IPMAN Ta Yi wa Gwamnati da Barazana saboda an Nemi Ta Rage Farashin Fetur

IPMAN Ta Yi wa Gwamnati da Barazana saboda an Nemi Ta Rage Farashin Fetur

  • Kungiyar masu kasuwancin man fetur ta IPMAN ta yi fatali da umarnin gwamnati, inda ta ce za ta ɗauki mataki idan aka tilasta mata kayyade farashin fetur
  • Ƙungiyar ta bayyana cewa babu dalilin da zai sa gwamnati ta tsoma baki a cikin harkar kayyade farashin mai domin kasuwar a bude ta ke
  • Tutsun IPMAN na zuwa ne bayan Ministan Albarkatun Man Fetur ya ce gwamnati ba za ta amince da cin zarafin masu amfani da fetur ta hanyar tsadar farashi ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT Abuja – Ƙungiyar 'yan kasuwar man fetur ta IPMAN ta yi gargaɗin cewa za ta rufe dukkannin gidajen man da 'ya'yanta ke da su a faɗin ƙasar nan idan gwamnatin tarayya ta yi ƙoƙarin tilasta kayyade farashin fetur.

Kara karanta wannan

Talaka zai samu sauki, gwamnatin Tinubu ta ce a rage kudin man fetur

Sakataren yaɗa labarai na ƙungiyar, Chinedu Ukadike, ne ya bayyana hakan yayin wata hira, inda ya ce ba zai yiwu a ce an buɗe kasuwa ga gasa, sannan kuma gwamnati ta riƙa saka farashin da za a sayar da fetur ba.

IPMAN za ta yi wa gwamnati bore
Ana saka man fetur a mota a gidan mai (hagu), shugaba Bola Tinubu a dama. Hoto: Bayo Onanuga|Getty Images
Source: Facebook

Jaridar Punch ta wallafa cewa wannan na zuwa ne bayan Ministan Ƙaramin Harkokin Albarkatun Man Fetur, Sanata Heineken Lokpobiri, ya ce gwamnati ba za ta lamunci gallaza wa talakawa a kan farashin man fetur ba.

IPMAN ta yi adawa da shawarar gwamnati

Politics Nigeria ta kawo labarin cewa Ukadike ya musanta zargin cewa masu kasuwancin mai na cin riba fiye da kima, yana mai cewa da dama daga cikinsu na tafka asara sakamakon sauye-sauyen farashin da matatar Dangote ke yi.

Ya ce:

"Masu kasuwancin mai za su rufe gidajen mai idan gwamnati ta yi ƙoƙarin tilasta kayyade farashi. Ba za ka iya tsara farashi a kasuwar da aka buɗe ga gasa ba."

A cewarsa, sau da dama 'yan kasuwa kan sayi fetur da tsada, amma kafin su kai shi gidajen mai sai farashi ya sauka, lamarin da ke jefa su cikin asara.

Ya ƙara da cewa:

"Idan ba ka rage farashi ba, ba za ka samu masu siya ba. Wannan shi ne amfanin tsarin kasuwar gasa. Idan ba za ka iya gogayya ba, ba za ka ci gaba da zama a kasuwa ba."

Kara karanta wannan

Kungiyar Obidient ta bada tabbaci kan takarar Obi da Kwankwaso a 2027 duk da hukuncin kotu

Yadda yan kasuwar fetur ke sana'arsu - IPMAN

Ukadike ya ce yawancin masu gidajen mai suna gudanar da kasuwancinsu ne da rancen banki, don haka sauyin farashi ba ya rage nauyin biyan bashin da ke kansu.

Ya buƙaci gwamnatin tarayya ta mayar da hankali wajen tabbatar da matatun mai na cikin gida sun fara aiki yadda ya kamata tare da ƙarfafa shigo da man fetur domin samar da cikakkiyar gasa.

Masu sayar da man fetur sun zargi gwamnati da kokarin yi masu tilas
Wasu ma'aikata a kamfanin mai na NNPCL Hoto: NNPC Limited
Source: Facebook

A nasa ɓangaren, shugaban yan kasuwar mai na PETROAN, Billy Gillis-Harry, ya ce ministan man fetur yana da ikon shiga tsakani domin kare masu amfani da fetur.

Sai dai ya jaddada cewa ya kamata a fara tattara dukkannin masu ruwa da tsaki a masana'antar domin tattauna matsalar kafin a ɗauki kowane mataki.

Matatar Dangote ta rage farashin fetur

A baya, kun samu labarin cewa matatar Dangote ta rage farashin litar fetur da take sayar wa 'yan kasuwa da N50, inda ta sauke farashin daga N1,175 zuwa N1,125 sakamakon faduwar farashin mai a duniya.

Kara karanta wannan

Abin da sabuwar dokar kafa 'yan sandan jihohi a Najeriya ta kunsa

An samu saukar farashin mai a kasuwar duniya ne sakamakon lafawar rikicin Gabas ta Tsakiya, inda Amurka da Iran suka cimma matsaya na tsagaita wuta yayin da ake ci gaba da tattauna yadda za a kawo karshen yakin.

Ana sa ran 'yan kasuwar mai na cikin Najeriya za su sauke farashin litar fetur din a gidajen mansu domin saukaka wa al'umma bayan sun samu saukin yadda suke sayo man daga kasuwar duniya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng