Batun Takarar Farfesa Pantami a Jam'iyyar PDP Ya Kai gaban Kotu

Batun Takarar Farfesa Pantami a Jam'iyyar PDP Ya Kai gaban Kotu

  • Tsohon Ministan sadarwa, Farfesa Isa Ali Ibrahim Pantami ya zama dan takarar gwamna na jam'iyyar PDP mai adawa a jihar Gombe
  • Daya daga cikin masu neman takarar gwamnan a inuwar Gombe, ya garzaya zuwa gaban kotu domin kalubalantar tikitin takarar da Pantami ya samu
  • Kotu ta fara sauraron karar da ke kalubalantar takarar da jam'iyyar PDP ta ba Farfesa Pantami, inda ta sanya lokacin da za ta ci gaba da sauraronta

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Jihar Gombe - Babbar kotun tarayya mai lamba 1 da ke zama a Gombe ta fara sauraron ƙaran da aka shigar kan takarar Farfesa Isa Ali Ibrahim Pantami a jam'iyyar PDP.

An shigar da karar ta hannun Abdulkadir Hamma Saleh, wanda ke ƙalubalantar zaman Farfesa Isa Ali Ibrahim Pantami a matsayin ɗan takarar gwamna na jam'iyyar PDP a jihar Gombe.

Kara karanta wannan

Ardo Risku: Mutane 10 da ake zargi da kisan shugaban Miyetti Allah sun shiga hannu

An fara sauraron kara kan takarar Pantami
Farfesa Isa Ali Ibrahim Pantami zaune a cikin ofis Hoto: Prof Isa Ali Pantami
Source: Twitter

Jaridar Daily Trust ta kawo rahoto ranar Lahadi, 28 ga watan Yunin 2026 cewa shari'ar ta zo gaban mai shari'a, Amina Aliyu Mohammed.

Alkalin kotun ta ɗage zaman kotun har zuwa ranar 9 ga Yuli, 2026, domin ci gaba da sauraron karar.

Meyasa aka kai Pantami kotu?

Abdulkadir Hamma Saleh yana neman taimakon kotun ne game da tsarin da ya samar da Pantami a matsayin mai rike da tutar PDP domin zaben gwamnan Gombe a zaben 2027.

Yana dai zargin an tafka kuskure da kura-kurai yayin gudanar da aikin zaɓen fitar da gwani na takarar gwamnan jam'iyyar PDP.

Kafin ya tunkari kotun, mai neman takarar da ke ya ɗaukaka ƙorafi ga shugabancin PDP domin su dubi kukansa tare da sake yin nazari kan yadda aka gudanar da zaɓen fitar da gwanin, inda ya nace kan cewa ya kamata jam'iyyar ta bi hanyoyin cikin gida na warware takaddama domin tabbatar da adalci, haɗin kai, da kuma bin ƙa'ida.

Kara karanta wannan

2027: Gwamna Fintiri ya mika fom din INEC ga 'yan takarar majalisar Adamawa

Mai neman takara na adawa da ba Pantami tikiti

To sai dai kuma, bayan abin da ya bayyana da rashin nasarar ƙoƙarin samun mafita a cikin jam'iyyar, Abdulkadir Hamma Saleh ya ƙaddamar da matakin shari'a domin ƙalubalantar sakamakon aikin zaɓen.

An kai karar PDP kotu kan Farfesa Pantami
Tsohon Ministan sadarwa, Farfesa Isa Ali Ibrahim Pantami Hoto: Prof Ali Isa Pantami
Source: Facebook

Ana tsammanin ƙarar za ta jawo hankalin 'yan siyasa sosai yayin da PDP ke tsananta shirye-shiryen zaɓen gwamna na shekarar 2027 a jihar Gombe.

Mai shari'a Amina Aliyu Mohammed ta ɗage batun zuwa ranar 9 ga watan Yuli, 2026, domin ci gaba da shari'ar.

Tsagin PDP ya tsayar da dan takarar gwamna

A wani labarin kuma, kun ji cewa tsagin jam'iyyar PDP da ke karkashin jagorancin Kabiru Tanimu Turaki, ya tsayar da dan takarar gwamna a jihar Gombe.

Tsagin jam'iyyar PDP ƙarƙashin jagorancin Tanimu Turaki ya gabatar da Mohammed Yayari a matsayin ɗan takarar gwamnan jam'iyyar a jihar Gombe.

Hakan yana zuwa ne bayan da tsagin PDP ƙarƙashin jagorancin Nyesom Wike ya sanar da tsohon Ministan sadarwa, Isa Pantami, a matsayin mai rike da tutar PDP a jihar Gombe.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com