Tafiyar Atiku Ta Shiga Matsala a Gombe, 'Yan ADC Sun Koma APC da PDP

Tafiyar Atiku Ta Shiga Matsala a Gombe, 'Yan ADC Sun Koma APC da PDP

  • 'Yan jam'iyyar ADC a jihar Gombe na sauya sheka zuwa jam'iyyun APC, PDP da sauransu tun bayan zaben fitar da gwani da aka yi
  • Sakataren jam'iyyar ADC a jihar Gombe, Dr Ahmad Gana ya sauya sheka zuwa APC, inda ya samu tarba ta hannun Jamilu Gwamna
  • Wasu 'yan siyasa da suka nemi takara a karkashin jam'iyyar ADC, Dr Muhammad Bello da Mubarak Musa Dantori sun sauya sheka

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Gombe - Jam'iyyar ADC na fuskantar rudani a jihar Gombe bayan zaben fitar da gwani da ta gudanar a watan da ya gabata.

Wasu 'yan jam'iyyar ADC, ciki har da manyan shugabanni na sauya sheka zuwa PDP da APC domin samun mafakar siyasa.

Gwamna Inuwa Yahaya da wasu 'yan APC
Muhammad A Bello da Inuwa Yahaya tare da wasu 'yan APC. Hoto: Isamila Uba Misilli
Source: Facebook

Sakataren ADC ya koma jam'iyyar APC

Kara karanta wannan

PDP ta kara birkicewa, 'yan majalisa 4 na jam'iyyar daga Bauchi sun koma APM

Hadimin dan takarar gwamnan Gombe a karkashin APC, Ibrahim Sani Shawai ya wallafa a Facebook cewa sakataren ADC, Dr Ahmad Gana ya koma APC.

Ya ce:

"Dr Gana, ƙwararren jami’in gwamnati kuma tsohon kwamishina, ya miƙa takardar murabus daga mukaminsa a ADC, yana mai cewa ya gamsu cewa Dr Gwamna ne ya fi cancanta ya jagoranci jihar Gombe a wannan muhimmin lokaci."

Tun a ranar 20 ga watan Mayun 2026 Dr Ahmad Gana ya yi rubutu a shafinsa na Facebook yana ba APC shawara kan yadda za ta magance rikicin da ya bulla bayan hana Sheikh Pantami da Saidu Alkali takarar gwamna.

Lamarin ya jawo zarge-zarge daga masu magana a sashen sharhi, suna cewa dama yana yi wa APC aiki ne. Ga sakon da Dr Gana ya rubuta a lokacin:

"Ga maslaha ga makwabtan mu na siyasa. Shi minista (Saidu Alkali) a maida shi kujerar sa, shi kuma akaramakallah (Pantami) a tura shi ambasada. Shikenan"
Dr Ahmad Gana da Jamilu Gwamna
Lokacin da Jamilu Gwamna ya karbi Dr Ahmad Gana zuwa APC. Hoto: Ibrahim Sani Shawai
Source: Facebook

'Dan takarar ADC ya koma APC

Tsohon dan majalisar jihar Gombe, Muhammad A Bello da ya nemi takarar majalisar tarayya a ADC a mazabar Gombe/Kwami/Funakaye, ya koma APC.

Kara karanta wannan

Bayan sace yayar tsohon minista, ƴan bindiga sun harbe shugaban jam'iyyar adawa

Ya bayyana haka ne bayan gaza samun tikitin takara a zaben fitar da gwani da aka yi, inda ya yi zargin ba a yi masa adalci ba.

Mai magana da yawun gwamnan jihar Gombe, Ismaila Uba Misilli, ya wallafa a Facebook cewa Dr Bello zai yi wa APC aiki a jihar.

Muhammad A Bello da Inuwa Yahaya
Lokacin da Dr Muhammad A Bello ya gana da Gwamna Inuwa Yahaya. Hoto: Ismaila Uba Misilli
Source: Facebook

Dantori ya koma jam'iyyar PDP

Mubarak Musa Dantori da ya nemi takarar majalisar jihar a Gombe ta Kudu karkashin jam'iyyar ADC ya sanar da komawa PDP bayan gaza samun tikiti.

A wani sako da ya wallafa a Facebook, Dantori ya ce:

"Bayan tattaunawa mai zurfi, nazari mai kyau, da kuma shawarwari masu amfani daga magoya bayana, abokan siyasa da dattawa masu daraja, na yanke shawarar komawa jam’iyyar PDP."
Mubarak Musa Dantori ya koma PDP
Lokacin da mutanen Sheikh Isa Ali Pantami suka karbi Mubarak Dantori zuwa PDP. Hoto: Mubarak Musa
Source: Facebook

Dantori ya ce ya yanke shawarar ba da cikakken goyon baya ga Sheikh Isa Ali Ibrahim Pantami domin ya zama gwamna a ƙarƙashin tutar PDP a jihar Gombe.

Tinka ya samu tikitin ADC a Gombe

A wani labarin, mun kawo muku cewa jam'iyyar ADC ta sanar da cewa Dr Bala Bello Tinka ne ya lashe zaben fitar da gwani da ta yi a Gombe.

Kara karanta wannan

Pantami da masu neman gwamna da suka sauya sheka bayan rasa tikiti a APC

A bayanin da jam'iyyar ta yi, ta ce dukkan masu ruwa da tsaki sun amince da Dr Bala Bello Tinka ya yi takarar gwamna a jihar a zaben 2027.

A jawabin karbar tikitin da ya yi, dan takarar ya ce a shirye ya ke ya yi ayyukan cigaba a jihar Gombe matukar aka kada masa kuri'a ya zama gwamna.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng