NDC Ta Ɗauki Mataki bayan Hukuncin Kotu, Ta Fara Tura Sunayen 'Yan Takara ga INEC
- Jam'iyyar NDC ta ɗaukaka ƙara kan hukuncin kotun Lokoja da ya soke rajistarta lamarin da ya zama babbar barazana ga siyasar 2027
- Kafin NDC ta daukaka kara, jagororin jam'iyyar da suka hada da Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso sun kwantar da hankulan 'yan Najeriya
- Sun bayar da tabbacin cewa babu abin da zai hana 'yan takararta shiga a fafata da su a babban zabe mai zuwa duk da wannan kalubale
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
FCT Abuja – Jagoran NDC na kasa, Seriake Dickson, ya bayyana cewa jam'iyyar ta ɗaukaka ƙara kan hukuncin Babbar Kotun Tarayya da ke Lokoja a jihar Kogi, wanda ya soke rajistar jam'iyyar.
Jagoran jam'iyyar ya bayyana haka ne kwanaki kadan bayan hukuncin da ya yamutsa hazo, inda ya bayyana cewa NDC na ci gaba da shirye-shiryen siyasar 2027.

Source: Twitter
Dickson ya bayyana hakan ne a wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na X a ranar Litinin, inda ya ce bayan shigar da ƙarar, Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC) ta bai wa jam'iyyar damar amfani da shafinta na yanar gizo domin loda sunayen 'yan takararta.
A kwanakin baya, Babbar Kotun Tarayya da ke Lokoja ta soke hukuncin da ta yanke a ranar 10 ga Disamba, 2025, wanda ya umarci INEC ta yi wa NDC rajista a matsayin jam'iyyar siyasa.
Kar ku ji 'dar - Jagoran NDC
Jaridar The Cable ta kawo labarin cewa Seriake Dickson ya ce jam'iyyar ta riga ta ɗaukaka ƙara tare da neman dakatar da aiwatar da hukuncin, kuma an miƙa takardun ga shugaban INEC domin hukumar ta yi abin da doka ta tanada.
Ya ce:
"Yanzu abin da ya rage shi ne kammala tsarin gudanarwa na miƙa sunayen 'yan takara ga INEC, kuma an ba mu damar shiga shafin hukumar domin loda sunayen waɗanda suka cancanta."

Kara karanta wannan
Kungiyar Obidient ta bada tabbaci kan takarar Obi da Kwankwaso a 2027 duk da hukuncin kotu
Ya ƙara da cewa an riga an AIKA sunansa da na ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar, Peter Obi, yayin da za a loda sunan ɗan takarar mataimakin shugaban ƙasa bayan kammala wasu takardu.
NDC na ci gaba da shirin 2027
Seriake Dickson ya bayyana cewa NDC tana bin jadawalin INEC yadda ya kamata, yana mai cewa har zuwa ranar 11 ga Yuli 2026 ne ake da wa'adin miƙa sunayen 'yan takarar Majalisar Tarayya, yayin da wa'adin na gwamnoni da 'yan majalisun jihohi zai ƙare ranar 17 ga Yuli, 2026.s

Source: Facebook
Ya ce:
"Saboda haka akwai isasshen lokaci na miƙa sunayen dukkannin 'yan takara ga INEC, kuma babu wani dalilin da zai sa mutane su firgita."
Jagoran jam'iyyar ya amince cewa an samu wasu matsaloli a zaɓen fitar da gwani na NDC, amma ya ce an fara sasanta masu ruwa da tsaki da waɗanda ba su gamsu da sakamakon ba.
An shawarci su Kwankwaso kan barin NDC
A baya, mun kawo labarin cewa jagoran NDC na kasa, Sanata Seriake Dickson ya fara roƙon yan takarar jam'iyyar kada su sauya sheka bayan hukuncin kotu da ya nemi a janye batun yi wa jam'iyyarsu rajista.

Kara karanta wannan
Sojoji sun ceto daliban da aka sace a Borno bayan ritsa 'yan ta'addan ISWAP cikin daji
Hakan na zuwa ne bayan an fara rade-radin cewa 'yan takarar NDC na duba yiwuwar canza jam'iyya gabanin babban zaben 2027 domin sama wa kansu mafita daga kalubalen da jam'iyyar ke fuskanta a yanzu.
Sanata Seriake Dickson ya tabbatar masu da cewa hukuncin da babbar Kotun Tarayya ta yanke ba zai hana su shiga zabe mai zuwa ba, saboda haka babu dalilin da ya zai sa su bar NDC saboda batun shari'ar.
Asali: Legit.ng
