Dalilin da Ya Sa Kashim Shettima Ya Tura Gwamnoni 3 Gidan Babban Jigon ADC, Mustapha Inuwa
- Tsohon sakataren gwamnatin Katsina, Dr Mustapha Inuwa ya magana kan ganinds tare da gwamnonin Kaduna, Katsina da Zamfara
- Ya bayyana cewa mataimakik shugaban kasa, Sanata Kashim Shettima ne ya tura su domin neman auren diyarsa ga wani danginsa
- Inuwa ya ce an amince da neman auren kuma an daura auren a ranar, amma duk da haka, ana ganin ziyarar na iya kasancewa da tasirin siyasa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Katsina, Nigeria - Dr Mustapha Inuwa, daya daga cikin jiga-jigan jam'iyyar ADC a jihar Katsina, ya yi karin haske kan ziyarar da gwamnonin Kaduna, Katsina da Zamfara suka kai gidansa.
A wata hira da aka yi da shi, Mustapha Inuwa ya ce Uba Sani, Dikko Umaru Radda da Dauda Lawal sun ziyarce shi ne a madadin Mataimakin Shugaban Kasa, Sanata Kashim Shettima.

Source: Facebook
Daily Trust ta rahoto cewa, Inuwa, tsohon sakataren gwamnatin Katsina ya ce gwamnonin sun je gidansa ne domin neman auren daya daga cikin 'ya'yansa ga wani dangin mataimakin shugaban kasar.
An daura auren nan take
A cewar Mustapha Inuwa, ya amince da bukatar neman auren, sannan aka cimma matsayar daura auren a wannan rana.
Ya ce:
"Mataimakin Shugaban Kasa, Sanata Kashim Shettima ne ya aiko su domin neman auren daya daga cikin 'ya'yana ga wani ɗan danginsa, wannan ne ya kawo su gidana.
"Tun kafin hakan ma mun dade da sanin juna. A lokacin aka bukaci a daura auren nan take, muka amince, kuma yanzu an daura auren."
Ziyarar gwamnonin na da alaka da siyasa?
Jigon na ADC ya jaddada cewa ziyarar gwamnonin na APC mai mulki ba ta da alaka da siyasa kamar yadda wadu ke yadawa.
A baya-bayan nan, Dr Mustapha Inuwa ya zama daga daga cikin jiga-jigan da jam'iyyun siyasa daban-daban a jihar Katsina ke zawarci, musamman bayan rikicin da ya barke a cikin ADC kan tsaida da 'yan takara ta hanyar maslaha.
Kwanan nan, mataimakin gwamnan jihar Katsina ya kai masa ziyara, yayin da rahotanni suka nuna cewa wasu jiga-jigan jam'iyyar PDP ma suna kokarin jawo shi zuwa jam'iyyarsu.

Source: Facebook
Masu sharhi sun hango tasirin siyasa
Sai dai masana harkokin siyasa na ganin ziyarar da gwamnonin APC uku suka kai gidan jigon ADC na iya kasancewa da wata ma'ana ta siyasa fiye da yadda aka bayyana.
A cewarsu, kwanaki masu zuwa ne za su bayyana hakikanin tasirin wannan ganawa tsakanin Mustapha Inuwa da gwamnonin APC.
Shema ya kare Tinubu da Radda
A wani rahoton, kun ji cewa tsohon gwamnan jihar Katsina, Barista Ibrahim Dhehu Shema ya kare matakan tattalin arziki na shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu.
Ya ce duk da cewa wasu daga cikin matakan tattalin arzikin da gwamnatin ta dauka sun jawo wa mutane wahala, amma sun zama dole domin magance matsalolin da suka dade suna addabar Najeriya.
Tsohon gwamnan ya bukaci mambobin APC su kara himma wajen tuntubar jama'a tare da kare manufofin gwamnatin Bola Tinubu da Radda.
Asali: Legit.ng

