Bayan Sun Ji Ruwan Wuta, Kwamandoji da Manyan ISWAP sama da 70 Sun Mika Wuya
- Aikin yaki da ayyukan ta'addanci a Arewacin Najeriya na kara samun tagomashi bayan dakarun sojin Najeriya sun kara azama wajen kai hare-hare
- Rahotanni sun ce wasu daga cikin 'yan kungiyar ISWAP sun gudu daga sansanoninsu bayan hare-haren soji da na sama da suka ci gaba da raunana ƙungiya
- Bayan sun ji ruwan wuta, kwamandoji da manyan yan ta'addan da suka haura 70 sun zubar da makamansu tare da ika wuyaga dakarun Najeriya a jihar Borno
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Borno – Wasu manyan kwamandojin ƙungiyar ta'addanci ta ISWAP sun miƙa wuya ga dakarun sojin Najeriya a jihar Borno.
Rahotannin sun bayyana cewa kwamandojin sun bar sansanoninsu ne bayan makonni ana ci gaba da kai musu hare-haren soji ta ƙasa da sama, tare da amfani da bayanan sirri wajen kai farmaki, lamarin da ya raunana ƙarfin ƙungiyar.

Source: Twitter
Jaridar Zagazola Makama ta wallafa cewa bayanan sirri sun ce halin yanzu ana tsare da kwamandojin a wani wurin tsaro, inda ake tantance su.
Ana binciken kwamandojin ISWAP
Jaridar The Cable ta kawo labarin cewa ana ci gaba da yi wa jagororin ISWAP da suka mika wuya tambayoyi domin samun bayanan sirri, kamar yadda ƙa'idojin aikin soja suka tanada.
An ce hukumomin tsaro ba su bayyana sunayen waɗanda suka miƙa wuya ba saboda dalilan tsaro, amma ana kallon matakin a matsayin babban koma baya ga shugabancin ISWAP, wanda ke nuna yadda matsin lambar da sojoji ke musu ke ƙaruwa.
Majiyoyin soja sun danganta lamarin da ƙaruwar hare-haren Operation HADIN KAI, wanda ya mayar da hankali kan lalata sansanonin 'yan ta'adda, cibiyoyin ajiyar kayayyaki, hanyoyin kai kayan tallafi da cibiyoyin jagoranci a Borno da sauran jihohin Arewa maso Gabas.
Sojoji na girgiza yan ta'addan ISWAP
Rahoton ya ƙara da cewa hare-haren sun takaita zirga-zirgar 'yan ta'addan, sun tarwatsa hanyoyin samar mAsu da kayan aiki, tare da rage mAsu ƙarfin shirya manyan hare-hare.
Haka kuma, rahoton ya ce wannan ya sa wasu gungun 'yan ta'adda sun miƙa wuya a wurare daban-daban na yankin Arewa maso Gabas cikin kwanakin baya.

Source: Original
Bayanan soja sun nuna cewa akalla mayaƙa 76, tare da wasu daga cikin iyalansu, sun miƙa wuya ga dakarun Operation HADIN KAI cikin makon da ya gabata.
Rahoton ya kuma ce bayanan sirri sun nuna cewa ana samun ƙarin saɓani tsakanin shugabannin ISWAP kan yadda ake gudanar da ayyuka, ƙarancin albarkatu da kuma ikon jagoranci, lamarin da ya rage ƙwarin gwiwar mayaƙan ƙungiyar.
An ceto dalibai daga hannun ISWAP
A baya, kun samu labarin cewa 'yan ta'addan kungiyar ISWAP sun sace wasu dalibai da malamai a wata makarantar sakandare da ke jihar Borno a lokacin da su ke kokarin rubuta jarrabawar kammala sakandare.
Dakarun sojoji sun bi sahun 'yan ta'addan bayan samun labarin barnar da suka yi a karamar hukumar Askira/Uba kuma sun samu nasarar ceto wasu daga cikin dalibai da malaman da 'yan ta'addan suka sace bayan an yi musayar wuta.
Majiyoyi sun bayyana cewa 'yan ta'addan sun afkawa makarantar sakandaren kimiyya da fasaha da ke Lassa da misalin ƙarfe 9:00 na safe a ranar Litinin, 29 ga watan Yunin 2026 yayin da suke zana jarrabawar NECO.
Asali: Legit.ng

