Iyalan Budurwar da Aka Tsinci Gawarta a gidan Ministan Tinubu Sun Kai Korafi gaban IGP
- Iyalan Mary Habila, ma'aikaciyar jinyar da ta rasu a gidan ministan ayyuka, David Umahi sun shigar ga korafi gaban Sufeto Janar na 'Yan Sanda
- A korafin sun kai karar kwamishinan yan sandan jihar Ebonhi, sannan sun bukaci a ba su gawar diyarsu domin gudanar da jana'izarta
- Mahaifin marigayiyar ya ce ba ya zargin an kashe diyarsa kuma bai kamata a siyasantar da mutuwarta ba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja, Nigeria - Iyalan Mary Habila, ma'aikaciyar jinya mai shekara 26 da aka tsinta a mace a gidan Ministan Ayyuka, David Umahi, da ke Uburu a jihar Ebonyi, sun mika koke ga Sufeto Janar na 'Yan Sanda, Olatunji Disu.
Iyalan marigayiyar sun bukaci shugaban rundunar yan sandan Najeriya ya ba da umarnin a ba su gawarta domin gudanar da jana'izarta.

Source: Facebook
Daily Trust ta rahoto cewa hakan na cikin koken da suka gabatar a hedkwatar rundunar 'yan sanda da ke Abuja ranar Juma'a, 17 ga watan Yulin 2026.
Iyalan sun yi barazanar gurfanar da Kwamishinan 'Yan Sandan jihar Ebonyi a kotu saboda ci gaba da rike gawar duk da bukatar da suka gabatar na a mika musu ita.
Sun ki amincewa da gwajin gawa
Da yake magana a madadin iyalan, lauyansu, Kaile Adamu Yusuf, ya ce iyalan ba su amince da yin gwajin gawa ba saboda dalilan addini da al'ada.
Ya kuma yi korafin cewa mutuwar Mary ta koma abin siyasa, inda wasu ke yi mata kazafi ta hanyar kiran ta da sunaye marasa kyau.
Lauyan ya ce:
"Mary Habila ba kwararriyar ilimin motsa jiki ba ce, ma'aikaciyar jinya ce. Ta yi aiki a Jami'ar Kiwon Lafiya ta David Umahi kafin a tura ta ofishin ministan, inda ta shafe kusan shekara uku tana aiki."
Iyalan Mary Habila sun koka
Yusuf ya ce duk da cewa iyalan sun bi dukkan matakan da doka ta tanada domin karbar gawar, har yanzu ba a mika musu ita ba.
Ya ce:
"Da alama wasu suna son amfani da lamarin wajen cimma muradunsu na siyasa maimakon a bar iyalan su binne diyarsu cikin mutunci."
Mahaifinta ya nemi a birne ta
A nasa bangaren, mahaifin marigayiyar, Tanko Habila Wisdom, ya roki jami'an 'yan sanda su sako gawar diyarsa domin su yi mata jana'iza.
Ya ce ba ya zargin kowa da hannu a mutuwarta, yana mai cewa mutuwa na iya riski kowa a kowane lokaci, kamar yadda Vanguard ta ruwaito.

Source: Twitter
A cewarsa:
"Abin da nake nema shi ne a ba ni gawar diyata domin na je na birne ta. Ba ma son a yi wannan gwajin gawa, kuma ba na zargin kowa saboda mutuwa na iya zuwa a kowane lokaci."
Umahi ya yi magana kan Mary Habila
Kun ji cewa ministan ayyuka, David Umahi ya yi magana kan mutuwar wata ma'aikaciyar jinya da ke aiki tare d shi na tsawon shekaru, a gidansa na jihar Ebonyi.
Umahi ya ce ba ya zargin an aikata wani laifi kan marigayiyar, yana mai cewa kokarin alakanta shi da lamarin siyasa ce da ta wuce gona da iri.
Asali: Legit.ng


