Zabe na Karatowa, Tinubu zai Ciwo Bashin Dala Biliyan 1.25 a Bankin Duniya

Zabe na Karatowa, Tinubu zai Ciwo Bashin Dala Biliyan 1.25 a Bankin Duniya

  • Bankin duniya ya amince zai ba Najeriya sabon bashi na dala biliyan 1.25 ƙarƙashin shirin bunƙasa zuba jari da sauransu
  • Amincewar bankin ta zo ne duk da damuwar jama'a kan ƙara yawan bashin da ƙasar ke ci a kasashen duniya a halin yanzu
  • A sanarwar da ya fitar, bankin ya ce bashin zai tallafa wajen inganta tattalin arzikin Najeriya, samar da ayyuka da sauransu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Bankin duniya ya amince da bai wa Najeriya sabon rancen dala biliyan 1.25 a ƙarƙashin shirinsa na samarwa da inganta sana'o'i a Najeriya.

Hakan na zuwa ne duk da korafin jama'a kan ƙara yawan bashin da ƙasar ke ci a ƙasashen waje da kuma kiraye-kirayen da ake yi ga gwamnatin tarayya da ta rage karɓar irin waɗannan rance.

Kara karanta wannan

IPMAN ta yi wa gwamnati barazana saboda an nemi ta rage farashin fetur

Shugaba Bola Ahmed Tinubu
Shugaban kasar Najeriya a wajen taro. Hoto: Bayo Onanuga
Source: Facebook

Bola Tinubu ya samu sabon bashi

Punch ta wallafa cewa bankin ya sanar da amincewar ne cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Laraba, tare da ƙaddamar da sabon tsarin haɗin gwiwa da Najeriya na shekarun 2026 zuwa 2032.

Bankin ya ce sabon tsarin zai jagoranci yadda zai tallafa wa Najeriya cikin shekaru shida masu zuwa, inda zai mayar da hankali kan samar da ƙarin ayyukan yi ta hanyar bunƙasa ci gaban da kamfanoni masu zaman kansu ke jagoranta.

Ana korafi kan cin bashi

Mutane da dama sun bayyana cewa duk da yawaitar bashin da ƙasar ke karɓa daga ƙasashen waje, har yanzu hakan bai haifar da inganta rayuwar al'umma ba.

Sai dai bankin duniya ya ce sabon tsarin haɗin gwiwar ya ginu ne kan sauye-sauyen tattalin arziki da Najeriya ta yi a baya-bayan nan, waɗanda ya ce sun haifar da bunƙasar tattalin arziki, ƙaruwa a kuɗin shiga da sauransu.

Kara karanta wannan

Yadda ake farautar 'yan Najeriya da sauran kasashe da sanduna a Afrika ta Kudu

Taiwo Oyedele da Bola Tinubu
Shugaba Bola Tinubu da Ministan kudin Najeriya, Taiwo Oyedele. Hoto: Bayo Onanuga
Source: Twitter

Me za a yi da bashin kudin?

Bankin ya ce shirin na da burin samar da wutar lantarki ga mutum miliyan 32, samar da intanet mai sauri ga mutum miliyan 58, inganta ayyukan lafiya da abinci mai gina jiki ga mutum miliyan 40, tare da tallafa wa manoma miliyan 9.5.

Haka kuma, shirin na neman ƙarfafa ɗan Adam, haɓaka yawan amfanin gona da kuma faɗaɗa damar samun makamashi da kayayyakin fasahar sadarwa.

Daraktan bankin duniya na Najeriya, Mathew Verghis, ya ce za su mayar da hankali wajen taimaka wa Najeriya ta juya nasarorin da ta samu a fannin tattalin arziki zuwa ingantacciyar rayuwa ga al'umma.

Ya ce:

“Sabon tsarin haɗin gwiwarmu ya bayyana yadda bankin duniya zai tallafa wa Najeriya a shekaru masu zuwa, musamman wajen samar da ƙarin ayyukan yi masu inganci ta hanyar bai wa kamfanoni masu zaman kansu damar bunƙasa.

Batun rage kudin mai a Najeriya

A wani labarin, kun ji cewa gwamnatin Najeriya karkashin shugaba Bola Ahmed Tinubu ta yi kira ga 'yan kasuwa da su rage kudin litar mai.

Kara karanta wannan

Tsaro: Najeriya na neman agajin kasashe bayan Trump ya ce ya gama kare ran Kiristoci

Hakan na zuwa ne bayan faduwar farashin danyen mai a kasuwar duniya biyo bayan sulhun da Iran ta yi da Amurka a Gabas ta Tsakiya.

Najeriya ta ce ba za ta dauki alhakin daidaida farashin man fetur ba bayan cire tallafi, amma za ta tabbatar da cewa 'yan kasuwa sun yi adalci.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng