan takarar gwamnan jam'iyyar ADC a zaben gwamnan jihar da ke tafe.

Mai shari'a Abiodun Adeyemi ne ya yanke hukuncin, wanda ya kawo karshen rikicin shugabanci da takarar gwamna da ya raba jam'iyyar gida biyu, inda kowane bangare ke ikirarin mallakar tikitin takarar gwamna.

Kara karanta wannan

Makinde: Gwamna ya mika mulki ga mataimakinsa bayan hukuncin majalisar dokoki

Kotu ta tabbatar da nasar Jimi Lawal a zaben fitar da gwani na ADC a jihar Ogun.
Jimi Lawal tare a amininsa Malam Nasir El-Rufai. Hoto: @SKefason
Source: Twitter

Jimi Lawal, wanda ake cewa na hannun daman tsohon gwamnan jihar Kaduna, Mallam Nasir El-Rufai, ya shafe watanni yana takun saka da Biodun Ogundipe kan tikitin takarar gwamnan ADC bayan zaben fidda gwani na jam'iyyar, in ji rahoton The Punch.

Kotu ta tabbatar da ingancin zaben ADC

Saboda rashin gamsuwa da yadda aka gudanar da zaben fidda gwani, Lawal ya shigar da kara mai lamba FHC/AB/CS/97/2026, yana neman kotu ta tabbatar da shi a matsayin wanda ya lashe zaben fidda gwani bisa ka'ida.

A hukuncinsa, Mai shari'a Adeyemi ya bayyana cewa an gudanar da zaben fidda gwanin da ya fitar da Lawal ne bisa doka, kuma Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta (INEC) ta sanya ido kan yadda aka gudanar da shi.

Kotun ta ce zaben ya cika dukkan sharuddan doka, kuma shi ne kadai halastaccen zaben fidda gwamnan ADC da aka gudanar a jihar Ogun.

Saboda haka, kotun ta ayyana Jimi Lawal a matsayin halastaccen ɗan takarar gwamnan ADC tare da umartar INEC ta amince da shi ta hanyar sanya sunansa cikin bayanan hukuma a matsayin ɗan takarar jam'iyyar.

Kara karanta wannan

'Dan Afrika zai fafata da turawa 5 a zaben shugaban Majalisar Dinkin Duniya

Shugaban ADC ya yi kira ga hadin kai

Da yake martani bayan hukuncin, shugaban ADC na jihar Ogun, Otunba Femi Soluade, ya bayyana hukuncin a matsayin nasara ga dimokuradiyya da kuma wata dama ta hada kan jam'iyyar kafin babban zabe.

Ya ce jam'iyyar ba za ta rungumi rarrabuwar kai ba, sai dai sulhu da hadin kai.

"Babu mai nasara, babu mai shan kaye. Wadanda ke wani bangaren ma 'yan'uwanmu ne, kuma dole mu kasance masu hakuri da karamci bayan wannan hukunci," in ji Soluade.
Kotu ta raba gardama kan sahihin dan takarar gwamnan ADC a Ogun.
Wani matashi rike da tutar jam'iyyar ADC a gangamin jam'iyyar da aka gudanar. Hoto: @ADCNig
Source: Twitter

"Gaskiya ta yi halinta" - Jimi Lawal

Shi ma da yake magana da manema labarai bayan fitowar hukuncin, Jimi Lawal ya bayyana cewa hukuncin ya zo masa a matsayin taimakon Allah bayan watanni na damuwa kan rikicin tikitin takarar.

Lawal ya ce tun watan Mayu yake cikin rashin kwanciyar hankali saboda ya yi imanin cewa an tauye masa hakkinsa duk da cewa shi ne ya samu gagarumar nasara a zaben fidda gwani.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com