Traoré, Nijar da Mali Sun Dura kan Tinubu a kan Rashin Tsaron Najeriya

Traoré, Nijar da Mali Sun Dura kan Tinubu a kan Rashin Tsaron Najeriya

  • Burkina Faso, Mali da Niger sun caccaki Shugaban Najeriya, Bola Tinubu, bayan ya alakanta matsalolin tsaron Najeriya da tabarbarewar tsaro a kasashensu
  • Kasashen uku na ƙungiyar AES sun gayyaci jami'in diflomasiyyar Najeriya a Ouagadougou domin nuna rashin amincewarsu da kalaman Tinubu
  • Ministan Harkokin Wajen Burkina Faso, Karamoko Jean-Marie Traoré, ya ce Najeriya da kasashen AES na fuskantar barazanar tsaro iri ɗaya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Abuja – Kasashen Burkina Faso, Mali da Niger sun mayar wa Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu, martani mai zafi bayan ya alakanta tabarbarewar tsaron Najeriya da matsalolin tsaro da ke faruwa a kasashen Sahel.

Kasashen uku na AES sun gayyaci jami'in diflomasiyyar Najeriya mai kula da harkokin ƙasar a Ouagadougou ranar Alhamis, 6 ga Agusta, domin nuna rashin amincewarsu da kalaman shugaban Najeriya.

Kara karanta wannan

Mutuwa ta sake girgiza Najeriya, tsohon antoni janar ya riga mu gidan gaskiya

Shugabannin kasashen AES
Shugabannin kasashen Mali, Birkina Faso da Nijar. Hoto: Getty Images
Source: Twitter

The Cable ta rahoto cewa Tinubu ya yi kalaman ne a ranar 30 ga Yuli yayin da yake magana da wasu sarakunan gargajiya a Najeriya kan matsalolin tsaron da kasar ke fuskanta.

Abin da Tinubu ya ce

Tinubu ya ce kasancewar wasu daga cikin 'yan ta'addan da ke addabar Najeriya ba 'yan Najeriya ba ne, matsalolin tsaro a Mali, Burkina Faso da Niger na ƙara tsananta matsalolin da Najeriya ke fuskanta.

Ya ce:

"Wasu daga cikinsu ['yan ta'addan] ba 'yan Najeriya ba ne. Kun ga, matsalar rashin tsaro a Mali, Burkina Faso da Niger tana ƙara tsananta mana matsalolinmu."
Shugaba Bola Ahmed Tinubu
Shugaban Najeriya a wajen wani taro. Hoto: Bayo Onanuga
Source: Facebook

Martanin Burkina Faso

Ministan Harkokin Wajen Burkina Faso, Karamoko Jean-Marie Traoré, wanda ya yi magana a madadin kasashen AES, ya ce Burkina Faso, Mali, Niger da Najeriya suna fuskantar barazana iri ɗaya.

Africa Business Insider ta wallafa cewa Traoré ya ce:

"Burkina Faso, Mali, Niger da Najeriya suna fuskantar maƙiya iri ɗaya."

Kara karanta wannan

Yadda Tinubu ke tafiya da kafa zuwa ofis da rashin cin abinci saboda aiki

A cewarsa, kasashen AES sun fi son a gabatar da cikakken bayani kan halin da tsaron yankin yake ciki maimakon daura alhakin rikicin da ke da sarkakiya kan kasashen makwabta.

AES na son aiki da Najeriya

Duk da sabuwar takaddamar, Traoré ya ce kasashen AES na son ci gaba da hulɗa da Najeriya wajen yaƙi da matsalar tsaro.

Ya ce kasashen na son a ci gaba da gudanar da "yaƙi na haɗin gwiwa da na bai ɗaya" domin tunkarar matsalar rashin tsaro da ta addabi yankin.

Yadda Tinubu ke cin abinci

A wani labarin, mun ruwaito cewa shugaban NRS, Zacch Adedeji, ya ce Shugaba Bola Tinubu ba ya rayuwar almubazzaranci duk da irin gata da alfarmar da ke tattare da matsayin shugaban ƙasa.

Adedeji ya fadi haka ne yayin amsa tambayoyi kan irin rayuwar 'yan siyasa a lokacin da 'yan Najeriya ke fuskantar matsin tattalin arziki da kuma damuwa kan yadda gwamnati ke kashe kuɗi.

Shugaban NRS ya ce Tinubu kan yi tafiya da ƙafa daga gidansa zuwa ofishinsa, kuma yana amfani da mota ne kawai idan zai tafi filin jirgin sama kuma yana cin abinci sau daya a rana kacal.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng