Bayan Lafta Masu Harajin N6m, 'Yan Bindiga Sun Yi wa Manoma a Kebbi Barazana
- Mazauna wasu daga cikin kauyukan da ke jihar Kebbi sun shiga dimuwa bayan 'yan ta'adda sun kakaba masu harajin miliyoyin nNaira
- Rahotanni sun ce 'yan bindiga sun kakaba harajin Naira miliyan 6 ga mazauna kauyuka uku a jihar Kebbi tare da yi masu barazanar da ta gigita su
- Tuni shugabannin al'umomin da aka yi wa barazanar suka fara neman dauki daga hukumomi da gwamnatin Najeriya domin a shawo kan matsalar
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Kebbi – Rahotanni sun nuna cewa wasu 'yan bindiga sun kakaba harajin N6m ga mazauna kauyuka uku da ke karamar hukumar Danko-Wasagu a jihar Kebbi.
'Yan bindigan da suka sanya mazauna yankunan a cikin fargaba sun kuma kara da yi masu barazana matukar suka gaza biyan wannan haraji.

Kara karanta wannan
Sokoto: Jama'a sun shiga firgici da 'yan bindiga suka kashe limami da wasu mutane

Source: Facebook
Mai sharhi a kan al'amuran tsaro a Arewa maso Yamma, Bakatsine da ta samu bayanai game da kakaba harajin ya wallafa a shafin X cewa 'yan bindigan sun yi barazanar hana manoma shiga gonakinsu idan harajin bai shiga hannunsu ba.
Mazauna Kebbi sun shiga rudani
Shugabannin al'umomi da ke kananan zaune a kauyukan Falfala, Dgolo da Dbebke da ke karamar hukumar Danko-Wasagu a jihar Kebbi sun shiga rudani.
Bakatsine ya wallafa cewa:
"'Yan bindiga sun kakaba harajin Naira miliyan 6 ga mazauna kauyukan Falfala, Dgolo da Dbebke da ke karamar hukumar Danko-Wasagu a jihar Kebbi, tare da gargadin cewa za su hana manoma shiga gonakinsu idan ba a biya kudin ba."
Shugabanni sun fara neman agaji a Kebbi
Rahoton ya ce tuni shugabannin al'ummomin da abin ya shafa suka fara neman agajin gwamnatin jihar Kebbi da hukumomin tsaro domin dakile lamarin tun kafin ya tabbata.
A cewarsa:
"Shugabannin al'umma sun roki gwamnatin jihar Kebbi da hukumomin tsaro da su gaggauta daukar mataki."

Source: Original
Bakatsine ya kara da cewa:
"Lamarin ya nuna karuwar matsin lambar da kungiyoyin masu dauke da makamai ke sanyawa al'ummomin manoma a karkara, lamarin da ke barazana ga hanyoyin samun abin rayuwa, yana kawo cikas ga aikin noma a lokacin damina tare da kara tayar da hankula kan matsalar tsaron abinci a Najeriya."
Rahoton ya kara nuna damuwar da ake ci gaba da yi kan tabarbarewar tsaro a wasu yankunan karkarar jihar Kebbi, musamman a lokacin da manoma ke kokarin fara noman bana.
Sojoji sun hallaka 'yan bindiga a Kebbi
A baya, kun samu labarin cewa dakarun sojojin Najeriya sun samu gagarumar nasara a yakin da suke yi da 'yan ta'addan Lakurawa da suka addabi jama'a musamman mazauna jihar Kebbi da kewaye.
Sojojin na rundunar Operation Fansan Yamma sun samu nasarar hallaka 'yan ta'addan Lakurawa bayan wani dauki ba dadi da aka yi a kokarin da jami'an tsaro ke yi na dawo da zaman lafiya a Arewacin Najeriya.
Jami'in Yaɗa labarai na rundunar, Laftanal Kanal Aliyu Danja, ya bayyana cewa zaratan sojojin sun samu nasarar kwato makamai masu tarin yawa daga hannun hatsabiban 'yan ta'addan da suka hana zaman lafiya a yankin.
Asali: Legit.ng
