An Kwarfe Sanatan APC da Ganduje ya yi wa Alkawarin Tikiti a 2027
- Sanata Ned Nwoko ya zargi jam’iyyar APC da rashin cika alkawarin ba shi tikitin takara kai tsaye na kujerar Sanatan Delta ta Arewa bayan ya sha kaye
- Tsohon gwamnan jihar Delta, Ifeanyi Okowa, ya samu kuri’u 113,309 inda ya doke Ned Nwoko wanda ya samu kuri’u 2,612 a zaben fitar da gwani na APC
- Sai dai Sanata Ned Nwoko, mai shekaru 65, ya ki amincewa da sakamakon zaben, yana mai zargin cewa an yi magudi domin ba Okowa nasara
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Delta - Sanatan da ke wakiltar Delta ta Arewa, Ned Nwoko, ya yi watsi da sakamakon zaben fitar da gwani na jam’iyyar APC, yana mai cewa tsarin bai kasance mai gaskiya da adalci ba.
Hakan na zuwa ne yayin da masu neman takara daga jam'iyyu daban-daban ke korafi kan yadda ake gudanar da zaben fitar da gwani.

Source: Facebook
Korafin Sanata Ned Nwoko
A wata hira da ya yi da AriseTV, Nwoko ya nuna rashin gamsuwa da yadda aka gudanar da zaben fidda gwani na sanatoci, musamman yadda aka bayyana Ifeanyi Okowa a matsayin wanda ya yi nasara.
Sanatan ya ce bidiyon da ke yawo a intanet da ke nuna yadda aka ayyana Okowa a matsayin wanda ya lashe zaben ya fito ne daga mazaba daya kacal daga cikin mazabu 98 da ke yankin.
Ya kalubalanci jam’iyyar da ta fitar da cikakken sakamakon dukkan sauran mazabu tare da hujjoji:
“Ba zan amince da shi ba.”
Ya dage cewa shi ne ya samu mafi yawan kuri’u a fadin yankin, kuma ya bukaci a bayyana sakamakon zabe dalla-dalla daga kowane mazaba tare da bidiyo domin tabbatar da sahihancin sakamakon da aka fitar.

Source: Twitter
Alkawarin Ganduje ga Nwoko
Nwoko ya ce ya shiga APC ne bisa tabbacin da shugabannin jam’iyyar suka ba shi, ciki har da tsohon shugaban jam’iyyar na kasa, Abdullahi Ganduje.
A cewarsa, alkawuran sun hada da tikitin takara kai tsaye, rabon madafun iko, rushe kwamitin zartarwa na jihar, da kuma shigar da masu sauya sheka cikin tsarin jam’iyyar — amma ya ce ba a cika wadannan alkawura ba.
“An fada min kafin na shiga jam’iyyar cewa za a ba ni tikitin kai tsaye. Me ya sa zan bar komai haka kawai ba tare da tabbatar da cewa ina da tabbataccen abu ba?”
In ji shi.
Nwoko ya gargadi cewa zai yi watsi da duk wani sakamako da shugabancin APC na kasa ya amince da shi idan ya saba da abin da ya aka masa alkawari.
Ga bidiyon Nwoko da shafin Yoruba Times ya wallafa a X:
Ana rigima kan takarar Pantami
A wani labarin, mun kawo muku cewa daya daga cikin masu neman tikitin takarar gwamna a karkashin PDP a jihar Gombe ya yi korafi kan ba Sheikh Pantami tikiti.
Abdulkadir Hamma Saleh ya ce ba za su amince da ba Sheikh Isa Ali Pantami tikiti ba saboda su ne suka shiga jam'iyyyar tun farar safiya.
Yayin da ya ke kira da a kwantar da hankali, Hamma Saleh ya bayyana cewa za su dauki matakin zuwa kotu domin kwato hakkinsu.
Asali: Legit.ng

