Takarar Gwamna Ta Barka Gidan Tsohon Shugaban Kasar Najeriya Obasanjo
- A zaben 2027, sanannen ‘dan majalisar dattawa a Najeriya, Solomon Adeola ne zai yi takarar gwamnan jihar Ogun a APC
- Wasu daga cikin ‘ya ‘yan tsohon shugaban kasa, Olusegun Obasanjo suna goyon bayan Sanata Yayi a karkashin jam’iyyar APC
- Sanata Iyabo-Obasanjo kuwa ba ta tare da ‘yanuwanta duk da cewa ta taba zama a APC kafin sauya-shekarta zuwa PDP
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
M. Malumfashi ya shafe shekaru 10 yana kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada
Ogun - Iyalin tsohon shugaban kasar Najeriya Olusegun Obasanjo sun samu kan su a rudani a sakamakon neman takarar gwamnan jihar Ogun.
A halin yanzu dai kusan an tsaida takara, ana shirin zaben sabon gwamna da zai gaji Dapo Abiodun wanda yake wa’adinsa na karshe a gidan gwamnati.

Source: Getty Images
Premium Times ta rahoto cewa akwai sabanin siyasa a gidan Olusegun Obasanjo wanda ya mulki Najeriya a zamanin mulkin soja da kuma farar hula.
Wasu yaran Olusegun Obasanjo sun bi APC
Sanata Solomon Adeola wanda yake rike da tutar APC a zaben gwamnan Ogun ya samu goyon bayan wasu daga cikin ‘ya ‘yan tsohon shugaban.
Olugbenga Obasanjo da Olujuwon Obasanjo sun ziyarci ‘dan takaran na APC, kuma suka nuna masa cewa sun yi masa mubaya’a a zaben 2027.
Hakan na zuwa ne kwanaki bayan yayarsu ta yi watsi da jam’iyyar APC, a karshe ta koma PDP.
‘Dan takaran ya sanar cewa a shafin Facebook:
“Ina mai alfarin karbar tatson babanmu kuma tsohon shugaban kasar Najeriya, Cif Olusegun Obasanjo GCFR, a gidana a Abeokuta a yau.
Dr Olugbenga Obasanjo da Mr Olujuwon Obasanjo sun ziyarce ni domin jinjina wa namijin kokari na wajen shugabanci kuma su yi mani cikakkiyar mubaya’a na takarar gwamnan jihar Ogun 2027.
Iyabo Obasanjo ba ta tare da 'yanuwanta
Jawabin ya gode wa ‘ya ‘yan tsohon shugaban kasar, amma PM News ta ce matakin nasu ya nuna bambancin ra’ayin siyasa da ya keta gidan Obasanjo.

Kara karanta wannan
Takarar Gwamna: Yadda jam'iyyar ADC ta tsumbula cikin rikicin gida a jihar Katsina
Sanata Iyabo Obasanjo ta shiga APC kuma ta nemi takarar gwamna a jam’iyyar mai rike da mulki, amma sai aka yi amfani da tsarin maslaha wajen bada tikiti.

Source: Facebook
Tsohuwar sanatar kuma farfesa ta soki yadda aka fito da ‘dan takarar gwamnan, ta yi ikirarin cewa an saba wa tsarin da jam’iyyar APC ta gidanya da kan ta.
Bayan ‘yan kwanaki sai aka ji cewa ta rabu da jam’iyyar, sannan ta koma PDP inda a nan ta fara siyasa har ta je Majalisar dattawa daga 2007 zuwa 2011.
Shi dai Olusegun Obasanjo bai nuna cewa yana goyon bayan Sanata Yayi a zaben ba, asali ma a lokacin aka gan shi tare da Rabiu Kwankwaso na NDC.
Obi/Kwankwaso za su sake canza sheka?
Labari ya zo cewa cewa kakaki a NDC ya maida wa Bashir Ahmad martani, Theo Agbada ya fada masa Rabiu Kwankwaso da Peter Obi ba za su canza sheka ba.
Jam’iyyar NDC ta tanka jita-jitar cewa Kwankwaso zai sulale zuwa PRP saboda hukuncin kotun tarayya da ya soke masu rajista a ranar Juma’ar da ta wuce.
Wasu suna ganin duk abin da zai faru sai Peter Obi ya yi takarar shugaban kasa a zaben 2027 kamar yadda ya yi wa magoya bayansa alkawari tun tuni.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
