Sojoji Sun Ceto Daliban da Aka Sace a Borno bayan Ritsa 'Yan Ta'addan ISWAP cikin Daji
- 'Yan ta'addan kungiyar ISWAP sun sace wasu dalibai da malamai a wata makarantar sakandare da ke jihar Borno
- Dakarun sojoji sun bi sahun 'yan ta'addan bayan samun labarin barnar da suka yi a karamar hukumar Askira/Uba
- Sojojin sun samu nasarar ceto wasu daga cikin dalibai da malaman da 'yan ta'addan suka sace bayan an yi musayar wuta a cikin daji
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Borno - Dakarun sojoji na rundunar ‘Operation Hadi Kai (OPHK) sun ceto ɗalibai masu rubuta jarabawar NECO da malamai guda 10 da aka sace a Borno.
Daliban da malaman da sojoji suka ceto na daga cikin waɗanda ake zargi 'yan ta'addan ISWAP ne suka yi garkuwa da su lokacin wani hari da suka kai garin Lassa da ke yankin karamar hukumar Askira/Uba a jihar Borno.

Source: Twitter
Masani kan harkokin tsaro a yankin Tafkin Chadi da Arewacin Najeriya, Zagazola Makama, ne ya bayyana hakan a shafinsa na X.
'Yan ISWAP sun sace dalibai a Borno
Majiyoyi sun bayyana cewa 'yan ta'addan sun afkawa makarantar sakandaren kimiyya da fasaha da ke Lassa da misalin ƙarfe 9:00 na safe a ranar Litinin, 29 ga watan Yunin 2026 yayin da ɗalibai ke tsaka da rubuta jarabawar NECO.
'Yan ta'addan sun yi garkuwa da ɗalibai da malamai da dama kafin su tsere zuwa cikin dajin da ke kewaye.
Sojoji sun fafata da 'yan ta'adda a daji
Bayan karɓar rahoton neman agajin gaggawa, hedkwatar rundunar Operation Hadin Kai cikin hanzari ta ƙaddamar da aikin haɗin gwiwa na bincike da ceto.
Majiyoyin sun ce sakamakon jagorancin sanya idanu na kai-tsaye daga sararin sama, dakarun soji sun gamu da 'yan ta'addan a kewayen yankin Daggu, inda aka yi musayar wuta.
Dakarun sun fi ƙarfin 'yan ta'addan, inda suka yi nasarar raunatawa tare da kashe wasu 'yan ta'addan da ke tserewa tare da tilasta musu barin wasu daga cikin mutanen da suka sace.
An ceto wasu daga cikin daliban
Samamen ya kai ga nasarar ceto mutane 10 da aka yi garkuwa da su, waɗanda suka haɗa da ɗalibai da malamai, waɗanda aka gano ba su samu wani rauni ba kuma a halin da ake ciki suna karɓar kulawar lafiya da ta dace.
Yayin bin sawun, dakarun sojoji sun kuma ƙwato babura guda bakwai mallakin 'yan ta'addan, lamarin da ya kawo babban cikas ga zirga-zirga da tserewarsu.

Source: Original
Sai dai kuma, samamen ya jawo asarar rayuka a ɓangaren dakarun tsaro, duba da cewa soja guda ɗaya da kuma wani mamba na CJTF sun sadaukar da rayukans yayin fafatawa da 'yan ta'addan.
Majiyoyin sun ce dakarun sun ci gaba da mamaye yankin baki ɗaya da daukacin hanyoyin da ake zargin za su bi domin tserewa, yayin da aka tura ƙarin sojoji domin kara matsa lamba kan 'yan ta'addan da ke tserewa.
Sojoji sun dakile harin 'yan ta'adda
A wani labarin kuma, kun ji cewa dakarun sojoji na Operation Whirl Stroke tare da haɗin gwiwar 'yan sa-kai sun dakile wani hari da ake zargin 'yan ta'adda ne suka shirya shi a Benue.
Sojojin sun kashe mutane biyu da ake zargi 'yan bindiga ne tare da ƙwato makamai da alburusai a wani samame da suka gudanar.
An gudanar da samamen ne bayan samun kiran neman agaji yayin da sojojin ke sintiri domin yaƙi da kuma ƙarfafa amincewar jama'a.
Asali: Legit.ng


