‘Yanzu Lagos Ta Fi Karfinka’: Fadar Shugaban Kasa ga Peter Obi kan Zaben 2027

‘Yanzu Lagos Ta Fi Karfinka’: Fadar Shugaban Kasa ga Peter Obi kan Zaben 2027

  • Fadar Shugaban Ƙasa ta yi martani ga wasu da ke daukar dan takarar shugaban kasa a NDC, Peter Obi a matsayin barazana
  • Mai bai wa shugaban ƙasa shawara kan yaɗa labarai, Sunday Dare, ya ce nasarorin gwamnatin Tinubu sun ba ta kwarin gwiwar samun nasara a zaɓe
  • Dare ya kuma soki kalaman Peter Obi, yana mai cewa ba zai sake kayar da Tinubu a Lagos kamar yadda ya yi a 2023 ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Abuja - Fadar Shugaban Ƙasa ta bayyana yadda ta ke kallon Peter Obi a yanzu bayan lashe zabe a Lagos a shekarar 2024.

Fadar ta yi watsi da zargin cewa ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar NDC, Peter Obi, barazana ce ga gwamnatin Bola Ahmed Tinubu gabanin zaɓen 2027.

Kara karanta wannan

Bayan shekaru 53, Tinubu ya amince da canza fasalin aikin bautar kasa na NYSC a Najeriya

Fadar shugaban kasa ta kaskantar da Peter Obi
Dan takarar shugaban kasa a NDC, Peter Obi da Bola Tinubu. Hoto: Mr Peter Obi, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu.
Source: Twitter

Mai bai wa shugaban ƙasa shawara kan harkokin yaɗa labarai da sadarwa, Sunday Dare, ya bayyana haka a wata hira da Mic On Podcast wanda Tribune ta bibiya.

Bangaren da Tinubu ya fi mayar da hankali

Tsohon ministan ya ce gwamnatin Tinubu ta fi mayar da hankali kan gudanar da mulki kamar yadda ya dace ga yan Najeriya.

Sunday Dare ya ce a yanzu ba su tsoron Peter Obi ko da kuwa a baya ya zama barazana saboda yadda gwamnatin Tinubu ta mayar da hankali wurin ayyukan alheri ga yan kasa.

Ya ce:

"Wannan gwamnati ba ta tsoron Peter Obi. Ba ya zama abin fargaba ga gwamnatinmu. Wataƙila a baya Peter Obi ya kasance barazana, amma a yanzu ba ya zama wata barazana saboda muna tsaye ne a kan tubalin kyakkyawan aiki da nasarorin da muka samu."
Hadimin Tinubu ya fadi kokarin gwamnatinsu a Najeriya
Hadimin Bola Tinubu a Najeriya, Sunday Dare. Hoto: Sunday Dare.
Source: Facebook

Nasarorin da gwamnatin Tinubu ta samu

Dare ya ce gwamnatin ta samu nasarori da suka ba ta ƙarfin gwiwa, yana mai cewa Peter Obi ba ya zama abin tsoro ga gwamnatin saboda ayyukan da aka gudanar.

Kara karanta wannan

Fada zai dawo: Trump ya yi gargadi mai tsauri kan Iran duk da maganar sulhu

Ya ce gwamnatin ta tantance manyan matsalolin Najeriya tare da ƙaddamar da manufofi da shirye-shiryen magance su, kuma tana da sakamakon ayyuka da za ta nuna.

Sunday Dare ya kuma soki kalaman Peter Obi, yana mai cewa yawancin hirarrakinsa da martaninsa ba su da cikakken ma'ana ko sahihin tsari.

Ya bayyana cewa Peter Obi ba zai sake maimaita nasarar da ya samu a Legas a zaɓen shugaban ƙasa na 2023 ba, inda ya doke Bola Tinubu a wancan lokaci.

"Peter Obi ya doke Shugaba Bola Tinubu a Lagos a zaɓen 2023. Amma wannan shekarar 2026 ce, hakan ba zai sake faruwa ba."

- Sunday Dare

Dare ya nuna ƙwarin gwiwar cewa hakan ba zai sake faruwa ba a zaɓe mai zuwa, yana mai cewa gwamnatin na da cikakken tabbacin samun nasara a 2027, cewar Punch.

Fadar shugaban kasa ta kare kalaman Oluremi

Mun ba ku labarin cewa Fadar Shugaban Kasa ta kare kananan sana'o'i, tana cewa akwai mutunci a cikinsu bayan kalaman Sanata Oluremi Tinubu.

Mai ba shugaban kasa shawara, Sunday Dare, ya ce an fahimci kalaman Uwargidan Shugaban Kasa ba daidai ba.

Fadar Shugaban Kasa ta ce sana'o'in akara, masara da kuli-kuli na samar wa miliyoyin 'yan Najeriya abin dogaro da kuma tallafa wa tattalin arziki.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.