'Za a Kayar da Tinubu Warwas a Zaben 2027,' Sanata Dickson na NDC
- Jagor NDC na ƙasa, Sanata Seriake Dickson, ya ce shugaba Bola Tinubu da APC za su sha kaye idan aka gudanar da zaɓen 2027 cikin gaskiya
- Sanatan ya buƙaci a bai wa dukkan jam'iyyun adawa damar shiga zaɓe ba tare da jawo masu matsala ba, yana mai cewa sun shirya tsaf
- Maganganun jagoran na zuwa ne a daidai lokacin da NDC ta shiga cikin rudanin siyasa bayan kotu ta yi umarni a soke rajistar jam'iyyar
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja - Jagoran Jam'iyyar NDC, Sanata Seriake Dickson, ya bayyana ƙwarin gwiwarsa cewa Shugaba Bola Tinubu da jam'iyyar APC mai mulki za su sha kaye a babban zaɓen 2027.
Sanata Seriake Dickson ya bayyana cewa Bola Tinubu zai fadi ne idan aka gudanar da zaɓen 2027 cikin 'yanci, gaskiya da adalci.

Source: Facebook
Da yake magana a shirin Sunday Politics na tashar Channels Television, Dickson ya ce rashin gamsuwar da jama'a ke yi da gwamnatin APC zai haifar da faduwar jam'iyyar mai mulki a zaɓe.
'Tinubu zai fadi a 2027,' Dickson
Yayin da ya ke magana kan yiwuwar faduwar Bola Tinubu da jam'iyyar APC a zaben 2027, Sanata Dickson ya ce 'yan Najeriya suna shan wahala sosai.
“A matsayina na shugaban NDC, kuma a matsayina na ɗan Najeriya da ya san yadda 'yan Najeriya ke ji da abin da suke buri, kuma wanda ya san cewa ba a cimma burinsu ba, mun yi imanin cewa gwamnatin APC da jam'iyyar APC baki ɗaya, ba shugaban ƙasa kaɗai ba, za su sha kaye warwas,”
In ji shi.
Maganar shiga zaben 2027
Sanatan ya yi kira da a samar da tsarin dimokuraɗiyya a buɗe, inda ya buƙaci hukumomi su bai wa dukkan jam'iyyun siyasa da ke son yin takara damar shiga zaɓe ba tare da katsalandan ba.
Vanguard ta rahoto ya kara da cewa:
“Ku bar kowace jam'iyya da ke son yin takara ta yi. Hanyar kayar da su ita ce a zaɓe. Don haka mu gudanar da zaɓe cikin 'yanci da adalci,”
Ya bayyana haka ne yayin da 'yan adawa ke cigaba da fuskantar kalubalen zuwa kotu da sauransu game da rikicin cikin gida gabanin zaben 2027 da ke tafe.
A yanzu haka dai manyan jam'iyyun adawa a Najeriya kamar NDC ta Peter Obi da Rabiu Kwankwaso da ADC ta su Atiku Abubakar na fama da shari'o'i.

Source: Facebook
Obi ya nemi muhawara da Tinubu
A wani labarin, kun ji cewa dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar NDC, Peter Obi ya kalubalanci shugaba Bola Tinubu su yi muhawara.
Obi ya bayyana cewa ba neman mulki ba ne ya sanya shi fitowa takarar shugaban kasa a zaben 2027 ba, sai domin kawo cigaba Najeriya.
Maganganun Obi na zuwa ne a lokacin da ake cigaba da tattauna batun zaben 2027 da kalubalen da 'yan jam'iyyun adawa ke fuskanta.
Asali: Legit.ng

