An Shigar da Ƙara a Jihar Kano, Ana Neman Hana Shugaba Tinubu Takara a Zaben 2027

An Shigar da Ƙara a Jihar Kano, Ana Neman Hana Shugaba Tinubu Takara a Zaben 2027

  • Kungiyar CFRPA ta sake taso da batun ingancin shaidar digirin shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu da sauran takardun karatunsa
  • CFRPA ta shigar da kara gaban babbar kotun tarayya mai zama a Kano, tare da neman a hana Tinubu shiga zaben shugaban kasa a 2027
  • Ta shaidawa kotu cewa tana zargin takardun karatun digirin Tinubu ba su da inganci, kuma ba shi da shaidar kammala karatun sakandire

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Kano, Nigeria - Wata ƙungiya mai suna Centre for Reform and Public Advocacy (CFRPA) ta shigar da ƙara a Babbar Kotun Tarayya da ke Kano kan takarar Shugaba Bola Ahmed Tinubu.

Kungiyar CFRPA ta nemi kotun ta hana Shugaba Bola Tinubu tsayawa takarar shugaban ƙasa a zaɓen 2027 bisa zargin gabatar da takardun karatu na bogi.

Kara karanta wannan

2027: An miƙa bukata ga Kwankwaso da Obi bayan an fara jita jitar za su fice daga NDC

Shugaba Tinubu.
Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu yana jawabi a wurin taro Hoto: @aonanuga1956
Source: Facebook

A cewar takardun shari’ar da Daily Trust ta gani, ƙungiyar ta yi zargin cewa Tinubu ya gabatar wa Hukumar Zaɓe (INEC) takardar shaidar karatu daga Jami'ar jihar Chicago (CSU) ta bogi.

A cewar kungiyar, tana zargin takardar digirin Tinubu da kuma takardar kammala bautar ƙasa (NYSC) da ya gabatar wa INEC a lokacin zaɓen 2023 duk ba masu inganci ba ne.

An shigar da ƙarar Tinubu a Kano

Karar mai lamba FHC/K/CS/312/2026 da kungiyar CFRPA ta shigar ta ambaci Shugaba Tinubu, INEC da Jami'ar jihar Chicago da ke kasar Amurka a matsayin waɗanda ake tuhuma.

Ƙungiyar ta kuma yi iƙirarin cewa Tinubu bai halarci kwalejin Lagos kamar yadda aka bayyana ba, tana mai cewa an kafa makarantar ne a 1974, shekaru huɗu bayan lokacin da ake ikirarin ya kammala karatu daga can.

Har ila yau, ƙungiyar ta ce Tinubu ba shi da sahihiyar takardar kammala sakandare, wadda ta ce ita ce mafi ƙarancin sharadin da kundin tsarin mulki ya tanada ga mai neman kujerar shugaban ƙasa.

Kara karanta wannan

Sarkin Musulmi ya yi magana kan kashe malamar Islamiyya a Kaduna

CFRPA ta zargi hukumar INEC

A cewar masu ƙarar, sun rubuta wa INEC wasiƙa a ranar 19 ga Yunin 2026, domin neman hukumar ta fayyace matsayar ta kan cancantar Tinubu, amma har yanzu ba su samu amsa ba.

Ƙungiyar ta kuma dogara da hukuncin wata kotu a Amurka da aka yanke 2023, wanda ya umarci jami'ar Chicago ta fitar da bayanan karatun Tinubu.

Ta ce bayanan da aka fitar sun nuna wasu bayanai da take zargin ba su dace ba, ciki har da takardar General Certificate of Education ta jami'ar Cambridge da ta yi zargin an ƙirƙira.

Kotu.
Gudumar da alkalai ke amfani da ita a kotunan Najeriya Hoto: Anadolu
Source: Getty Images

Abubuwan da masu ƙarar ke nema

A cikin ƙarar, CFRPA ta roƙi kotu da ta ayyana cewa takardar shaidar digirin Tinubu a jami'ar Chicago ba sahihiya ba ce kuma ta umarci INEC ta hana shi tsayawa takarar shugaban ƙasa a 2027.

Haka nan kuma ta nemi kotun ta umarci jami'ar Chicago ta cire sunan Tinubu daga bayananta sannan ta hana INEC sanya sunan Tinubu cikin jerin 'yan takarar shugaban ƙasa, cewar rahoton Punch.

Kara karanta wannan

Gombe: Batun takarar Farfesa Pantami a jam'iyyar PDP ya kai gaban kotu

An hango faduwar Tinubu a zaben 2027

A wani labarin, kun ji cewa jagoran NDC na ƙasa, Sanata Seriake Dickson, ya ce shugaba Bola Tinubu da APC za su sha kaye idan aka gudanar da sahihin zaɓe a 2027.

Tsohon gwamnan na jihar Bayelsa, Dickson ya ce rashin gamsuwar da jama'a ke yi da gwamnatin APC zai haifar da faduwar jam'iyyar mai mulki a zaɓe.

Sanatan ya buƙaci a bai wa dukkan jam'iyyun adawa damar shiga zaɓe ba tare da jawo masu matsala ba, yana mai cewa sun shirya tsaf.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262