2027: Atiku Ya Bayyana Tsare Tsarensa game da Najeriya bayan Lashe Tikitin ADC

2027: Atiku Ya Bayyana Tsare Tsarensa game da Najeriya bayan Lashe Tikitin ADC

  • 'Dan takarar shugaban kasa, Atiku Abubakar ya bayyana manyan tsare-tsarensa kan tsaro, ilimi, tattalin arziki da lafiya bayan lashe tikitin shugaban ƙasa na ADC
  • Ya zargi gwamnatin APC da tauye dimokuraɗiyya da muzgunawa ‘yan adawa a yayin da ya ke furucin godiya bayan yan ADC sun zabe shi a matsayin dan takara
  • Atiku ya yi alƙawarin samar da ilimin firamare da sakandare kyauta tare da ɗaukar matakai kan matsalar tsaro da wutar lantarki da a yanzu ke farfadiya a Najeriya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT Abuja –Tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, ya bayyana manyan manufofinsa kan tsaro, ilimi, tattalin arziki da kiwon lafiya bayan zama ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar ADC gabanin zaɓen 2027.

Kara karanta wannan

Zaben ADC: Atiku Abubakar ya shiga gaba, ya samu gagarumar nasara a jihohi 5

Ya bayyana haka ne bayan ya yi nasarar zama dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar ADC a babban zabe mai zuwa inda ake sa ran zai fafata da Bola Tinubu da sauran yan takara.

Atiku ya zama 'dan takarar shugaban kasa a ADC
Atiku Abubakar a lokacin da ya kada kuri'a a zaben fitar da gwanin ADC Hoto: Atiku Abubakar
Source: Twitter

Atiku ya bayyana haka ne cikin saƙonnin da ya wallafa a shafinsa na X, inda ya nuna godiyarsa ga jam’iyyar ADC bisa ba shi damar jagorantar ta zuwa babban zaɓe mai zuwa.

Atiku Abubakar ya gode wa ADC

Atiku Abubakar ya ce ADC ta nuna cewa dimokuraɗiyya na nan da rai duk da abin da ya kira ƙoƙarin gwamnatin APC na murƙushe tsarin dimokuraɗiyya.

Ya ce:

“Ina miƙa godiyata matuƙa bisa damar da kuka ba ni ta jagorantar babbar jam’iyyarmu ta ADC zuwa zaɓe mai zuwa a matsayin ɗan takarar shugaban ƙasa. Ina matuƙar farin ciki da tawali’u bisa wannan gagarumar karramawa.”

Atiku ya yi alƙawari kan tsaro da ilimi

Atiku Abubakar ya bayyana cewa idan ADC ta kafa gwamnati ƙarƙashin jagorancinsa, za ta ɗauki matakai masu tsauri domin kawo ƙarshen matsalar tsaro da kashe-kashe a ƙasar nan. Ya ce:

“Gwamnatin ADC ƙarƙashin jagorancina za ta ɗauki mataki kai-tsaye wajen magance rashin tsaro da kare rayuka da dukiyoyin jama’a.”

Kara karanta wannan

NDC ta yi zargin wasu shugabanninta na karbar na goro domin tsayar da 'dan takara

Ya bayyana cewa za su ƙarfafa rundunonin tsaro ta hanyar ɗaukar sababbin jami’ai, samar da kayan aiki na zamani, horaswa da inganta walwalar jami’an tsaro.

Atiku ya yi alkawarin inganta Najeriya bayan samun tikitin takarar ADC
Atiku Abubakar da dandazon magoya baya a Najeriya Hoto: Atiku Abubakar
Source: Twitter

Atiku ya kuma ce ilimi zai kasance babban ginshiƙi a gwamnatinsa, yana mai cewa sama da yara miliyan 20 masu zuwa makaranta ba sa makaranta a Najeriya.

A cewarsa:

“Saboda haka za mu aiwatar da ilimin firamare da sakandare kyauta kuma dole ga kowa.”

Ya ce gwamnatinsa za ta zuba jari wajen koyar da fasahar shugabanci, kere-kere, fasahar zamani da kirkire-kirkire ga matasa domin su zama masu anfani ga ƙasa.

Atiku ya zargi gwamnatin APC da gazawa wajen tafiyar da tattalin arziki, yana mai cewa talauci da tsadar rayuwa sun yi muni a ƙasar nan.

Ya yi alƙawarin cewa gwamnatin ADC za ta mayar da hankali wajen gyara matsalar wutar lantarki da jawo hannun jari daga ciki da wajen ƙasa domin samar da ayyukan yi. Game da harkar lafiya kuwa, Atiku ya ce gwamnatinsa za ta zuba jari sosai a fannin kula da lafiya musamman matakin farko.

Atiku ya samu gagarumar nasara

Kara karanta wannan

2027: Atiku da manyan ADC za su san makomarsu game da takarar shugaban kasa

A baya, kun samu labarin cewa tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, ya lashe zaben fitar da gwani na shugaban kasa da aka yi a ADC a shirin jam'iyyar na tunkarar babban zabe mai zuwa.

A jihar Gombe, jami’in tattara sakamako, Farfesa David Agbu, ya ce an gudanar da zaben cikin lumana yayin da mutane 140,949 suka kada kuri’unsu a tsakanin manyan jam'iyyar uku da ke neman takarar.

Rotimi Amaechi ya samu kuri’u 1,150, yayin da Muhammad Hayatu-Deen ya samu 465 a zaben da jami’an INEC suka sanya ido a kai, yayin da Atiku Abubakar ya yi zarra da kuri'a 139,334.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng