Rikicin NDC na Kara Kamari, Dickson Ya Ce Ya Fi Obi da Kwankwaso Cancanta da Takara a 2027

Rikicin NDC na Kara Kamari, Dickson Ya Ce Ya Fi Obi da Kwankwaso Cancanta da Takara a 2027

  • Jagoran jam'iyyar NDC, Seriake Dickson, ya ce babu dan siyasar da ya fi shi cancantar takarar shugaban kasa a zaben 2027
  • Tsohon gwamnan na Bayelsa ya ce ya zabi kada ya tsaya takarar shugaban kasa duk da gogewa da kwarewar da yake da ita
  • Sanata Dickson mai wakiltar Bayelsa ta Yamma ya jaddada cewa Peter Obi da Rabiu Kwankwaso ba su yi wa NDC wata alfarma ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja, Nigeria - Jagoran NDC kuma sanata mai wakiltar Bayelsa ta Yamma, Seriake Dickson, ya bayyana cewa babu wani 'dan siyasa da ya fi shi cancantar tsayawa takarar shugaban kasa a Najeriya.

Tsohon gwamnan na jihar Bayelsa ya ce ya yanke shawarar kada ya shiga takarar duk da irin gogewa da cancantar da yake da ita.

Seriake Dickson.
Jagoran NDC na kasa kuma Sanata mai wakiltar Bayelsa ta Yamma, Seriake Dickson Hoto: Henry Seriake Dickson
Source: Facebook

Sanata Dickson ya bayyana haka ne a wata hira da ya yi da gidan talabijin na Arise TV a shirin Prime Time.

Kara karanta wannan

"Suna da amfani": Jagoran NDC ya fadi makomar Kwankwasiyya da Obidents a jam'iyyar

Seriake Dickson ya ce ya fi kowa cancanta

Da yake mayar da martani kan ra'ayin cewa Peter Obi da Rabiu Musa Kwankwaso ne suka kara wa NDC karfi bayan sun shiga jam'iyyar, Dickson ya ce:

"Ni ma zan iya tsayawa takara. Babu wanda ya fi ni cancanta. Babu wanda ya fi ni cancantar zama dan takarar shugaban kasa. Babu ko daya."

Tsohon gwamnan ya ce ya zabi kada ya tsaya takarar ne saboda wasu dalilai na kansa, amma ba wai don an fi shi cancanta ba.

Babu wanda ya yi wa NDC alfarma

Sanata Dickson ya jaddada cewa NDC ba ta dogara da wani mutum guda domin samun karbuwa a siyasa ba.

"Kada a nuna kamar wani ne yake yi wa NDC alfarma. A maimakon haka, NDC da mu shugabanninta ne muka samar wa mutane dandamali," in ji shi.

Dickson ya ce duk wanda ke goyon bayan Peter Obi ko Kwankwaso dole ne ya mutunta jam'iyyar da shugabanninta, kamar yadda The Cable ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Jigon ADC ya tona bakar magana da Obi ya fada game da Atiku a sirrance

Ya bayyana cewa ba daidai ba ne mutum ya ce yana goyon bayan wani dan takara amma yana zagin jam'iyyar da ta ba shi dama.

"Ba za ka ce kana goyon bayan Peter Obi ba sannan kana cin mutuncina ko na shugabancin jam'iyyar ba."
Seriake Dickson.
Sanata Seriake Dickson yana jawabi a taron NEC na jam'iyyar NDC a Abuja Hoto: Henry Seriake Dickson
Source: Facebook

Yadda NDC ta karbi manyan jiga-jigai

Dickson ya ce tun kafin Peter Obi da Kwankwaso su shiga NDC, mutane daga sassa daban-daban na Najeriya suna ta shiga jam'iyyar.

Ya bayyana cewa ya karbi fitattun 'yan siyasa da dama ciki har da Sanata Kabiru Marafa daga Zamfara da Aishatu Binani daga Adamawa, tare da wasu da dama daga fadin kasar nan.

A karshe, Dickson ya gargadi magoya bayan kungiyar Obidient da Kwankwasiyya cewa idan suka ci gaba da sukar NDC ko raina jam'iyyar, hakan zai iya rage damar samun nasarar tikitin shugaban kasa a zaben 2027.

Sanata Dickson ya gana da Kwankwaso

A wanu labarin, kun ji cewa jagoran NDC na kasa, Seriake Dickson, ya gana da madugun Kwankwasiyya, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso da wasu manyan jiga-jigan jam'iyyar.

Kara karanta wannan

'Haka aka yi wa Jonathan': Malami ya hango makarkashiya ga Tinubu a 2027

Bayan wannn ganawa, Dickson ya bayyana cewa yana kokarin gyara saɓani a tsakanin masu ruwa da tsaki na jam'iyyar.

Sanata Dickson ya ce taron wani ɓangare ne na shirin tattaunawa da ake ci gaba da yi da nufin tabbatar da jituwa tsakanin shugabannin jam'iyyar a Kano.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262