2027: Peter Obi Ya Bayyana Tanadin da Ya Yi wa 'Yan Najeriya na Ayyukan Alheri
- 'Dan takarar shugaban kasa a jam'iyyar NDC, Peter Obi ya bayyana sabon hangen nesansa na yadda zai gina Najeriya mai ɗorewa idan aka zabe shi
- Mista Peter Obi ya ce gwamnatinsa za ta mayar da hankali kan ilimi, tare da zayyano sauran bangarorin da zai fi matar da hankali domin farfado da kasar nan
- 'Dan takarar ya yi alƙawarin kafa kwamitin musamman domin rage yawan yaran da ba sa zuwa makaranta da kuma ƙarfafa tsarin TVET
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
FCT Abuja – Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar NDC, Peter Obi, ya bayyana tanadinsa na gina Najeriya mai albarka da ci gaba, yana mai cewa burinsa shi ne haɗa kan ƙasa tare da inganta rayuwar jama'a.
A cikin saƙon da ya fitar ranar Laraba, 1 ga watan Yulin 2026, Obi ya tuna cewa tun lokacin da ya fara neman shugabancin ƙasa ya yi alƙawarin ɗora Najeriya kan turbar haɗin kai da sauyi mai ɗorewa.

Source: Twitter
A sakon da ya wallafa a shafinsa na X, Peter Obi ya ce a matsayinsa na ɗan takarar shugaban ƙasa na NDC, zai ci gaba da bayyana wa 'yan Najeriya cikakken tsarinsa a makonni da watanni masu zuwa.
Tanadin Peter Obi ga yan Najeriya
A cikin sakon, Mista Obi ya ce wannan tsari zai mayar da hankali kan rage cin zarafin iko a gwamnati, dakatar da tabarbarewar rayuwar al'umma, da kuma samar da zaman lafiya, haɗin kai, ci gaba da wadata.
Ya ce manufarsa ta ta'allaka ne kan haɗa kan al'umma, tabbatar da adalci, daidaito da bai wa kowane ɗan ƙasa damar cimma burinsa ta hanyar da doka ta tanada.
Peter Obi ya bayyana cewa manyan ginshiƙan shirin nasa sun haɗa da yin garambawul a bangaren ilimi da kiwon lafiya, yana mai cewa su ne tushen bunƙasa jarin ɗan Adam.

Source: Twitter
A cewarsa, samun ingantaccen jari na ɗan Adam shi ne tubalin ci gaban ƙasa, domin shi ne ke tallafa wa tattalin arziki, rayuwar yau da kullum da kuma ingantattun ayyukan gwamnati.
Ya ce idan aka ba shi damar jagoranci, gwamnatinsa za ta kafa kwamitin musamman tun daga farkon mulki domin rage matsalar yaran da ba sa zuwa makaranta.
Ina da shirin samar da aikin yi - Obi
Obi ya kuma ce za a ƙara mayar da hankali kan Ilimin Fasaha da Koyon Sana'o'i (TVET) domin samar da ƙwararrun ma'aikata da za su tallafa wa manufofin bunƙasa masana'antu da ƙara darajar kayayyakin noma a faɗin ƙasar nan.
Ya bayyana cewa za a inganta cibiyoyin TVET ta hanyar samar da kuɗi da kayan aiki tare da haɗin gwiwar gwamnati, kamfanoni masu zaman kansu da ƙungiyoyin da ke ba da gudummawa ga ilimi.
A cewarsa:
"Matsalar shi ne rashin aikin yi ya karu, yayin da 'yan kasuwar Najeriya ke gina sana'o'insu a wasu wuraren daban saboda rashin kwararrun da ake da bukata a nan."
Obi ya ce dole ne Najeriya ta magance matsalar rashin aikin yi da ƙarancin ƙwararrun ma'aikata, wanda ya sa wasu 'yan kasuwa ke kafa masana'antunsu a ƙasashen waje.
Ya ƙara da cewa gwamnatinsa za ta kuma ba da muhimmanci ga koyar da ɗabi'a da tarbiyyar ƙasa domin gina amana, shugabanci nagari da ƙarfafa ƙimomin da za su haɗa 'yan Najeriya wuri guda.
NDC ta daukaka kara
A baya, mun wallafa cewa jam'iyyar NDC ta dauki matakin ɗaukaka ƙara domin kalubalantar hukuncin kotun Lokoja da ya soke rajistarta lamarin da ya zama babbar barazana ga siyasar 2027.
Kafin NDC ta daukaka kara, jagororin jam'iyyar da suka hada da Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso sun kwantar da hankulan 'yan Najeriya, inda suka bayyana cewa za a fafata da su a zabe mai zuwa.
Jagoran jam'iyyar na kasa Seriake Dickson ya bayyana cewa a yanzu haka, hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) ta ba su damar tura sunayen wadanda za su yi wa NDC takara a kakar 2027.
Asali: Legit.ng


