NDC Ta Ce An Samu Kura Kurai a Zaben Fitar da Gwani, Ta Nemi Afuwa
- Jagoran NDC na kasa, Henry Seriake Dickson ya amince cewa an samu wasu kura-kurai a zaɓukan fitar da gwani a jam'iyyar
- Ya ce jam’iyyar tana fuskantar ƙalubale ne saboda ƙarancin lokacin da aka ba ta duk da kasancewarta sabuwa da za ta fafata a 2027
- Henry Seriake Dickson ya tabbatar da cewa babu wanda aka sanar a hukumance a matsayin wanda ya yi nasara a zaɓukan fitar da gwani
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
FCT Abuja – Jagoran jam’iyyar NDC na ƙasa, Henry Seriake Dickson, ya jajanta wa masu neman takara da suka shiga zaɓukan fitar da gwani na jam’iyyar da aka kammala kwanan nan.
Jagoran jam'iyyar ya kuma tabbatar da cewa an samu wasu matsaloli da kura-kurai a yayin gudanar da zaɓukan.

Source: Facebook
Rahoton jaridar Punch ya bayyana cewa Seriake Dickson ya ce duk da cewa zaɓukan ba su gudana yadda aka so ba, ya kama yan jam’iyyar su yi haƙuri.
Jam'iyyar NDC ta ba 'yayanta hakuri
Daily Post ta kawo labarin cewa Seriake Dickson ya shaidawa 'yan jam'iyya cewa NDC na ƙoƙarin shawo kan ƙalubalen da ke tattare halin da ake ciki a yanzu.
Ya bayyana tausayinsa ga masu neman takara a cikin jam'iyyar da ba su samu abin da suka nema ba, tare da cewa har yanzu ana tare.
A cewarsa, irin waɗannan matsaloli ba sabon abu ba ne ga NDC kaɗai, domin hatta manyan jam’iyyun siyasa da suka daɗe suna aiki sun taɓa fuskantar makamantan ƙorafe-ƙorafe a lokuta daban-daban.

Source: Twitter
Dickson ya ce jam’iyyar NDC tana da watanni huɗu kacal da kafuwa, amma cikin ɗan gajeren lokaci ta gudanar da rajistar mambobi da tarukan jam’iyya daga matakin jiha zuwa babban taron ƙasa.

Kara karanta wannan
"Me kuma suke so"; Ana neman tunzura jagoran NDC kan tikitin Obi da Kwankwaso a 2027
Haka kuma a cikin wannan dan kankanin lokaci, an gudanar da zaɓukan fitar da gwani, sauraron ƙorafe-ƙorafe da kuma matakan sulhu.
Ana sulhu a NDC, cewar Dickson
Tsohon gwamnan jihar Bayelsa ya danganta yawancin korafe-korafen da aka samu da tsarin zaɓen kai tsaye da dokar zaɓe ta tanada.
Duk da koke-koken da wasu masu neman takara suka yi, Dickson ya bayyana cewa NDC ta yi abin a yaba da shi idan aka yi la’akari da ƙarancin shekarunta da kuma yawan masu neman takara da ta gudanar da harkokinsu.
Har ila yau, ya yi watsi da rahotannin da ke yawo a kafafen sada zumunta da ke cewa an riga an fitar da sunayen waɗanda suka yi nasara a zaɓukan fitar da gwani.
Ya ce babu wata jam’iyya da ta sanar da sakamakon ƙarshe na zaɓukanta, don haka ya buƙaci jama’a su yi watsi da irin waɗannan rahotanni har sai an fitar da bayanai a hukumance.
Dalilin rikicin NDC da ƴan adawa – Masani
Dr. Sa’idu Ahmad Dukawa, mai sharhi a kan al'amuran tsaro ya ce rikicin da ya dabaibaye jam’iyyar NDC n da alaƙa da canji a siyasar Najeriya gabanin zaɓen 2027.

Kara karanta wannan
"Suna da amfani": Jagoran NDC ya fadi makomar Kwankwasiyya da Obidents a jam'iyyar
Ya shaida wa majiyar Legit cewa daga cikin abubuwan da suka haddasa matsalolin cikin gida da ke addabar NDC shi ne yadda gwamnatin Bola Ahmed Tinubu ke ƙoƙarin raunana jam’iyyun adawa domin rage musu ƙarfi a fagen siyasa.
Dr. Dukawa ya ce ana ƙoƙarin tabbatar da cewa babu wata babbar jam’iyyar adawa da za ta iya yin gogayya mai ƙarfi da jam’iyyar APC a zaɓe mai zuwa.
Manyan NDC sun gana da Kwankwaso
A baya, mun wallafa cewa jagoran NDC na kasa, Henry Seriake Dickson, ya gana da madugun Kwankwasiyya, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso da wasu manyan jiga-jigan jam'iyyar.
Sanata Seriake Dickson ya nuna cewa ya gana da jiga-jigan ne domin dinke barakar da ta taso a jam'iyyar mai adawa a Najeriya bayan an fara samun musayar yawu a kan fitar da yan takara.
Jagoran na NDC ya bayyana cewa kungiyoyin Kwankwasiyya da Obidients suna da rawar da za su taka a cikin sabuwar jam'iyyar, sannan za a ci gaba da kokarin aiki tare wajen ci gabanta.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
