An Daure Yar TikTok kan Yada Cewa Shugaban Kasa Ya Kashe Shanu 32 don Cin Zabe

An Daure Yar TikTok kan Yada Cewa Shugaban Kasa Ya Kashe Shanu 32 don Cin Zabe

  • Wata mai amfani da TikTok a Ghana, Camilla Alhassan, ta gamu da hukuncin ɗaurin shekara guda saboda yaɗa labaran ƙarya a Ghana
  • Kotu ta ce hukuncin zai zama darasi ga masu yaɗa ƙarya a kafafen sada zumunta, yayin da lamarin ya sake jawo da muhawara
  • Masu gabatar da ƙara sun ce Alhassan ta wallafa zarge-zargen da ba su da hujja, lamarin da ya ƙara tayar da damuwa kan yaɗuwar bayanan ƙarya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Accra, Ghana - An yankewa wata fitacciyar mai amfani da TikTok a Ghana, Camilla Alhassan, hukuncin ɗaurin shekara guda a gidan yarin Ghana.

Majiyoyi sun ce ana zarginta da wallafa labaran ƙarya da kuma kalaman batanci game da Shugaba John Mahama.

An daure yar TikTok a Ghana
Yar TikTok, Camilla Alhassan da shugaban Ghana, John Mahama. Hoto: @camillaalhassan/officialjdmahama.
Source: Instagram

Rahoton BBC News ya tabbatar da cewa Alhassan ta amsa laifin da ake zarginta da shi na cin mutunci, yada karya da bata sunan shugaban kasa.

Kara karanta wannan

Gaskiya ta fito kan hoton da Messi ke yi wa Yamal wanka a baho

Abin da yar TikTok ta wallafa kan Mahama

A kwanakin baya, Alhassan ta wallafa bidiyoyi tana zargin shugaban ƙasa wai ya yanka shanu 32 domin yin wani tsafi da zai taimaka masa ya lashe zaɓen shugaban ƙasa na shekarar 2024.

Ta kuma yi zargin cewa shirin gwamnati na rabon kayan tsaftar mata masu al'ada ga mutanen da ambaliyar ruwa ta shafa wani yunkuri ne na ɓoye abin da ta ce shugaban ya aikata.

Sai dai masu gabatar da ƙara sun bayyana cewa waɗannan zarge-zarge ba su da tushe.

Alkalin da ya saurari shari'ar ya ƙi roƙon a sassauta mata hukunci, yana mai cewa ɗaurin kurkuku zai zama darasi ga masu irin wannan ɗabi'a, tare da taimakawa wajen rage yaɗuwar bayanan ƙarya a kafafen sada zumunta.

Masu gabatar da ƙara sun bayyana cewa Alhassan, wadda ke da mabiya sama da 70,000 a TikTok, ta yi jerin wallafe-wallafen da suka ƙunshi ƙarya da ɓata suna kan shugaban ƙasa.

Kara karanta wannan

Kotu ta hukunta mutumin da aka kama da laifin ta'addanci

Bidiyoyin nata sun bazu sosai kafin jami'an tsaro su kama ta a farkon wannan watan.

Yar TikTok ya shiga matsala a Ghana
Shugaban kasar Ghana, John Mahama a wurin taro. Hoto: VS Alliance.
Source: Twitter

Yadda hukuncin ya jawo magana a Ghana

Lamarin ya sake tayar da muhawara a Ghana kan yadda za a daidaita yaƙi da yaɗuwar labaran ƙarya a kafafen sada zumunta tare da kare 'yancin faɗar albarkacin baki.

Alkalin ya ce hukuncin ya zama dole saboda ƙaryace-ƙaryace na ƙara yaɗuwa a shafukan sada zumunta.

Ba shi ne karo na farko da aka daure wani fitaccen mai amfani da kafafen sada zumunta a Ghana ba.

A watan Satumban bara, an yankewa fitaccen ɗan TikTok David Kwodwo Prah Afful, wanda aka fi sani da Kwame Nkrumah II, hukuncin ɗaurin watanni bakwai saboda yin barazanar kisa da kuma wallafa saƙonnin da za su iya tayar da tarzoma.

A bara, Shugaba Mahama ya bayyana cewa gwamnatinsa na nazarin hanyoyin tsaftace kafafen sada zumunta, tare da umartar hukumomi su kamo masu yaɗa bayanan ƙarya da na yaudara.

Ministan Sadarwa Samuel Nartey George ma ya sanar da shirin gabatar da dokar da za ta yaƙi irin waɗannan matsaloli tare da kiyaye 'yancin faɗar albarkacin baki.

Kara karanta wannan

Qatar ta ware kwanakin makoki, ta ba da hutun aiki bayan mutuwar tsohon Sarki

Matar tsohon shugaban Ghana ta rasu

An ji cewa kasar Ghana ta yi babban rashin bayan sanar da rasuwar matar tsohon shugaban kasar kuma mai kare haƙƙin mata.

An tabbatar da cewa Nana Konadu Agyeman-Rawlings, ta rasu tana da shekaru 76 bayan gajeriyar rashin lafiya.

Marigayiyar matar Jerry John Rawlings, ta taka muhimmiyar rawa wajen samar da dokokin da suka kare haƙƙin mata da yara a ƙasar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.