Da Yiwuwar Trump Ya Gana da Tinubu bayan Hare Haren da Amurka Ta Kawo Najeriya

Da Yiwuwar Trump Ya Gana da Tinubu bayan Hare Haren da Amurka Ta Kawo Najeriya

  • Shugaba Bola Ahmed Tinubu da takwaransa na Amurka, Donald Trump na iya haduwa ido da ido domin tattauna muhimman batutuwa
  • Jakadan Najeriya a kasar Amurka, Ambasada Kayode Are ne ya bayyana hakan, inda ya ce yana fatan Tinubu zai ziyarci Trump nan gaba
  • Ya ce ziyarar za ta ƙara ƙarfafa haɗin gwiwar Najeriya da Amurka, musamman a fannonin siyasa, tattalin arziki, kasuwanci, zuba jari da kuma tsaro

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja, Nigeria - Jakadan Najeriya a Amurka, Ambasada Kayode Are, ya bayyana cewa da yiwuwar Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya kai ziyarar aiki a birnin Washington kafin ƙarshen wa'adinsa.

Jakadan ya tabbatar da cewa kyakkyawar alaƙar diflomasiyya tsakanin Najeriya da Amurka ta samar da ingantacciyar damar kai wannan ziyara.

Trump da Tinubu.
Shugaban Amurka, Donald Trump da takwaransa na Najeriya, Bola Ahmed Tinubu Hoto: @aonanuga1956
Source: Twitter

Ya bayyana hakan ne yayin wata hira a shirin Inside Sources with Laolu Akande na gidan talabijin na Channels.

Kara karanta wannan

"Ba haka Buhari da Jonathan suka yi ba," Atiku Abubakar ya aika sako ga Shugaba Tinubu

Da yiwuwar Tinubu ya ziyarci Amurka

Are ya ce duk da cewa shirye-shiryen tafiye-tafiyen shugabannin ƙasa sun dogara ne kan muhimman batutuwa, dangantakar da ke tsakanin Shugaba Bola Tinubu da Shugaban Amurka Donald Trump na ƙara kyau.

Ya ce:

“Saboda kyakkyawar dangantakar da ke tsakanin shugabannin biyu, na yi imanin za a samu damar hakan ta wata hanya. Shirye-shiryen tafiye-tafiyen shugaban ƙasa ne ke tantance inda zai je ko ba zai je ba.
“A yanzu akwai kyakkyawar hulɗa da tattaunawa tsakanin ƙasashen biyu a matakai daban-daban, ko da yake ba a ga shugabannin biyu sun haɗu ido da ido ba. Ina fatan kafin ƙarshen wa'adina zan samu damar tarbar shugaba Tinubu a nan (Amurka).”

Amfanin ganawar Tinubu da Trump

Jakadan ya ce ziyarar shugaban ƙasa za ta ƙara ƙarfafa haɗin gwiwar Najeriya da Amurka, musamman a fannonin siyasa, tattalin arziki, kasuwanci, zuba jari da kuma tsaro.

Ya kuma tuna da tasirin rashin cikakken jakadan Najeriya a Washington na tsawon shekaru uku, yana mai cewa hakan ya raunana hulɗar diflomasiyya tare da kawo tsaiko ga ayyukan ofishin jakadancin.

Kara karanta wannan

NASFAT ta ja hankalin musulmai, ta nemi su taimaka kan matsalar tsaron Najeriya

Illar rashin tura Jakada Amurka

A cewarsa, ma'aikata da dama da aka tura daga Najeriya ba su taɓa yin aiki ƙarƙashin cikakken jakada ba

“Har yanzu ina jin tasirin rashin jakada na tsawon shekaru uku. Wasu daga cikin ma'aikatanmu ba su taɓa yin aiki da cikakken jakada ba, saboda haka sabon darasi ne gare su. Tasirin hakan a bayyane yake," in ji Are.

Ya ce jakadu na taka muhimmiyar rawa wajen bunƙasa hulɗar siyasa tsakanin ƙasashe, jawo masu zuba jari, bunƙasa kasuwanci da kuma kare muradun ƙasarsu.

Shugaba Tinubu.
Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu a wani taro da ya halarta a kasar waje Hoto: @aonanuga1956
Source: Twitter

Daily Trust ta ruwaito cewa Najeriya ta shafe lokaci ba tare da cikakken jakada a Amurka ba tun bayan da aka dawo da jakadunta gida a shekarar 2023, kafin daga bisani aka naɗa Kayode Are.

Ɗan Majalisar Amurka ya yabawa Tinubu

A wani rahoton, kun ji cewa ɗn majalisar dokokin Amurka, Riley Moore Wanda ya saka Najeriya a gaba kwanakin baya, ya yaba da matakin Bola Ahmed Tinubu kan tsaro.

Kara karanta wannan

Manyan abubuwa 4 da ka iya ruguza yarjejeniyar kasar Musulunci ta Iran da Amurka

Moore ya yaba da matakin da Majalisar Wakilan Najeriya ta dauka na amincewa da kudirin kafa rundunar ‘yan sandan jihohi.

Moore ya bayyana cewa wannan mataki ne mai muhimmanci da zai taimaka wajen magance matsalolin rashin tsaro a Najeriya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262