Ekiti: Zaben Gwamna Ya Zo da Zafinsa, an Kona Ofishin Yan Sanda Kurmus
- Tsohon gwamnan Ekiti, Kayode Fayemi, ya yi magana game da kona ofishin ‘yan sanda yayin da ake zaben gwamna a jihar
- Fayemi ya yaba wa INEC kan yadda tantance masu kaɗa ƙuri’a ta gudana cikin sauƙi da tsari, tare da bayyana aikin a matsayin nasara
- Ya buƙaci mazauna Ekiti su ci gaba da zaman lafiya, yana mai cewa al’ummar Isan-Ekiti masu son zaman lafiya ne duk da abin da ya faru
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Ekiti - Tsohon gwamnan Ekiti, Kayode Fayemi, ya yi Allah-wadai da kona wani ofishin ‘yan sanda da aka yi a garinsu.
Majiyoyi sun tabbatar da cewa lamarin ya faru ne garinsu na Isan-Ekiti, yana mai bayyana lamarin a matsayin abin takaici.

Source: Facebook
Da yake zantawa da ‘yan jarida bayan ya kaɗa ƙuri’arsa, Fayemi ya ce lamarin ba shi da wata alaƙa da zaɓen gwamna da ke gudana, cewar Leadership.
Ekiti 2026: Fayemi ya yaba wa hukumar zabe
Ya yaba wa Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Kasa, INEC saboda yadda ta tantance masu zaɓe cikin sauri da tsari.
Kayode Fayemi ya ce ya kamata a yaba wa jami’an INEC da suka gudanar da aikin saboda yadda suka tabbatar da komai ya tafi cikin sauƙi.
A cewarsa, tsarin kaɗa ƙuri’a ya fi inganci idan aka kwatanta da wasu zaɓukan da suka gabata a jihar duba yadda mutane suka ba da hadin kai.
Ya ce:
“Komai ya gudana yadda ya kamata. Tantance masu zaɓe ta kasance cikin sauri kuma ba tare da wata matsala ba, haka ma na gani ga matata.”
Ya ce ba a saba ganin komai yana tafiya cikin wannan sauƙi ba, musamman ta fuskar fasaha, wanda ya nuna an shirya aikin yadda ya kamata.

Source: Twitter
Tsohon gwamna ya yaba wa masu zabe a Ekiti
Tsohon gwamnan ya kuma yaba wa masu zaɓe saboda yadda suka kiyaye doka da oda duk da matsalar tsaro da aka samu a yankin a daren jajibirin zaɓe.
Ya ce abin da ya faru a daren da ya gabata abin takaici ne, amma ba shi da alaƙa da siyasa ko zaɓen da ake gudanarwa, cewar rahoton TheCable.
Fayemi ya yi gargadin cewa mutane su guji yin hasashe marasa tushe kan lamarin, domin faruwarsa a ranar zaɓe na iya haifar da jita-jita da za su kawo matsala.
Fada ya kaure tsakanin 'yan APC da ADC
Mun ba ku labarin cewa an samu hatsaniya tsakanin magoya bayan jam'iyyun APC da ADC a wata rumfar zaɓe a Ilawe Ekiti kan zargin sayen ƙuri'u.
'Dan takarar gwamnan ADC, Dare Bejide, ya yi zargin cewa an kawo kuɗi domin rabawa masu zaɓe amma aka hana hakan.
Rikicin ya jikkata wani magoyin bayan jam'iyyar ADC, wanda aka garzaya da shi asibiti domin samun kulawar likitoci kamar yadda ya dace.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

