Kwankwaso Ya Yi Magana kan Shari'ar NDC, Ya Aika Sako ga Magoya Baya

Kwankwaso Ya Yi Magana kan Shari'ar NDC, Ya Aika Sako ga Magoya Baya

  • Jagoran Kwankwasiyya a Najeriya, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya ce jam'iyyar NDC za ta shawo kan matsalolin shari'ar da suka sako ta a gaba
  • Ya bayyana haka ne a lokacin da NDC ke kici-kici da batun kotu bayan an jingine batun yi wa jam'iyyar rajista yayin da ake shirin tunkarar zabe mai zuwa
  • Sanata Kwankwaso, wanda ya kwantar da hankalin magoya bayan NDC ya ce ajwai cikakken yakinin za a samu nasara a dukkanin kalubalen da suka tunkaro su

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kano – Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, mataimakin dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar NDC, ya tabbatar wa magoya bayansu cewa za a shawo kan matsalolin shari'a da suke fuskanta.

Ya bayyana haka ne bayan wasu manyan kalubale sun sako NDC a gaba gabanin shirin babban zaben 2027 da ke tunkaro 'yan Najeriya.

Kara karanta wannan

2027: 'Yan takarar NDC sun gamu da matsala bayan INEC 'ta hana' a shigar da sunayensu

Sanata Kwankwaso ya yi magana a kan kalubalen da suka tunkaro NDC
'Dan takarar mataimakin shugaban kasa a NDC, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso Hoto: @KwankwasoRM
Source: Twitter

Kwankwaso ya bayyana haka ne a wani sako da ya wallafa a shafinsa na X bayan ya kai ziyarar girmamawa ga jagoran jam'iyyar na kasa, Sanata Seriake Dickson, a gidansa da ke Abuja.

Kwankwaso ya ziyarci jagoran NDC

Jaridar Vanguard ta kawo lavarin cewa Kwankwaso ya ce ziyarar na daga cikin kokarin da shugabannin jam'iyyar ke yi domin kara dankon hadin kai, juriya da kuma shirye-shiryen tunkarar babban zaben shekarar 2027.

A cewar tsohon gwamnan jihar Kano:

"A yau na kai ziyarar girmamawa ga jagoran jam'iyyarmu ta NDC, Mai Girma Seriake Dickson, a gidansa da ke Abuja."

Ya kara da cewa:

"Wannan ganawar na daga cikin ci gaba da kokarinmu na karfafa hadin kai, juriya da kuma shirye-shiryen jam'iyya yayin da muke tunkarar babban zaben shekarar 2027."

Kiran Kwankwaso ga 'yan NDC

Kwankwaso ya bukaci dukkannin 'yan jam'iyya da magoya bayan NDC da su ci gaba da kasancewa cikin natsuwa duk da kalubalen da ake fuskanta.

Kara karanta wannan

Dan takarar majalisa da jiga jigan NDC sun sauya sheka zuwa jam'iyyar APC

Jagoran ya ce jamiyyar NDC na ci gaba da mutunta doka kuma tana da cikakken yakini da tsarin shari'ar Najeriya yayin da ta daukaka kara.

Kwankwaso ya shawarci yn NDC su kwantar da hankulansu
Peter Obi, Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso Seriake Dickson da sauran yan jam'iyya Hoto: @KwankwasoRM
Source: Twitter

Ya ce:

"A matsayinmu na masu bin tafarkin dimokuradiyya, muna ci gaba da mutunta doka kuma muna da cikakken yakini da tsarin shari'a. Babu wani kalubale na wucin gadi da zai iya raunana tafiyar da aka gina bisa fata, adalci, daidaito da kuma burin al'ummar Najeriya."

Obi da Kwankwaso sun tsaya kan NDC

A baya, mun wallafa cewa hukuncin alkalin Kotun Tarayya da ke Lokoja a jihar Kogi ya tada hankalin shugabanni da ‘ya ‘yan jam’iyyar NDC a Najeriya, musamman ganin ana dab da buga gangamin zaben 2027.

Kotu ta canza matakin da ta dauka a baya, inda a yanzu ta yi umarni a soke rajistar da aka yi jam'iyyar NDC ‘yan kwanaki bayan lamarin da ya jawo 'ya'yanta fara neman mafita ta hanyar daukaka kara.

Wani babba a jam’iyyar NDC ya shaida cewa jagorori irin su Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso da Peter Obi sun yi zaman gaggawa domin ganin an tunkari matsalar soke rajistar a Kotun Daukaka Kara.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng