Soke Rajista: Daga Yin Hukuncin Kotu, Na Hannun Daman Jagoran NDC Ya Ruga APC
- Hon. Fyneman Wilson ya yi sallama da wanda ake gani na kusa da shi ne sosai a siyasa a jihar Bayelsa, Henry Seriake Dickson
- ‘Dan siyasar mai shekaru kusan 80 ya kira NDC da mallakin mutum guda, kuma yana ganin jam’iyyar ba za ta kai labari ba
- Wilson ya dauke wa jagoran NDC na kasa mutane a mahaifarsa a sa’ilin da jam’iyyar adawar ke kokawa da hukuncin kotu
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
M. Malumfashi ya shafe shekaru 10 yana kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada
Bayelsa - Hon. Fyneman Wilson wanda yake da kusanci sosai da Seriake Dickson ya yi sallama da jam’iyyar hamayya ta NDC.
Ana ganin sauya-shekar Fyneman Wilson za ta taba Seriake Dickson ganin cewa ya tsallaka ne zuwa APC ana cikin mawuyacin hali.

Source: Facebook
Tsohon hadimin Seriake Dickson ya bar NDC
A safiyar Talata, jaridar Daily Trust ta rahoto cewa Hon. Fyneman Wilson ya rabu da jam’iyyar NDC yana mai cewa ba za ta kai ko ina ba.

Kara karanta wannan
NDC: Yaron Atiku ya nemi ADC, PDP da sauran jam’iyyu su taya Obi da Kwankwaso fada
‘Dan siyasar wanda da shi aka kafa jam’iyyar NDC ya taba zama Mai ba Sanata Dickson shawara kan harkokin siyasa da yake gwamna.
Kafin zamansa sanatan Bayelsa ta yamma, Seriake Dickson ya yi gwamna na tsawon shekaru takwas tun daga shekarar 2012 zuwa farkon 2020.
Tsohon hadimin na jagoran NDC a Najeriya ya ja mutanensa a jihar Bayelsa suka fice daga jam’iyyar hamayyar kuma suka shiga APC.
Jiya aka karbi Wilson a wani dakin taro na gidan gwamnatin jihar Bayelsa da ke garin Onopa.
Hon. Wilson ya kamanta NDC da ya baro da wani kamfani mallakin mutum guda, watakila yana nuni ne ga salon tsohon mai gidansa.
Sauya-shekar da ya yi ta ci mutane har a garin Sagbama inda daga nan Dickson ya fito, kuma har ya wakilce su a Majalisar tarayya a 2007.

Source: Facebook
Shugabannin APC sun karbi 'yan jam'iyyar NDC
The Nation ta ce wadanda suka halaci bikin sauya shekar sun hada da sabon Mataimakin gwamnan jihar Bayelsa, Fasto Peter Akpe.
An kuma ga fuskokin Rt. Hon. Peremobowei Ebebi da sakataren APC a Bayelsa, Odoji Japan.
Wannan yana zuwa ne kwanaki kadan bayan NDC ta rasa wasu ‘ya ‘yanta a mazabar Toru-Orua a karamar hukumar Bayelsa zuwa APC.
Dickson yana yi wa Wilson kallon uba
A shekarar bara ta 2025 da dattijon ya cika shekaru 79 a duniya, ‘dan majalisar ya yi amfani da shafinsa na Facebook wajen taya shi murna.
A lokacin sanatan ya ce Hon. Wilson tamkar uba yake a wurinsa saboda muhimmancinsa da tasirinsa wajen mutanensa a Sagbama.
Siyasa ta raba gidan Olusegun Obasanjo
An ji yadda kan 'ya 'yan tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo ya rabu saboda takarar da Solomon Adeoola yake yi a jihar Ogun.
Wasu 'ya 'yan Obasanjo ciki har da Gbenga Obasanjo suna tare da APC a zaben gwamna, amma yayarsu Iyabo Obasanjo tana jam'iyyar PDP.
Samun sabanin ra’ayin siyasa ba bakon abu ba ne a gidan Cif Olusegun Obasanjo idan za a tuna labarin Sanata Iyabo Obasanjo Bello.
Asali: Legit.ng
