Kwankwaso Ya Yaba Wa Tinubu game da Gagarumin Aikin N46bn a Kano

Kwankwaso Ya Yaba Wa Tinubu game da Gagarumin Aikin N46bn a Kano

  • Jigo a APC Kano, Iliyasu Musa Kwankwaso, ya yabawa Shugaba Bola Tinubu bisa kokarin da yake yi a jihar
  • Kwankwaso ya ce hakan zai ƙarfafa tattalin arzikin Arewa, ya bunƙasa kasuwanci, sannan ya buƙaci al'umma su rika yaba ayyukansa
  • Ministan Sufurin Jiragen Sama Festus Keyamo ya ce an saki kusan kashi 60 cikin ɗari na kuɗin ayyuka a Kano

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Kano - Jigo a jam'iyyar APC a Kano, Alhaji Iliyasu Musa Kwankwaso, ya yabawa Shugaba Bola Ahmed Tinubu kan kokarin da yake yi a Kano.

Ilyasu Kwankwaso ya yaba Tinubu ne bisa amincewar gwamnatin tarayya da kashe naira biliyan 46 domin sake shimfiɗa da gyaran titin saukar jirage na biyu a Filin Jirgin Sama na Mallam Aminu Kano.

Ilyasu Kwankwaso ya yaba wa Tinubu
Shugaba Bola Tinubu da jigon APC, Musa Ilyasu Kwankwaso. Hoto: Asiwaju Bola Tinubu.
Source: Facebook

Ilyasu Kwankwaso ya yabawa Tinubu

Kara karanta wannan

Fadar shugaban kasa na neman hada Obi fada da ƙabilarsa, ta fadi yadda zai cutar da su

Kwankwaso, wanda kuma shi ne Daraktan Kuɗi na Hukumar Raya Kogin Hadejia Jama'are, ya bayyana hakan a Kano yayin da yake martani kan amincewar da aka ba aikin, cewar Tribune.

Ya ce wannan mataki ya nuna irin ƙudirin Shugaba Tinubu na bunƙasa Arewa da tattalin arzikinta, yana mai cewa aikin zai ƙara haɓaka harkokin kasuwanci a faɗin yankin.

A cewarsa, ya dace al'ummar Arewa su nuna godiya ga wannan mataki na shugaban ƙasa ba tare da la'akari da bambancin ra'ayin siyasa ba.

Ya ce amincewa da naira biliyan 46 domin gyaran titin saukar jiragen alama ce cewa Shugaba Bola Ahmed Tinubu yana kaunar Arewa kuma yana son ganin yankin ya ci gaba.

Kwankwaso ya buƙaci mazauna yankin su riƙa yabawa kyawawan ayyukan gwamnati maimakon mayar da hankali kan abubuwan da ba su gamsar da su ba kaɗai.

Har ila yau, ya yabawa Shugaba Tinubu, Abdullahi Umar Ganduje, Ministan Sufurin Jiragen Sama da Raya Sararin Samaniya Festus Keyamo, da shugaban Kwamitin Kasafin Kuɗi na Majalisar Wakilai Abubakar Kabir Abubakar Bichi, tare da sauran waɗanda suka taimaka wajen samun amincewar aikin.

Kara karanta wannan

'Yan APC sun yi wa Peter Obi rubdugu da ya tabo Bola Tinubu

Ya bayyana kwarin gwiwar cewa gyaran titin saukar jirage na biyu zai dawo da martabar filin jirgin Kano a matsayin babbar ƙofar tattalin arzikin Arewacin Najeriya.

Tinubu ya sha yabo kan ayyukan alheri a Kano
Shugaba Bola Tinubu na Najeriya. Hoto: Asiwaju Bola Tinubu.
Source: Facebook

Rokon Kwankwaso ga al'ummar Arewa

Kwankwaso ya kuma roƙi masu ruwa da tsaki a Arewa, ciki har da masu riƙe da sarautun gargajiya da na addini, su yaba da aikin tare da ƙarfafa goyon baya ga shugabannin da ke aiwatar da ayyukan ci gaba.

A lokacin ƙaddamar da sabon sashen jiragen cikin gida na Muhammadu Adamu Dankabo da aka gyara, Minista Festus Keyamo ya sanar da amincewar aikin.

A cewarsa, an riga an fitar da kusan kashi 60 cikin ɗari na kuɗin kwangilar, yayin da ɗan kwangilar ya isa wurin domin fara aikin.

Keyamo ya ce gyaran titin saukar jiragen wani ɓangare ne na shirin gwamnatin tarayya na sabunta filin jirgin Kano da ƙarfafa matsayinsa a matsayin muhimmin cibiyar sufurin jiragen sama da kasuwanci a Arewacin Najeriya.

Ilyasu Kwankwaso ya yaba ayyukan Tinubu a Arewa

An ji cewa Musa Iliyasu Kwankwaso ya ce ayyukan da Gwamnatin Tinubu ke yi a Arewa ne ya sa manyan yan siyasa ke tururuwar komawa APC.

Kara karanta wannan

Kai mutane Hajji, taimakon almajirai da ayyukan Peter Obi a Arewa

Tsohon kwamishinan na Kano ya jero wasu manyan ayyuka da Tinubu ya fara aiwatarwa a Kano da wasu jihohi a Arewacin Najeriya.

Musa Kwankwaso ya bayyana cewa akwai manyan yan siyasa da za su baro jam'iyyun adawa, su koma APC daga nan zuwa karshen 2025.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.