Kebbi: Yan Bindiga Sun Bindige Babban Darakta, Sun Sace Matarsa da Malamar Makaranta

Kebbi: Yan Bindiga Sun Bindige Babban Darakta, Sun Sace Matarsa da Malamar Makaranta

  • 'Yan bindiga sun kai hari gidan Daraktan Ma'aikata na karamar hukumar Ngaski, Alhaji Nasiru Muhammed
  • Majiyoyi sun tabbatar da cewa an kai harin ne a Yauri, inda suka harbe shi har lahira da daren ranar Alhamis 16 ga watan Yulin 2026
  • Maharan sun kuma yi garkuwa da matar mamacin tare da wata malama mai suna Maryam, yayin da har yanzu ba a san inda suke ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Kebbi - 'Yan bindiga sun kai wani mummunan hari a jihar Kebbi inda suka kashe wani mutum da kuma garkuwa da matarsa.

Maharan sun kashe Daraktan Ma'aikata na karamar hukumar Ngaski, Alhaji Nasiru Muhammed, bayan sun kai hari gidansa.

Yan bindiga sun kashe babban darakta a Kebbi
Taswirar jihar Kebbi da ke fama da matsalolin tsaro. Hoto: Legit.
Source: Original

Rahoton Bakatsine ya ce an kai harin ne a unguwar Low Cost a karamar hukumar Yauri ta Kebbi da ke fama da hare-haren ƴan bindiga.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun yi ta'asa a Sokoto, an sace 'yan gudun hijira

Yan bindiga sun kashe wani darakta a Kebbi

Rahotanni sun bayyana cewa lamarin ya faru ne a daren Alhamis lokacin da wasu dauke da muggan makamai suka kutsa cikin unguwar suka nufi gidan jami'in.

An ce maharan sun harbe Alhaji Nasiru Muhammed har lahira yayin harin, kamar yadda Sahara Reporters ta bayyana a rahotonta.

Baya ga kashe jami'in, 'yan bindigar sun yi garkuwa da matarsa tare da wata mazauniyar unguwar mai suna Maryam, wadda ke aiki a matsayin malama.

Har zuwa lokacin hada wannan rahoto, ba a san inda matan biyu suke ba, kuma babu wata alaka da aka ce an samu da masu garkuwar.

Lamarin ya jefa al'ummar yankin cikin jimami tare da kara tayar da fargaba saboda yadda hare-haren 'yan bindiga ke ci gaba da karuwa a sassan Kebbi.

Yadda aka sace matar darakta da wata malama

A ranar Juma'a, an tabbatar da cewa Daraktan Ma'aikatan ya rasa ransa a harin, yayin da matarsa da malamar makarantar suka fada hannun maharan.

Kara karanta wannan

Sojoji sun rikata 'yan Boko Haram a kananan hukumomin Borno 5

Ya ce 'yan bindigar sun kai hari gidan Alhaji Nasiru Muhammed, Daraktan Ma'aikata na Ngaski, sannan suka yi garkuwa da matarsa da Maryam, wata malama makwabciya.

Mazauna yankin da abin ya shafa sun bayyana matukar damuwa da wannan hari, suna cewa yawaitar hare-haren 'yan bindiga na ci gaba da razana al'ummominsu.

Ya ce 'yan bindigar sun kai hari gidan Alhaji Nasiru Muhammed, Daraktan Ma'aikata na Ngaski, sannan suka yi garkuwa da matarsa da Maryam, wata malama makwabciya.

Mazauna yankin da abin ya shafa sun bayyana matukar damuwa da wannan hari, suna cewa yawaitar hare-haren 'yan bindiga na ci gaba da razana al'ummominsu.

An kama masu kera makamai ga ƴan ta'adda

Tun farko, kun ji cewa rahotanni sun bayyana cewa dakarun sojojin Najeriya sun tarwatsa wata haramtacciyar cibiyar ƙera makamai a wani yanki na jihar Kebbi.

Yayin da aka kai farmaki masana'anatar, sojoji sun ƙwato bindigogi biyar da aka ƙera a cikin gida masu kama da AK-47 tare da kama mutum biyu.

Jami'an tsaro sun fara ƙarin bincike da samame domin cafke sauran waɗanda ke da hannu a cibiyar da kuma dakile safarar makamai a jihar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.