Magana Ta Girma: An Bukaci Hukumomin Tsaro Su Cafke Sheikh Jingir

Magana Ta Girma: An Bukaci Hukumomin Tsaro Su Cafke Sheikh Jingir

  • Ana ci gaba da muhawara da cece-kuce kan kalaman da Sheikh Sani Yahaya Jingir ya yi wajen tallata muslim-muslim
  • Hukumar NHRC ta ce kalaman malamin addinin sun hada da kira ga siyasar da ta ware wasu addinai da kuma tunzura magoya baya
  • NHRC ta gargadi shugabannin addini, sarakuna da ’yan siyasa kan kalaman da za su iya raba kan ’yan Najeriya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

FCT, Abuja - Gabanin babban zaben 2027, Hukumar Kare Hakkin Dan Adam ta Kasa (NHRC) ta yi magana kan kalaman da Sheikh Sani Yahaya Jingir ya yi.

NHRC ta bukaci gwamnatin tarayya da ta gaggauta kama tare da gurfanar da Sheikh Yahaya Jingir, kan zargin kalaman kiyayya da tunzura jama’a.

An bukaci a cafke Sheikh Jingir
Shugaban kungiyar Izala bangaren Jos, Sheikh Sani Yahaya Jingir Hoto: Jibwis Hq Jos
Source: Facebook

Hukumar ta bayyana hakan ne a wata sanarwa da Sakataren zartaswarta, Chief Tony Ojukwu, SAN, ya sanya wa hannu ranar Talata, 11 ga watan Agustan 2026 a shafinta na intanet.

Kara karanta wannan

EU ta janye daga sanya ido kan zaben 2027 a Najeriya? An ji yadda lamarin yake

NHRC ta yi Allah wadai da kalaman Jingir

NHRC ta ce ta yi Allah-wadai matuka da “kalaman kiyayya da tunzura jama’a” da ta ce malamin ya yi a wani bidiyo da ya yadu a ranar Lahadi.

Hukumar ta ce ta kalli bidiyon cikin matukar damuwa, inda ta ce malamin ya fito fili yana neman goyon bayan siyasar da ta ware wasu addinai gabanin babban zaben da ke tafe.

Ta kuma ce ya yi amfani da kalmar wulakanci ta “kafirai” tare da kira ga magoya bayansa da su mallaki katin zabe domin su “nuna masu iyakarsu”.

NHRC ta soki kalaman Sheikh Jingir

Hukumar kare hakkin dan adam ta bayyana cewa kalaman sun saba wa ka'idojin daidaito, rashin nuna wariya da zaman lafiya da kundin tsarin mulkin Najeriya na 1999, kamar yadda aka yi masa gyara, ya tanada.

Ta ce kalaman sun kuma saba wa wasu alkawuran Najeriya na kasa da kasa kan kare hakkin dan adam.

Kara karanta wannan

Kwankwaso ya zargi Jingir da rura wutar rikici bayan kalamansa kan Muslim Muslim

“Kwamitin ya gano cewa wadannan kalamai kalaman kiyayya ne da tunzura kiyayyar addini da kuma yiwuwar haifar da tashin hankali.

“A daidai lokacin da muke shirin sake gudanar da babban zabe, irin wadannan kalamai sakaci ne kuma suna da hadari,” in ji hukumar.

NHRC ta kara da cewa irin wadannan kalamai ba su da wata manufa face raba kan ’yan Najeriya bisa addini da kuma jefa su gaba da juna.

An gargadi malamai da ’yan siyasa

Hukumar ta ce bai kamata a yi shiru kan irin wadannan kalamai ba, tana mai gargadin cewa rashin daukar mataki zai iya karfafa wasu malaman addinin Kirista da Musulmi da sauran masu tasiri su rika yin kalamai mafi muni a watannin da ke tafe.

Saboda haka, NHRC ta bukaci Sufeto-Janar na ’Yan Sandan Najeriya, Darakta-Janar na Hukumar Tsaro ta Kasa (DSS) da sauran hukumomin da abin ya shafa da su gaggauta kama tare da gurfanar da Sheikh Jingir kan zargin kalaman kiyayya da tunzura jama’a.

Hukumar ta kuma roki shugabannin addini, sarakunan gargajiya da ’yan siyasa da su guji kalaman da ke raba kan jama’a.

Kara karanta wannan

Ana shirin 2027, an gano bindigogi 399 da aka yi shirin kawowa Najeriya

Haka zalika, ta bukaci ’yan Najeriya da su yi watsi da siyasar da ta dogara kan kabila ko addini, tare da rike shugabanni da alhaki bisa cancanta, ingancin ayyukan da suke samarwa da kuma mutunta hakkin dan adam.

Ana ta maganganu kan Sheikh Jingir
Sheikh Sani Yahaya Jingir a masallaci Hoto: Jibwis Hq Jos
Source: Facebook

Adeyanju ya soki Sheikh Jingir

A wani labarin kuma, kun ji cewa lauyan kare hakkin ɗan Adam, Deji Adeyanju, ya yi Allah-wadai da kalaman da malamin addinin Musulunci, Sheikh Yahya Jingir, ya yi kan muslim-muslim.

Deji Adeyanju ya yi gargadin cewa kalaman addini da za su iya ƙara kawo rarrabuwar kawuna da za su iya barazana ga haɗin kan Najeriya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng