‘Na Taya Uwata Sayar da Kosai’: Hadimin Tinubu Ya Kare Kalaman Oluremi

‘Na Taya Uwata Sayar da Kosai’: Hadimin Tinubu Ya Kare Kalaman Oluremi

  • Fadar Shugaban Kasa ta kare kananan sana'o'i, tana cewa akwai mutunci a cikinsu bayan kalaman Sanata Oluremi Tinubu
  • Mai ba shugaban kasa shawara, Sunday Dare, ya ce an fahimci kalaman Uwargidan Shugaban Kasa ba daidai ba
  • Fadar Shugaban Kasa ta ce sana'o'in akara, masara da kuli-kuli na samar wa miliyoyin 'yan Najeriya abin dogaro da kuma tallafa wa tattalin arziki

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Abuja - Fadar Shugaban Kasa ta yi martani game da kalaman matar shugaban kasa da suka jawo ce-ce-ku-ce a tsakanin al'umma.

Fadar ta nuna goyon baya ga bangaren kananan sana'o'i a Najeriya, tana mai cewa akwai mutunci a cikinsu duk da suka da aka yi wa kalaman Oluremi Tinubu.

Fadar shugaban kasa ta kare kalaman Oluremi Tinubu
Matar shugaban kasa, Sanata Oluremi Tinubu. Hoto: Sen. Oluremi Tinubu.
Source: Facebook

Hakan na cikin wata hira da mai ba Shugaba Bola Tinubu shawara kan yada labarai da hulɗar jama'a, Sunday Dare a shirin Mic-On Podcast wanda ya wallafa a Facebook.

Kara karanta wannan

An gano yadda aka bindige jigon APC a kofar gidansu bayan sauya jam'iyyar siyasa

Hadimin Tinubu ya tuna rayuwarsa ta baya

Sunday Dare ya bayyana cewa tun yana yaro a Jos, ya kan taimaka wa mahaifiyarsa sayar da akara, ayaba da lemu.

Tsohon ministan ya ce mutane da dama sun fahimci kalaman Uwargidan Shugaban Kasa ba daidai ba.

Ya ce manufarta ita ce karfafa dogaro da kai da kuma bunkasa sana'o'i, ba wai raina irin matsin tattalin arzikin da 'yan Najeriya ke fuskanta ba.

A cewarsa, kudin da ake samu daga wadannan kananan sana'o'i ne suka taimaka wa iyayensa wajen ciyar da iyali da kuma biya masa kudin karatu.

Ya ce:

"Babu wani laifi a sayar da akara, ayaba ko lemu. Mahaifiyata ta yi wannan sana'a, kuma ta hanyar haka ta samu damar karantar da ni."
Hadimin Tinubu ya tuna rayuwarsa ta baya
Tsohon minista kuma hadimin Bola Tinubu, Sunday Dare. Hoto: Sunday Dare.
Source: UGC

Dare ya shawarci yan kasa kan sana'o'i

Dare ya jaddada cewa miliyoyin 'yan Najeriya na samun halalcin abin rayuwa ta hanyar kananan kasuwanci da sauran sana'o'i masu sauki.

Ya bayyana bangaren kananan sana'o'i a matsayin daya daga cikin ginshikan da suka ci gaba da tallafa wa tattalin arzikin Najeriya duk da kalubalen da ake fuskanta.

Kara karanta wannan

Bayan Boko Haram, ISWAP da Lakurawa, sabuwar kungiyar 'yan ta'adda ta bayyana a Arewa

Kakakin shugaban kasar ya ce masu sukar Uwargidan Shugaban Kasa sun dauki kalamanta ba a mahallinsu ba, domin abin da take nufi shi ne mutane su koyi wata sana'a.

Ya ce:

"Kada ku juya ainihin sakon Uwargidan Shugaban Kasa. Abin da take nufi shi ne duk abin da za ka iya yi, ka yi shi, sannan ka mallaki wata kwarewar sana'a."

Kalaman nata sun biyo bayan suka daga wasu 'yan Najeriya da suka ce ba su magance manyan matsalolin tattalin arzikin kasar ba.

Sai dai duk da wannan suka, Fadar Shugaban Kasa ta nace cewa babu wata sana'a da ta yi kankanta, yayin da juriyar bangaren kananan sana'o'i ke ci gaba da samar wa miliyoyin 'yan Najeriya abin rayuwa.

Oluremi Tinubu ta kunyata gwamna a bainar jama'a

An ji cewa Gwamna Ademola Adeleke ya gamu da cikas daga wurin uwargidan shugaban kasa, Oluremi Tinubu a taron cikar Ooni na Ife shekara 10 a gadon mulki.

Lamarin ya faru ne lokacin da Gwamna Adeleke ke gabatar da jawabinsa, inda aka ga yana rawa a wurin taron wanda ya gudana.

A faifan bidiyon da ke yawo a kafafen sada zumunta, an ga yadda matar Tinubu ta taka wa Gwamna Adeleke burki saboda kurewar lokaci.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.