Ekiti 2026: Rigima Mai Zafi Ta Kaure tsakanin Magoya Bayan APC da ADC bayan An Jibge Kudi

Ekiti 2026: Rigima Mai Zafi Ta Kaure tsakanin Magoya Bayan APC da ADC bayan An Jibge Kudi

  • An samu cacar baki tsakanin magoya bayan jam'iyyun APC da ADC a wata rumfar zaɓe a Ilawe Ekiti kan zargin sayen ƙuri'u
  • Ɗan takarar gwamnan ADC, Dare Bejide, ya yi zargin cewa an kawo kuɗi domin rabawa masu zaɓe amma aka hana hakan
  • Rikicin ya jikkata wani magoyin bayan jam'iyyar ADC, wanda aka garzaya da shi asibiti domin samun kulawar likitoci

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Ekiti, Nigeria - An samu tashin hankali a rumfa ta 4, gunduma ta 2 da ke Ilawe Ekiti yayin zaɓen gwamnan jihar Ekiti da ke gudana yau Asabar, 20 ga watan Yuni, 2026.

Rigima ta kauce a rumfar zaben ne bayan da magoya bayan jam’iyyar APC da ADC sun shiga cacar baki kan zargin sayen ƙuri'u.

Jihar Ekiti.
Taswirar jihar Ekiti da ke Kudancin Najeriya Hoto: Legit.ng
Source: Original

Punch ta rahoto cewa ɗan takarar gwamna na ADC, Mista Dare Bejide, wanda ya kada ƙuri’arsa a rumfar, ya yi zargin cewa wasu ‘yan siyasa sun kawo kuɗi masu yawa domin rabawa masu zaɓe, amma aka dakile yunkurin.

Kara karanta wannan

'Za ta karewa Tinubu a 2027,' Momodu ya fadi yadda Atiku zai kifar da APC

Bejide ya kuma yi zargin cewa wani jigo na APC ya iso wurin a cikin mota kirar Toyota Jeep dauke da kuɗi masu yawa, inda ake zargin yana shirin rabawa masu zaɓe a wani wuri da ke kusa da rumfar zaɓen.

A cewarsa, wannan ne ya haddasa gardama da rikici tsakanin bangarorin biyu, wanda har ya kai ga doke-doke.

An jikkata magoyin bayan ADC

Rahotanni sun nun cewa wani daga cikin magoya bayan ADC ya samu rauni a kai yayin rikicin, inda aka garzaya da shi asibiti domin samun kulawar likitoci.

Da yake magana kan lamarin, Bejide ya ce:

"Kun ji sautin da aka ɗauka daga rigimar, daya daga cikinsu ta kawo kuɗi a cikin buhu, amma muka tare ta. Daga nan sai ta kira shugaban ƙaramar hukuma, shi ma ya zo wurin."

Ya ce APC ta yi ƙoƙarin kare kanta ta hanyar zargin wasu mambobin ADC da rabon kuɗi, amma ba su iya ambaton ko mutum guda ba, kamar yadda The Nation ta rahoto.

"Mun san inda aka ajiye kuɗin, kuma a lokacin da suka yi ƙoƙarin kwashe kuɗin ne hayaniya da rikici suka barke a wurin," in ji shi.

Kara karanta wannan

Jerin jihohin da APC, APGA da sauran jam'iyyu ke mulki gabanin zaben gwamnan Ekiti

Bejide.
Shugaban ADC na kasa, David Mark tare da dan takarar gwamnan jam'iyyar a zaben Ekiti, Dare Bejide Hoto: ADC Party
Source: Twitter

Bejide ya yaba wa hukumar INEC

Sai dai duk da zargin da ya yi, Bejide ya yaba wa Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) kan yadda take gudanar da zaɓen.

"Jami'an zaɓe suna aiki yadda ya kamata kuma komai na tafiya lafiya. Kafin ku zo akwai tashin hankali a nan, amma da suka ga kun zo da kyamara sai suka tsere," in ji shi.

'Yan sanda sun shiryawa zaben Ekiti

Kun ji cewa Rundunar ‘yan sandan Najeriya ta gargadi masu shirin karya dokokin zabe a Ekiti, tana mai cewa za a hukunta duk wanda ya sabawa doka.

Rundunar ta bukaci masu kada kuri’a da sauran masu ruwa da tsaki su kasance masu bin doka tare da gudanar da harkokinsu cikin kwanciyar hankali a lokacin zaben.

Kwamishinan ‘yan sanda mai kula da tsaron zabe, Shogule Abayomi, ya ce an samar da wani tsari mai karfi na tsaro domin tabbatar da zaben.ya kasance cikin lumana, gaskiya da inganci.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262