'Lokaci na Kure wa': Jigon APC Ya Nemi Kwankwaso Ya Dawo 'Gida'
- Jigon APC a jihar Kano, Fa'izu Alfindiki, ya buƙaci Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya hakura da jam'iyyar adawa ta NDC
- Ya ce rikicin da ya biyo bayan zaɓen fitar da gwani na NDC ya nuna akwai rarrabuwar kai a jam'iyyar kuma ba zai haifar da 'da mai ido ba
- Fa'izu Alfindiki ya yi ikirarin cewa akwai mafita matukar Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso yi amfani da kwarewa da hangen nesansa a siyasa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Kano – Wani jigo a jam'iyyar APC, Faizu Alfindiki, ya yi kira ga tsohon gwamnan jihar Kano, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, da ya hakura da NDC.
Ya bayyana haka ne bayan an fara samun rahotannin cewa akwai baraka a cikin jam'iyyar adawa musamman bayan an kammala zaben fitar da gwani.

Source: Twitter
Independent News ta kawo labarin cewa Fa'izu Alfindiki na ganin yanzu ne lokacin da Kwankwaso zai yi amfani da kwarewa da hangen nesansa a siyasa.
Jigon APC ya shawarci Kwankwaso
A cikin wata sanarwa da ya fitar a jihar Kano, Fa'izu Alfindiki ya bayyana cewa APC ce ta rage wa Kwankwaso a matsayin jam'iyyar da zai yi tasiri gabanin zaben 2027.
Ya ce cece-kucen da suka dabaibaye zaɓen fitar da gwani a NDC sun sa tilas Kwankwaso ya sake nazarin makomarsa ta siyasa.
A cewar Fa'izu Alfindiki:
"Ya kamata Sanata Kwankwaso ya koma APC kafin lokaci ya kure. Siyasa tana sauyawa, kuma shugabanni masu hikima sun san lokacin da ya dace su sake duba matakansu domin amfanin al'umma."
An nemi Kwankwas ya koma APC
Alfindiki ya bayyana cewa sauya-sauyen jam'iyyun siyasa da Kwankwaso ya yi a baya bai samar masa da sakamakon da ake tsammani ba, kuma hakan ya raunana tsarin siyasar da ya taba ginawa.

Source: Facebook
Ya ce:
"Hakikanin halin da ake ciki a yau ya bambanta da na shekarun baya. Yanayin siyasa ya sauya, kuma alamu sun nuna cewa yana buƙatar sabuwar dabara idan yana son ci gaba da kasancewa mai tasiri a siyasar ƙasa."
Har ila yau, ya yi ikirarin cewa haɗakar siyasar Kwankwaso da Peter Obi ba ta samu karɓuwa daga mutane da dama a Arewa ba.
A cewarsa, wannan haɗakar ta haifar da shakku a tsakanin wasu daga cikin magoya bayan Kwankwaso na asali tare da rage masa farin jini a yankin.
Jigon APC ɗin ya bayyana APC a matsayin gida na siyasa da Kwankwaso ya sani, yana mai cewa da dama daga cikin tsofaffin abokansa da abokan tafiyarsa sun riga sun shiga jam'iyyar.
Ya ce:
"Har yanzu muna kallonsa a matsayin ɗaya daga cikinmu. Da yawa daga cikin abokansa da abokan siyasarsa suna APC. Ƙofar jam'iyyar ba a rufe take a gare shi ba."

Kara karanta wannan
Wata sabuwa: Kwankwaso ya yi barazanar ficewa daga NDC, an ji dalilin fusatar Madugu
Kwankwaso ba zai bar NDC ba - Kwankwasiyya
A baya, kun samu labarin cewa kungiyar Kwankwasiyya ta yi martani ga rahotannin da ke cewa Sanata Rabiu Musa Kwankwaso na son barin NDC saboda an samu sabani.
Mai magana da yawun kungiyar na kasa, Habibu Sale Mohammed, ya bayyana cewa zuwa yanzu, Kwankwaso bai mika wani koke ga uwar jam'iyya kan zaben fitar da gwani ba.
Ya ce an gudanar da zaɓen fitar da gwani bisa doka kuma akwai kuskure a rahoton da ake yada wa kan zargin akwai baraka, tare da jaddada cewa NDC ya fi cancanta ta yi karin haske.
Asali: Legit.ng

