An Fasa Ƙwai: Yadda Atiku Ya So Ɗaukar Mace a matsayin Abokiyar Takararsa a 2027
- Rahotanni sun ce Atiku Abubakar ya kusa daukar wata kwararriya daga yankin Kudu maso Gabas a matsayin mataimakiyarsa
- Wasu jiga-jigan ADC sun nemi a zaɓi ɗan Kudu maso Gabas, inda aka ambaci Ngozi Okonjo-Iweala, Ben Obi, Emeka Ihedioha da Liyel Imoke
- Daga ƙarshe dattawan jam'iyyar sun ba da shawarar zaɓen Amaechi domin kauce wa sabanin cikin gida da ƙarfafa haɗin kan jam'iyyar
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
Abuja - Rahotanni sun bayyana cewa jam'iyyar ADC ta fuskanci tattaunawa da rikice-rikice kafin ta amince da tsohon ministan sufuri, Rotimi Amaechi.
An tabbatar da cewa Atiku Abubakar ya so daukar wata kwararriya daga yankin Kudu maso Gabashin kasar a matsayin mataimakiyarsa.

Source: Facebook
An so zabar Okonjo-Iweala a matsayin mataimakiyar Atiku
Majiyoyi daga jam'iyyar sun ce wasu na kusa da Atiku sun yi imanin cewa ya dace a zaɓi mataimaki daga yankin Kudu maso Gabas domin ƙarfafa damar jam'iyyar a zaɓen 2027, cewar Tribune.
Saboda haka aka fara ambaton sunayen Sanata Ben Obi, Emeka Ihedioha da tsohuwar ministar kuɗi, Dakta Ngozi Okonjo-Iweala, domin cike gurbin mataimakin ɗan takara.
Wata majiya ta ce idan ɗan takarar Kudu maso Gabas bai yiwu ba, sai aka ba da shawarar tsohon gwamnan Cross River, Sanata Liyel Imoke.
An kuma ce wasu shugabannin jam'iyyar sun kai ziyara ga Okonjo-Iweala a lokacin bikin ranar haihuwarta, inda suka tattauna yiwuwar shiga takarar.
Sai dai rahotanni sun ce Okonjo-Iweala ba ta amince ko ta ƙi ba, illa ta shawarci tawagar da su ci gaba da yin faɗaɗɗen tuntuba a faɗin ƙasar, cewar Vanguard.
Daga bisani dattawan jam'iyyar suka ba da shawarar kada a ɗauki matakin da zai iya haddasa ƙarin rarrabuwar kai, lamarin da ya sa aka zaɓi Amaechi.

Source: Twitter
Kusancin Atiku Abubakar Rotimi da Amaechi
Majiyar ta ƙara da cewa Atiku Abubakar ya ci gaba da kasancewa cikin kusanci da Amaechi a duk lokacin tattaunawar, abin da ya taimaka wajen kammala zaɓin cikin lumana.
Wata majiya ta ce:
"Matakin da ADC ta ɗauka na zaɓar Amaechi bai kasance mai sauƙi kamar yadda mutane suka ɗauka ba. Ko da yake tun farko ya bayyana a matsayin wanda ya fi dacewa, kasancewarsa wanda ya zo na biyu a zaɓen fidda gwani kuma fitaccen ɗan takara daga Kudancin ƙasar.

Kara karanta wannan
Yadda Atiku ya kusa zabar tsohuwar Minista a matsayin abokiyar takara a zaben 2027
"Sai dai wasu ƙungiyoyi a cikin jam'iyyar sun yi imanin cewa ɗan takara daga Kudu maso Gabas zai fi amfani ga jam'iyyar.
"Saboda haka suka tsara wani shiri na shigar da Ngozi Okonjo-Iweala cikin takara domin ta zama mataimakiyar Atiku Abubakar."
Atiku ya soki salon mulkin Bola Tinubu
A wani labarin, an ji cewa dan takarar shugaban kasa, Atiku Abubakar ya zargi gwamnatin shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu da yunkurin maida Najeriya tsarin jam'iyya daya.
Dan takarar shugaban kasa na jam'iyar ADC ya nuna damuwa kan yunkurin soke rijistar NDC ta hanyar amfani da kotu.
Atiku ya bukaci Shugaba Tinubu ya yi koyi da tsofaffin shugabannin Najeriya, Muhammadu Buhari da Goodluck Jonathan.
Asali: Legit.ng
