INEC Ta Dage Ranar ba Jam’iyyu Damar Loda Sunayen Yan Takararsu a Shafinta

INEC Ta Dage Ranar ba Jam’iyyu Damar Loda Sunayen Yan Takararsu a Shafinta

  • Hukumar INEC ta ɗaga ranar bai wa jam'iyyun siyasa lambar shiga manhajar gabatar da sunayen 'yan takara
  • INEC ta ce an yi jinkirin ne domin tabbatar da cewa aikin loda takardun tsayar da 'yan takara na zaɓen 2027 zai gudana cikin sauƙi
  • PDP ta riga ta bai wa 'yan takararta takardun shaidar nasara da fom na INEC, tare da umarnin mayar da su cikin sa'o'i 72

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Abuja - Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) ta ɗaga ranar sanya sunayen yan takarar jam'iyyun siyasa a shafinta.

Hukumar zaben ta dage ranar zuwa Litinin, 29 ga Yunin 2026, domin loda sunayen 'yan takarar zaɓen 2027.

INEC ta sauya ranar sanya sunayen yan takara
Shugaban hukumar INEC a Najeriya, Joash Amupitan. Hoto: INEC Nigeria.
Source: Facebook

Jam'iyyu suna jiran ba su dama daga INEC

Wata majiya daga INEC ta ce jam'iyyun sun karɓi fom ɗin da za su cike, amma ba za su iya loda su a manhajar ba sai bayan an ba su damar shiga, cewar Punch.

Kara karanta wannan

Dakarun sojoji sun farmaki 'yan ta'addan Lakurawa a Kebbi, an kashe miyagu

Tun da farko INEC ta shirya fitar da lambar shiga a ranar Juma'a, 26 ga Yuni, amma majiyoyi daga hukumar da jam'iyyun siyasa sun ce an ɗage hakan domin kauce wa matsaloli.

Hukumar ta riga ta raba fom ɗin tsayar da 'yan takara ga jam'iyyun siyasa, abin da ya rage shi ne fitar da lambar shiga domin a loda takardun.

An kuma ruwaito cewa jam'iyyar PDP ta miƙa takardun shaidar nasara ga zaɓaɓɓun 'yan takararta tare da ba su fom na INEC domin cike su.

NDC ta yi korafi game da INEC
Dan takarar shugaban kasa a NDC, Peter Obi da mataimakinsa, Rabiu Kwankwaso. Hoto: Mr Peter Obi.
Source: Twitter

Korafin jam'iyyar NDC kan lamarin

Jam'iyyar NDC ta zargi INEC da ƙin ba ta damar shiga da ake buƙata domin loda sunayen 'yan takararta a manhajar karɓar sunayen 'yan takara ta hukumar.

Wannan na zuwa ne bayan wata kotun tarayya ta ba da umarnin INEC ta cire jam'iyyar NDC daga rajista, hukuncin da ya haifar da rashin tabbas kan matsayin jam'iyyar a doka da kuma damar da take da ita ta shiga zaɓe mai zuwa.

Da yake magana kan lamarin, sakataren yaɗa labarai na ƙasa na jam'iyyar NDC, Osa Director, ya ce jam'iyyar ta tuntuɓi INEC domin samun lambar shiga da ake buƙata don kammala loda sunayen 'yan takararta ta yanar gizo, amma ta kasa samun lambar.

Kara karanta wannan

Bayan hukuncin kotu, NDC ta bayyana makomar takarar Peter Obi da Kwankwaso a zaben 2027

Umarni da aka ba yan takara a jam'iyyu

Haka kuma, an umarci kowane ɗan takara ya mayar da fom ɗinsa cikin sa'o'i 72 domin bai wa jam'iyyar damar fara loda su a manhajar tsayar da 'yan takara ta INEC.

Za a buɗe manhajar ne domin karɓar takardun 'yan takarar shugaban ƙasa da na majalisar dokoki ta ƙasa, inda jam'iyyu za su loda fom EC9 da EC9A-E ta yanar gizo, kamar yadda Arise TV ta ce.

Har yanzu INEC na dakon kasafin kudin zabe

A wani labarin, mun ruwaito cewa Hukumar zaben Najeriya, INEC ta ce har yanzu ba ta karɓi kasafin kuɗin da ta gabatar domin shirya zaɓen 2027 daga gwamnatin tarayya ba.

Ta ce duk da haka shirye-shiryen zaɓen na ci gaba kamar yadda doka ta tanada, yayin da take dakon a tura mata Naira biliyan 873.78.

INEC ta kuma bayyana shirinta na gudanar da zaben gwaji domin tabbatar da ingancin tsarin fasahar da za a yi amfani da shi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com