Wata Sabuwa: Kwankwaso Ya Yi Barazanar Ficewa daga NDC, an Ji Dalili

Wata Sabuwa: Kwankwaso Ya Yi Barazanar Ficewa daga NDC, an Ji Dalili

  • Bisa ga dukkan alamu abubuwa na neman tabarbarewa tsakanin Sanata Rabiu Musa Kwankwaso da shugabannin NDC a Kano
  • An ruwaito cewa shugabannin na NDC sun sauya sunaye wasu 'yan takara na Kwankwasiyya domin mutunta yarjejeniyar da aka yi
  • Sai dai, alamu sun nuna hakan bai yi wa madugun Kwankwasiyya dadi ba, inda ya yi baranazar raba gari da jam'iyyar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Kano - An ruwaito cewa tsohon gwamnan Jihar Kano, Rabiu Musa Kwankwaso, ya yi barazanar barin jam'iyyar NDC.

Kwankwaso ya yi barazanar ne bayan da jam'iyyar ta canza manyan 'yan takara na ɓangaren kungiyar Kwankwasiyya a Kano domin tabbatar da tsarin raba madafun iko na 60/40 da aka amince da shi tun da farko, wanda ya ba wa ɓangarensa kaso 60.

Kara karanta wannan

Sabuwar rigima ta barke tsakanin Kwankwaso da shugabannin jam'iyyar NDC

Kwankwaso ya yi barazanar rabuwa da NDC
Madugun Kwankwasiyya, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso Hoto: Hon. Saifullahi Hassan
Source: Facebook

Jam'iyyar NDC ta canza 'yan takara da dama da ɓangaren Kwankwasiyya ya gabatar da farko a Jihar Kano saboda zargin taka yarjejeniyar raba madafun iko, kamar yaddda wani rahoto na jaridar The Guardian ya bayyana.

An sauya sunayen 'yan Kwankwasiyya

Sauya 'yan takarar na kunshe ne a cikin wata takarda da shugaban NDC na jihar Kano, Hon. Hussaini Isah Mairiga ya sanya wa hannu, rahoton Daily Post ya nuna hakan.

Mairiga ya ce an gudanar da canje-canjen ne domin nuna yarjejeniyar da aka yi tun da farko a kan rarraba muƙaman jam'iyya da tikitin takarar zaɓe tsakanin asalin tsarin NDC da ke jihar da kuma ɓangaren Kwankwasiyya.

An aika wa jagoran jam'iyyar ta hamayya na kasa, Sanata Seriake Dickson, Kwankwaso, da kuma shugaban NDC na shiyyar Arewa maso Yamma kwafin wannan takarda.

Kara karanta wannan

Tafiyar Atiku ta shiga matsala a Gombe, 'yan ADC sun koma APC da PDP

Sababbin sunayen da aka kawo

A ƙarkashin sabon jerin sunayen da aka gyara, jam'iyyar ta amince da waɗannan mutane na mazaɓun tarayya: Barista Isma’il Idris Sani (Kumbotso), Nasiru Ali Ahmed (Nassarawa) Kabiru Ishaq Sa’id (Kano Municipal).

Sauran su ne Barista Dayyabu Jamilu Ibrahim (Doguwa/Tudun Wada), Muhammad Hamisu Abubakar (Dawakin Tofa/Rimin Gado/Tofa), Ibrahim Bashir Bango (Sumaila/Takai) da kuma Abdulmajid Isa Umar Mairigar Fata (Gwale).

An kuma gudanar da gyare-gyare a kan tikitin takarar Majalisar dokoki ta jihar Kano a mazaɓun Dala, Tarauni, Kumbotso, Ungogo, da kuma Dawakin Kudu.

Kara karanta wannan

Atiku ya zayyano kurakuran gwamnatin Tinubu kan rashin tsaro "ta ki daukar darasi"

Kwankwaso bai ji dadin canza sunayen 'yan Kwankwasiyya ba
Dan takarar mataimakin shugaban kasa na NDC a zaben 2027, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso Hoto: Hon. Saifullahi Hassan
Source: Facebook

A cewar NDC, akwai tsayayyiyar yarjejeniya na cewa za a raba muƙaman zaɓe da na ofisoshin jam'iyya a kan tsarin kashi 60 da kashi 40, inda ɓangaren Kwankwasiyya zai karɓi kashi 60 yayin da asalin tsarin jam'iyyar zai riƙe kashi 40.

NDC: An kai karar jam'iyyarsu Kwankwaso

A wani labarin kuma, kun ji cewa an shigar da kara gaban kotu domin neman soke rajistar jam'iyyar NDC mai adawa a Najeriya.

An shigar da karar ne ta hannun mukaddashin shugaban tsare-tsare na kungiyar ADA, Ahidjo Karlahi, inda yake neman hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) ta soke rajistar NDC.

A cikin takardar karar da Ahidjo Karlahi ya gabatar, ya ce NDC ba ta cika sharudan kundin tsarin mulki da dokokin zabe suka tanada ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng